Tun daga wannan rana komi ya sake sauyawa Ahmad shike komi na gidan kama daga wankin kayansu Indo da Husna har ma da na Abbah duk kuwa da cewar akwai masu yi din da farko idan ta saka shi aiki kin yi yake duk da cewar idan Abbah ya dawo haka zata saka ya kamashi ya daka bawai dan Abbah yafi karfinshi bane yake tsayuwa a'a tun wani rana da Abbah ya daki Ummy yy yunkurin zuwa ya rama mata tamai kashedin cewar ko kallon banza yaiwa mahaifinsa bata yafe ba shine dalilin da yake bari ya bugi son ranshi ya kyale bashi zai hana gobe ya sake yin laifin ba ganin yanason fin karfinta yasa tayi amfani da soyayyar da yake wa kanwarshi Fatima idan yy mata laifi ta kamata ta buga to a nan ne ya kasa Jura tunda ta gano weakness dinshi shikenan ya sallama komi ta sakashi zaiyi bb musu.
Ahmad ke wa Fatima komi kamar su Wanki, guga, tsifan kai ya kaita kitso ya yanke mata kumba da sauran abubuwa tare suke tafia makaranta idan an tashi ta jirashi shima su tashi ya goyata su dawo gida ya zama Uwa da Ubanta bata da kowa sai shi hatta abinci shi zai nemo ya kuma dafa ya bata taci idan babu yawa shi ya hakura haka dai suke rayuwa basu kula kowa basa shiga sabgar kowa haka itama Indo bb ruwanta dasu indai zasuyi mata bauta ta kuma hanasu abinci to burinta ya cika haka Husna ke zagin Ahmad bai isa ya tanka ba kuma ko badon haka ba ma tana cin albarkacin Imran da yaso kanwarshi tsakani da Allah tsakanin su da Abba kam sai hange daga nesa.
Lokacin rubuta WAEC yy Ahmad bai ko tunkari Abba ba daman yana dan tara kudadenshi hakan yasa ya kwashe abunshi yaje makaranta don ya biya to cikin ikon Allah sai gwamnati ta biya musu WAEC akace duk maison yin NECO ya biya shikam ya gode wa Allah daman Fatima ma zata gama Primary yana tunanin sai ya nemi kudin sakata a JSS to tunda ga wannan bari ya ajiye zaiyi iya kokarinshi yaga yaci guda dayan ma da taimakon Allah.
Kuma hakan akayi bayan Fatima ta gama Primary Ahmad ya nema mata Private School mai dan Dama a nan Na'ibawan mai suna SILVER PEN ya sakata sosai taji dadi sbd bata son wancan makarantar a cewarta yara sunyi yawa a Ajin shima ya maida hankali kan nashi karantun har lkc yy suka rubuta Exam Alhamdulillah yana saka ran zai sami Result mai kyau daga yadda jarrabawar tamai sauki.
Ganin baya komi yasa ya cigaba da dan buga-bugan shi duk aikin da ya samu yana yi har gini ko buga Bulo bb abinda baiyi.
Yakan raka Fatima makaranta kuma in aka tashi yaje su taho tare wata rana bayan ta gama shiryawa ne ya fito daga Kitchen dinsu inda yake wanke abubuwan da suka karya yana fadin "Baby na muje in raka ki kada a miki bulalan makara idan na dawo nayi sharan" turo baki tayi "Yaya ni fa na girma Allah kuwan 'yan Class dinmu suna min daria wai katuwa dani Ana kawoni Schl ai ko yaran Nursery ma akwai masu zuwa da kansu" murmushi yy ya shafa kanta "rabu dasu ai ba kowa ke samun mai kawo shi ba haushi sukaji yau kan ma a baya zan goyaki muje" ya duka wai ta hau da gudu ta fita tana daria tasan tsokanarta yake don tace ta girmi goyo ynx shima darian yy ya dauko Backpack dinta ya biyo bayanta suka fita suna daria suna tafia suna hira sunje dai2 wani gida dake layinsu wata ta fito itama sanye da kayan makarantar amma na SSS Murmushi taiwa Fatima itama ta daga mata hannu cigaba tayi da tafia suna bayanta Fatima tace "Yaya ya baku gaisa da Aunty ba yau daman anan kuke haduwa?" Bai fahimceta ba yace "wacce Anty kuma?" Dalibar nan dake gaban su ta nuna yace "to na santa ne da zan gaisa da ita in ma sbd