Bangaren Fatima ma har da dare da sukazo kwanciya tana zancen su Sadiq tace "Yaya daman kana da aboki ne ban taba ganinsa ba sai yau?" Yaja hancinta "Baby sarkin tmby ni ba abokina bane yau na taba ganinsa nima" ta tashi zaune "kai Yaya naji fa da zasu tafi yace maka abokina sai mun hadu kace to kuma bamu sansu bane muka shiga motarsu?" Ya dafe kai "Baby ki kwanta don Allah yau fa na gaji ni motarsu ce ta bigeni naji wannan ciwon shine Abbansu yace a kawoni gida sbd kafar" ta danyi shiru kafin tace "to Yaya sukam sunji dadi Abbansu yana da kirki ko ba irin Abban nan gidan b" Hararanta yy "Baby ba na hanaki gulma ba maganar wanda baya nan fa gulmace kar in sake ji Okay?nd ki kwanta kiyi bacci" hakuri ta bashi ganin yana bata rai tace "ni sunana Princess ba Baby ba" yy murmushi ganin yadda take tura baki "Okay Princess din new Yaya kuma Babyna Gud night" rufe ido tayi cikin jin dadi ya mata Addu'a yaja bargo ya rufeta kafin ya fice ya rufe musu Falon ya wuce dakinta wanda ya mayar nasa tun barin Ummy gidan ita kuma take kwana dakin Ummyn
Bayan Kwana biyu
Sadiq da yy ta rokon Momma dakyar ta barshi zuwa gidansu Ahmad bayan ta fadawa Papa yace yaje daga nan saa duba Ahmad din da kafa tunda shi ya koma wajen aiki cewa tayi yaje Baba Bala ya kaishi baiyi musu ba don yasan ba gane gidan zaiyi ba daman tunda bai taba fita shi kadai ba a Kanon kawai de abinda ya sani bb nisa da gidansu
Dakinsu ya shiga ya debi Chocolates din Salim ya fice suka kama hanya da Baba kasancewar zagaye sukayi rannan sbd sunbi makarantar su Fatima yau sai Baba yabi hanya direct har zuwa gidan nan ne ma Sadiq yaga ashe bb wani wuyar ganewa direct hanya ne har gidansu
Sallama Sadiq yy a Kofar gidan mai gadi ya leqo ta karamar kofan "lafia Dan samari wa kk nema?" Gaidashi yy sannan yace "naxo wajen Yayan Fatima ne" "to to wajen Ahmad ynx kuwa ya tafi kai ita Fadimar Islamiyya ynx zaka ganshi" ai ko yana rufe baki sai ga Ahmad din nan yana sauri yaxo ya wanke kayan makarantar Husna sbd yau Sunday gobe da Schl kuma don wulakanci Mama Indo na ganinshi jiya ya wanke na Fatima bata bashi ba sai ynx da taga zai fita ta kumace kar ya sake 6 tayi basu bushe ba kada abar mata kayan 'ya aljannu su sauka a kai
Sakin fuska yy ganin Sadiq ya bashi hannu suka gaisa yace "ashe da gaske kk zaka dawo din" daria yy "sosai ma ai ni tun ranar nacewa Momma nayi aboki daman tun dawowar mu kano banda gidan Grandpa bb inda na sani sbd 'yan uwan Papa duk ba mazauna nan bane" Ahmad yace "ayya to ngd da aka zabeni na zama abokin" "Hhhh Lallai kam ai nike d godia tunda naga alamar an karbeni matsayin abokin" Baba Bala ne ya fito daga mota yace " Baban Baba ba ynx zamu koma bane?" Ahmad ya dan harari Sadiq yana karasawa wajen Baba "sannu Baba tare kuke? Ina yini" cike da fara'a ya amsa "wlh kuwa samari ya kafar taka Alhaji yace a gaidaka" Ahmad yace "Laa kafa ta warke Baba ngd sosai" Sadiq yace "Baba fa sunanshi Ahmad ba Samari ba ka tafi kawai sai karfe 6pm kaga Princess taje Islamiyya kuma ni sai na ganta in tafi" sallama Baban yy musu ya wuce Ahmad ya kama hannun Sadiq suka shiga gidan nan ne Sadiq yaga cikin gidan duk da cewar bai kai nasu ba amma gidan nada kyau sosai Part dinda suka nufa ya kalla yaga wurin ya dan tsufa sauran Part biyun kam Maa Sha Allah sai sheqi suke bai dai ce komi ba Key Ahmad ya ciro ya bude Falon suka shiga komi tsaf a tunanin Sadiq ko Mamansu taje Unguwa ne amma bai tmby ba yy shiru kitchen Ahmad yaje ya kawo wa Sadiq ruwa koda yake basuda shi hakan bai hana Ahmad saya musu Swan water ba da kuma Lemu sbd kar Fatima ta gani wajen wasu don yy Alqawari indai yana da Lafia zai nema kodan kar Fatima ta nemi wani abu ta rasa
