Page 1

215 11 0
                                    

GODIYA

Bismillahir-rahmanir-rahim.

Ina mai miƙa godiya ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai daya bani ikon fara wannan rubutu mai albarka in sha Allah. salati marar adadi ga fiyayyen halitti manzon tsira annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.

Godiya ta musamman ga iyaye na tare fatan rahama a garesu duniya da lahira.

Bazan manta da miji na ba wan da kulawarsa, taimakonsa tare da sadaukarwan sa gare ni ya zama silar kasance wata a wannan matakin da nake a halin yanzu. Tabbas duk wani ci gaba da zan sanu a rayuwa ko mataki da zan taka yana da kaso mai yawa cikin nasarata, ina masa addu'a Allah ya azurta shi, ya kare imaninsa ya azurta shi da duk abunda zai zama alfanu a rayuwasa. Amin.

'Yan uwana da dangi na tare da 'yaya na, ina muku fatan alkairi tare da addu'a Allah ya kare ku ya ƙarawa rayuwa albarka da dankwan zumunci tsakaninmu.

Bazan manta da ɗaukacin al'umar musulmi ba, ina fatan Allah ya mana gafara, ya jiƙanmu, ya yalwata mana arzikinmu sannan ya haɗa kan ahlus-sunnah a duk in da suke.
Allah ya sauƙaƙa mana tsadar rayuwa, ya bamu aminci da nitsuwa, ya yaye mana musiba da bala'i, ya azuratamu da tsaro ya rabamu da tsoro ya bamu lafiya da zaman lafiya, ya shiryar da mu da 'ya 'yan mu da zuriyarmu baki ɗaya. Amin.

GABATARWA

Bin dokar Allah ba ƙauyanci bane" labari ne ƙirƙirarre dana rubuta dan faɗakar da kaina da kuma sauran 'yan uwa musulmai baki ɗaya.

GARGAƊI

Ni nake da hakkin mallakar dukkannin rubutuna ko littafina, ban yarda ayi amfani da shi dan wata manufa ba sai da izini na.

BAYANI

Idan wani sashin labarin yayi daidai da labarin ki/ka to an samu kamanceceniya ne kawai amma ba da niyyar cin mutunci ko tonon asiri ba.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now