tana makarantar ku ne ai ni ya kamata ta gaida tunda na girmeta" Fatima taja ta tsaya "Yaya ka fa cemin Karya bb kyau nasan kaima bakayi to wa yake bata chocolate ta kawo min idan ba kai b?" Shima tsayuwan yy "ni ban ma taba ganinta ba sai yau wanne irin chocolate kuma?" Fatima tace "wlh Yaya kullum idan aka fita Break sai ta bani chocolate tace kaine ka aikota ni kuma shine nake karba daman su Nadia suna min daria wai ba'a bani Chocolate da Lemon kwali a gidan mu" hannunta y ja da sauri suka isko wannan Dalibar shan gabanta yy daman Ahmad akwai zafin rai "ke Malama me kike nema wajen kanwata?" Ita kam yarinyar da ta razana sanadin shiga gabanta da yy ba tsammani sai ta saki ajiyar zucia amma kuma sai tamai kallon rashin fahimta "ni kuma me zan nema wajen kanwarka ni Halima" kara hade fuska yy "meysa kk bata abu kuma dan taki karba kk cewan nine na aiko ki so kk ki cutar da ita ko? Idan ma mayya ce ke kici kanki jininmu yafi karfin ki" ai tuni sai ga hawaye nabin fuskarta already daman sun iso kofar makarantan don haka ta share hawayenta ta raba gefenshi zata wuce ganin ana shirin fara tsaron latti sake tareta yy "Mlm bb inda zakije sai kin fada min Okay!" Ta kalleshi lalle ma guy din nan amma sai tace "kayi hkr kaga zamuyi latti amma idan an tashi nasan ai kana zuwa zan fada maka dalili" zaiyi magana taja hannun Fatima suka shige yana hangensu har aji ta rakata kafin ta wuce nasu yayi tunani kamar mutuniyar kirki ce amma kuma ai mugu baida kama duk da yaga tana da nutsuwa sedai samm ya kasa yadda da ita haka kawai ta kama baiwa kanwarsa abu bb dalili ai akwai alamun tambaya a nan haka dai ya tafi yana sake2.
Time din tashi bai gama cika ba ya kamo hanyar Schl din a tunaninsa na zata iya guduwa kafin yaje yana tsaye kuwa aka tashesu tare suka fito tana rike da hannun Fatima suna mgn suna murmushi baisan ya shagala da kallon su ba har suka kariso inda yake sbd yaune rana ta farko da yaga Fatima tana ma wani daria bayan shi tun bayan rabuwarsu da Ummy kama hannunsa da tayi yasa ya dawo haiyacinshi tare da sakar mata murmushi ya karbi jakanta yana shafa kanta "Baby na sannu da Schl fatan bb wanda ya taba min ke?" Wannan shine tmbyr da kullum yake mata itama kamar kullum tayi daria "Ai Yaya ko Prefect zasu bigeni Aunty tana hanawa" ta fada tana nuna wannan Budurwar dake tsaye kallonta yy sai ta sunkui da kai kasa tare da fadin "Sannu da zuwa Yaya" da "Yauwa" ya amsa sannan yace wa Fatima "Baby muje fara gaba" bb musu ta fara tafiya suna biye a bayanta "ina jinki fada min dalilin abinda kike" bata wani tsaya jan mgn ba tace "bb wani dalili kawai gani nayi bata shiga cikin sa'anninta kullum tana gefe shine na fara kulata to rannan sai naji yaran ajin suna fadin ba'a bata Chocolate a gida ita kuma tace ai Yaya yana siyo mata ni kuma har ga Allah ina sonta shiyasa nake kawo mata ranar farko da na bata sai taki karba to da yake ina ganinku tare kullum kuma naji maganarta komi Yaya shine nace mata kaine kk bani in kawo mata kuma ta yadda amma kayi hkr idan hakan laifi ne" a sanyaye ta karisa maganar dai2 kuma sun iso gate din gidansu tayi shigewarta abinta sai kuma yaji baiji dadin ce mata Mayyan da yy ba ina laifin meson naka don haka ya kuduri aniyar bata hkr in sun sake haduwa isko Fatima yy suka karasa nasu gidan yana hada mata abinci tana bashi lbrn yadda Auntyn ke taimakon ta a Schl din yaji dadi kwarai kuma ta sami matsayi mai girma a wajenshi don yadda yake son Fatima to fa dole yaso duk mai kaunarta.
