Page 9

24 4 0
                                    

(Gidansu Zubaida)

A hankali Zubaida ta shigo gida dan kar Inna ta ji motsinta, kai tsaye ta wuce ɗakinta sannna ta ɓoye kyautar da Ahmad ya bata; Motsin futowar Inna daga bayi Zubaida taji sai tayi maza ta futo daga ɗaki tace "Inna naji gidan shiru dana dawo ashe kina bayi?"

Inna tace "eh na ɗan shiga watsa ruwa dan yau ana zafi sosai, ya ki ka baro Khadija da mamanta?"

"Lafiya lau na baro su, harma su kace na gaida ki sosai." Inna tace "to gaisuwa ya iso kuma na gode barin shiga ciki."

Inna tana shiga ɗaki Zubaidan ma ta koma ɗakinta ta saki labule sannan ta ɗauko jakarta ta buɗe dan taga dubu nawa maman Khadija ta samata, aiko tana ɗauko kudin ta bude baki tace "yanzu dama ashe matar nan dubu biyar ta samun a jaka? Tabdi jam gaskiya duk san kudi na ta fini, amma in ba yau akwai wataran.
Gashi sai kiran wayar Khadija na ketayi amma shiru bata ɗaukan wayata karde abunda nake tunani ya zama gaskiya, "hm lalle ashe kuwa zasu gane shayi ruwane."

Inna tana ɗaki amma tanatajin sambatu sai ta futo waje ta nufi ɗakin Zubaida tace "ikon Allah  Zubaida anya futanki kin yi addu'a kuwa?"

Zubaida tayi sauri ta ɓoye kayan da jakan sannna tace "eh Inna, na yi ai bana futa daga gida banyi addu'a ba; duk wani azkhar da kike koyamun ina yinsu, mai yasa ki ka tambaye ni Inna?"

Inna tace toh ai naji sai sambatu ki ke yi ne kuma ke kaɗai ce a ɗakin shine nake zaton ko gamo ki ka yi"

Zubaida taɗanyi dariya tace "haba Inna wani irin gamo kuma, ba komai kawai dai lissafi na keyi kin san mun kusa fara jarrabawar shiga aji biyar, kuma wannan litinin din zamu fara."

Inna tace "ikon Allah kinga lokaci baya jimawa, toh shikkenan Allah ya taimaka ya baku sa'a, babanki ya dawo yana kiranki kije ku gaisa."

Zubaida tace "to Inna."

Bayan shigar Zubaida ɗakin mahaifinta sai ta nemi guri ta zauna sannan tace baba sannu da dawowa gaskiya kasha hanya."

Baban Zubaida yace "yauwa, nace wa Innarki ta turomun ke dan akwai wata magana da nake so muyi dake, kin san dai na je ƙauye ko?"

"Ea baba, na sani" Zubaida ta faɗa.

Baban Zubaida yace "to bayan na je mungama maganar gona da sauran 'yan uwana munsa gona a kasuwa sai mukai sa'a mai gari yaga gona yana so kuma muka sayar masa, to bayan an kammala maganar gona sai ya kirani yakemun wata magana akanki danganeda dansa Yarima."

Zubaida tace "ni kuma baba?"

Baban Zubaida yace "ea ke, ɗansa Yarima ya ganki kuma ya ce yana sanki da aure kuma zai jiraki zuwa ki gama makaranta sai ayi bikinku, kinga shikkenan ciki lafiya baka lafiya kuma in bazaki manta ba ai dama can mai gari  dan uwanmu ne domin kuwa Adda Iyani kakarmu ta gurin uba sun haɗa dangi da ita yadikkon mai gari ta wajen kanwar mahaifiyarta. Kinga ai kuwa Yarima dan uwanki ne sai ayi tuwo na mai na musha biki abunmu."

Zubaida taɗan gyara zama tace "Baba ɗan mai gari fa kac? kuma wannan kallen dangin da ko maimaitawa bazan iya yi ba shine za'ace tuwo na mai n! gaskiya Baba ni ban shirya aure yanzu ba akwai tanadi mai kyau dana yiwa rayuwata dan haka bazan iya auran wahala da zaman ƙauye ba."

Baban Zubaida ya zabura cikin fushi ya dakamata tsawa yace "baki isa ba kin yi kaɗan ki watsamun ƙasa a ido,kuma ba shawararki nake nemaba umarni nake baki auren Yarima ya zama dole; ana nunamiki hanyar arziki kina rintse ido."

Inna tana tsaya bakin ƙofa tana jin abunda ke faruwa a cikin ɗakin tsakanin Zubaida da baban ta ba tare da sun sani ba, cikin hanzari tayi wuf ta faɗa cikin ɗakin sannan tace "haba mai gida yanzu da bakinka kake faɗan wannan maganar? ca nake kwanakin baya mun/yi magana akan karatunta kuma ka amince?"

Baban Zubaida yace  "wato ashe kina laɓe kenan? ai ni bance ba zatayi karatu ba in ta gama karatun sai ayi auren." Inna tace "ina nufin makarantar kwaleji fa ba sakandire ba."

Baban Zubaida yace "ba zatayi ba, yanzu ke a irin wannan rayuwa ina mu kaga kudin biyan makarantar kwalej? kuma banda abunki mairo ai wannan kamar auren jari ne in fa akai aurannan wataran gonar da mai gari ya saya tamu ta gado zai iya dawo mun da abina; kinga ga kudi ga gona kenan."

Maganarsa ya bawa Inna haushi sai kawai ta juya ta futa tabar ɗakin.

Baba in dai dan kuɗi ne ka ke so na auri Yarima to na maka alkawarin samun miji ɗan masu arziki wanda zan huta kuma ku huta sannan mu ji daɗi mu fantama a cikin dukiya."

Baban Zubaida yaɗanyi dariya sannan yace Allah zubaida ƴata, da gaske ki ke yi?"

Zubaida tace "sosai ma kuwa Baba, daga sudan yake kamar ɗan barabe in ka ganshi ga wata mota kamar tayi numfashi; Baba na maka alkawarin sai ya zama sirikinka."

Baban Zubaida yace "kaji ƴar albarka, to ke kin san da maganar mota kika bari ina ta maganar gona, to kwantar da hankalinki maganar yarima na soke ta."

Zubaida tayi dariya sannan tace "yauwa Babana na kaina ai na san zaka fahimce ni."

"Allah ya miki albarka, haihuwar kyakkawar mace jari; je ki abunki magana ya ƙare ki cewa Innar ki ta hadamun dambun nan yanzu na farafa jin yunwa." Baban Zubaida ya faɗa.

Zubaida tace "toh baba."

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now