Har y zauna suna hira sai ya tuna da aikin da Mama ta saka shi da sauri ya mike yace wa Sadiq abokin minti kadan baran dan wanke wasu kaya to da yake a Side dinsu zaiyi wanki sai Sadiq ya fito ya zauna suna hira Ahmad na wankin shi Sadiq zatonshi kayan makarantar Fatima ne amma sai yaga ba irin wanda suka ganta dashi bane rannan amma still kasancewar shi ba mai yawan tambaya bane yasa yai shiru a nan tsakar gidan suka cigaba da hiransu Ahmad na bashi lbrn Kano din shiko yace zai xo su fita yawo watarana a haka har lkcn tashinsu Fatima yy suka tafi daukota tare a kofar makarantar suka hangota ai ko tana ganinsu ta taho da gudu amma maimakon ta nufi Ahmad kamar yadda ta saba sai ta nufi Sadiq tana ta wahe baki jakanta ya karba kamar yadda yaga ranan Ahmad yy itako cike da murna tace "My Prince kasan Islamiyyar mu ne daman?" Yy daria "kai My Princess bb ko gaisuwa sai tmby baki ga tare da Yaya mukazo b shine ya nuna min" rufe fuskar ta tayi wai taji kunya tace "Good evening" ya kama hannunta "ya makaranta ina fatan bb wanda ya taba min ke?" Tayi daria "laa hakama fa kullum Yaaya yake cewa kuma ni ai bana rashin ji ina kawo hadda kuma bana latti bb mai dukana" murmushi yy "Gud girl haka nake son ji" Ahmad da ya zuba musu ido yace "Allah sarki ni ynx Baby ba za'a kulani ba ko?" Saurin isa kusa dashi tayi ta kamo hannun shi "Sorry Yaya ai kai gidanmu daya idan munje zan kulaka shi kuma Prince ai tafia zaiyi" daria Sadiq yy "yauwa Princess fada masa kishi yake da ni" haka dai suka taho gida cikin jin dadi a Kofar gidan sukayi karo da Mama Indo cikin Motar ta ta dauko Husna daga Islamiyya Bude mata gate akayi ta shige tayi parking dai2 fitowar ta suka shigo ciki Sadiq ne sunxo gifta ta yace "sannu Mama ina yini?" Tsaki tayi "mtsww da ban yini b zaka ganni shi munafikin bai hanaka gaidani bane tunda shi ba'a masa tarbiyyar gaida Manya b" jan Sadiq kawai Ahmad yy suka wuce ganin bai kulata ba tace "aikin banxa anyi gadon halin munafurci daga wajen Uwar ai ana chan inda aka kai musu kuma ana fama" wani irin juyowa yy ya dawo dai2 saitin ta kafin ya nuna ta "duk rashin mutuncin ki kada ki kara ambato Uwata ya tsaya iyaka kaina" ihu tayi ta tafa hannu "wuhuhu ba dai tsawon mu yy dai2 ba to dakar ni mana Ahmad nace dakar ni kuma wallahi uban naka zai dawo zanji ko shine ya daure maka kk min abinda kaso" bai tsaya sauraronta ba ya wuce fuu zuwa bangaren su Sadiq ne yaja hannun Fatima suka bi bayanshi yana jinjina abin a ransa don shikam bai taba ganin irin hakan b lamarin gidan nasu gaba daya wani iri yake mai amma baice komi ba