Basu sake haduwa ba daga ranan har aka share sati 2 sai rannan yake tambayar Fatima "Baby ina Auntyn ki ne naga bata zuwa makaranta" tace "nima Yaya bana ganinta jiya naje ajinsu sai Aunty Rahima tace wai batada lafia ne an kaita asibiti" baiji dadi ba sbd haka da suka karaso gidan ya tsaya suka gaisa da mai gadinsu dake zaune a benci ya tmby shi mai jiki nan yake fada masa ai gado aka bata amma yaji ana cewar gobe za'a sallame ta yaso ya tambayi sunan asibitin amma yayi tunanin idan yaje yace shi waye? Yayan 'yar makarantar su ko me don haka sai yace Allahu ya bata lafia suka wuce gida.
Washegari Result din su Ahmad ya fito bai sami zuwa ranar ba sbd aikin gini da sukeyi sai bayan kwana biyu yaje CAFE ya duba kuma Alhamdulillah yy kyau yanda ma baiyi tsammani ba ya dawo gida bayan ya dauko Fatima daga makaranta suna dawowa a hanya yake bata lbr yaci Jarrabawar shi itama sai murna take tana jefo masa tambayoyi sunxo giftawa ta gidansu Halima ne Maigadi dake zaune kan Benci ya tsaida su "saurayi don Allah tsaya Autar Hajia tace idan na ganku in mata magana" Ahmad ya gane wannan yarinyar ta makarantar su Fatima yake nufi don haka suka jirashi ya shige cikin gidan Jimm kadan kuwa sai gasu tare da Halima dake Sanye da Abaya ruwan kasa da Mayafinshi tana murmushi ta karaso inda suke tana fadin "Yaya da Babyn Yaya sannun barkan ku da rana" da Sauri Fatima ta saki hannun Ahmad taje ta rike na Halima har tana duduba jikinta "Aunty sannu ya jiki kinji sauki ko?" Daria tayi "naji sauki sosai kanwata ya Schl" da Lafia ta amsa Ahmad dake kallonsu yace "Sannu ya jikin ki keda bakida lafia ai bai kamata ki fito ba" "Haba dai naji sauki fa gobe ma In Shaa Allah zan koma mkrnt Baba ne ke fada min kunzo nemana shiyasa nace in kun taho yamin mgn" Ta karasa fuskarta dauke da murmushi shima murmushi yy "yeah naga bama ganinki kwana biyu na tmby kanwarki tace wai Classmate dinki tace bakida lafia shine nace bari mu dubaki ashe ma abin serious ne to Allah ya kara lafia" daga nan suka mata sallama suka wuce.
Ahmad tafe yana tunanin yadda zaiyi don har ga Allah yana son karatu amma baida halin shiga Jami'a a ynx don dole karatu saida kudi sannan ga Kanwarshi itama kuma shi bazai taba zuwa wajen Abbah ya rokesa ba ko wani nashi Uncle Musa kuma ga nauyin Ummy dake kanshi sbd haka ya yanke hukuncin hakura da nashi in yaso ya cigaba da buga2 ita Fatimar ya biya mata tayi
Kiiiiii!!! Karan taka birki ne ya dawo dashi daga dogon tunanin da yake har baisan ya hawo titin ba sedai duk da mai tuka motar ya taka birki hakan bai hana ya gogeshi ba saida yakai kasa da sauri matukin motar ya fito dattijo ne dan babba dan zai kusa sa'an Babanshi ya karaso yana fadin "sannu ko ina ta horn baka ji ba kuma na rigada na kwaso gudu shiyasa kayi hkr" Ahmad dake kokarin mikewa yace "bb komi wlh banji bane jeka abinka" ya fara kokarin tafia drivern ne ya lura da ciwon da Ahmad din yaji da har ya fara jini don haka yy hanzarin rikoshi ya zaunar a gefen titin "dakata kaga kaji ciwo fa" zaiyi mgn aka bude bayan motan aka fito.#Smarty💞
YOU ARE READING
RAYUWAR FATIMA
Short StoryMuryar Gwaggon ta a lkcn da ta bijire kan bukatar ta wanda shine silar rugujewar RAYUWAR ta karo na biyu Muryar matan gidan a lkcn da suke kara zuga Gwaggon nata da kuma Rantsuwar da ita Gwaggon tayi wanda kuma saida ta tabbar dashi a kanta Muryar...