Zaune suka sami Ahmad sai huci yake don shi akwai zucia Sadiq ne yace wa Fatima "Princess bani ruwa insha" tafia dauko masa tayi tana waiwayen Yayan nata don in yy irin wannan fushin ita kanta tsoronshi take zama Sadiq yy gefensa ya dafa kafadan shi yace "kayi hkr Broda ni naja maka wlh bansan bakwa mgn ba da ban gaisheta b ni naga Babba ce shiyasa please kayi hkr" ajiyan zucia ya sauke "bb komi kar ka damu ai na saba da halinta nikam" shiru sukayi Fatima ta kawo ruwan tana rakubewa a gefen Sadiq murmushi yy ganin duk yadda suke wasa da Yayan nata tana masifar tsoronsa ya amshi ruwa tare da mika mata jakanta "ungo kai daki ki cire Uniform din" bb musu ta wuce tana waigensu kiran Sallahr magriba aka kwala hakan yasa Sadiq mikewa "Bro ina zanyi alwala ne gara muyi sallah ynx Baba Bala zai dawo" tashi Ahmad yy yace muje dakinshi suka shiga ya nunawa Sadiq din Bathroom shi kuma ya fito zuwa dakin Fatima a zaune ya sameta tayi tagumi yy murmushi tare da zare mata hannun yace "Princess din Sadiq ba na hana tagumi b?" Da sauri tace "kayi hkr Yaya kaji to kabar fushin?" Daga mata kai yy yace "na bari to barinyi alwala a bayinki" har yakai kofa tace "Yayan ya tafi ne?" Girgiza kai kawai yy ya shige ita kuma ta fita falon daidai shima ya fito yana warware hannun rigarsa murmushi ya mata yace "ina Yayanmu?" Tace "yana alwala daki na kai fa ba yayanka bane shi ai tsayinku daya har kama fisa" yace "yes amma Yayan Princess dina ai yayana ne" "to sarakan magana wuce kije kiyi Sallah mun tafi Masjid" suka fita Ahmad ya kulleta da Key ta baya tare da kwashe kayan dake kan igiyan suka fito dai2 side din Mama Indo Ahmad ya tsaya sai ga mai aikinta ta dawo daga baiwa Maigadi abinci baice komi ba ya mika mata kayan suka nufi masallacin sai ynx ne Sadiq ya gane Uniform din yarinyar matan ne kenan Ahmad y wanke
Suna idar da Sallah suka taho gidan Ahmad ya shiga kitchen ya zubo musu abinci a Babban Faranti ya saka Spoon uku ya fito musu dashi ya zauna yana kiran "Baby! Baby!! Fito muci abinci" da saurinta ta fito amma maimakon ta zauna kitchen ta nufa sai gata ta fito da karamin Serving tray mai dauke da ruwa da cup guda biyu daria Ahmad yy "wlh na ma manta da maganar ruwa sbd yunwar da ta koro ni" suka mai dariar suma Sadiq yana kallon Fatima don duk da kananun shekarunta tana da wani irin nutsuwa irin na ya'yan da suka samu cikakken tarbiyya
Fara ci sukayi dukansu ukun don Sadiq sam baida matsala yana da saurin sakewa musamman in abu yamar to balle yadda zuciarsa ta karbi su Ahmad 100% jinsu yake tamkar su Saleem da suka fito ciki daya to a bangaren Ahmad din ma hakane don farat daya ya karbi Sadiq din a ranshi yanajin zai iya sharing damuwar shi da Sadiq din ga kuma yadda yaga Sadiq na kula da Fatiman shi kamar tashi kanwar don haka yakejinsa kamar Danuwa ba aboki b
Suna gama cin abincin Fatima ta dauko Book dinta ta kawo Assignment za'a gwada mata Sadiq ne ya zauna yake koya mata shidai Ahmad na gefe yana kallonsu cikin farin cikin da ya dade baiji ba tun sanda aka rabasu da Imran da kuma wargajewar da gidan yy a nan ya tuna Imran da kalan kukan da suka dinga yi ranarda zai tafi shida Fatima a ransa ya mishi fatan Alkhairy don har ga Allah yana kaunarsa duk da halin Babarshi yasan Samm bb laifin Imran a ciki
#Smarty💞
![](https://img.wattpad.com/cover/202269501-288-k308204.jpg)
YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...