Page 11

19 3 0
                                    

Bayan kokari da takurawa da Maman kamal tayi dan yaje su gaisa da safiya, hakan yasa yajeshi gurinnata a karo nafarko duk da baya son zuwa. Hanu biyu babanta yakarɓe shi yakai shi ɗakin hutu ya zauna aka kawo ruwa da ɗan abun taɓawa daga bisani aka kira safiya.
Tana isowa ƙofar shiga tayi masa sallama kamar haka Assalamu Alaikum, yaya kamal barka da zuwa

Kamal ya amsa sallaman sannan yace yauwa nagode, ya kike ya makaranta?

Safiya tace lafiya lau Alhamdulillah, kayi hakuri nabarka kana jira natsaya aikine aciki

Kamal yace ba komai, ai jiran mata yazama dole akan kowani namiji duk da bama so amma dole mu koya

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace  hakane

Kamal yace mum ta turoni gurinki, nasan kinsan dalilin zuwana ko?

Safiya eh nasani, adda ta faɗamin komai amman abinda na fahimta shine ba'a yiwa namiji auren dole kazalika koda ga mata ne hakan be halattaba, sai dai kasan shi hadin zumunci abune me kyau koma in yayi daɗi yana ƙara dankon zumunci tsakanin ƴan uwa sosai.

Kamal yace hakane, amma abinda nake gani shine bekamata ace anmiki maganan aure yanzuba tinda ko secondary school baki gamaba, abinda nake ganin yadace shine mubar maganan zuwa sanda zaki gama school inyaso senaji ra'ayinki

Safiya tace hakane, ba komai nima abunda nake tinani kenan

Kamal yace shikkenan tinda shawaranmu yazo daya I think bazamu samu matsala ba da mum

Safiya tace in sha Allah

Kamal ya dubi safiya yace mata amma kinsan Me, keda salma halinku abun mamaki ace saurayi kamarni yazo gurinki a karo na farko amma ki dauko wani katon hijab kinsa, ba kya ganin zai rage miki aji?

Safiya tana murmushi tace yaya kamal kenan, har akwai wani aji da mace takeda shi daya wuce hijabinta?  nuna ado, kwalliya da tsiraici ai anan zubda aji yake kuma na tabbata ko kaine bazaka so kasayi alawarda aka budeta kuda da kura da datti suka hau kaiba....

Kamal yace any way abinda kika fada ya danyi ma'ana duk da kinsan ni ba hausan nake fahimtaba inyayi zurfi, ni zantafi ga tsarabarki inji hajiya. Nizantafi kigaida mutanen gida

Safiya tace toh nagode Sosai Allah yakai ka lafiya

Bayan barin gidansu safiya, kamal gida ya wuce kai tsaye, shigarsa keda wuya yaji mum and dad ɗinsa suna cacar baki kamar de yanda aka saba, hakan yasa be karisa cikiba seya tsaya abakin kofar parlour adai dai lokacin yaji mahaifiyarsa tana cewa wai mesa kullum aka tashi magana sekace wai nice na ɓata yaran nan sekace nice kadai na haifeshi, kai mesa baka gyara shiba in hakane?

Baban kamal yace sanin kanki ne ina iya bakin kokarina wajen tarbiyan ki da ɗanki amma kasancewar ina yawan tafiye tafiye hakan yasa kike amfanida rashin zaman danakeyi kike rusa duk wani tarbiya danakeyi masa, yanzu ke idan bazaki zama mace tagari ga mijinkiba ai yakamata kizama uwa tagari ga danki, sabida shakkun tarbiyanki yasa kobana gari ninake tashinsa sallan asuba ta waya.  sannan nasashi islamiya amma sam baki damu da yaje ba kemafa nasaki amma kikace wai local mutanene awajen ke bazaki iya hada jiki dasuba..

Maman kamal tace to Meye laifina dannace local mutane ne ai gaskiya nafaɗa kuma karatu inde ansamu na sallah ba shikkenan ba

Baban kamal yace ina rokon Allah kada kamal yasamu Matar aure irinki samira, kekuma Allah ya shiryeki, amma kisani girman kai bazai haifarmiki da komaiba se kaskanci

Maman kamal tace shikkenan kanka akeji

Baban kamal harya juya zai fita seya dawo ya matso kusa da ita yace har cikin raina banaso ina biyemiki amma dole kike sani magana, zan cigabada yimiki addu'a Allah yarabaki da wannan zafin kishin konima na huta. zanfita idan kamal ya dawo kice inasan ganinsa kada yaje ko ina harse na dawo.
Da kamal yaji baban sa na fitowa seya ɓuya a bayan ƙofa, bayan fitar mahaifinsa seya shiga ciki yasamu maman sa tanata hucin zuciyata amma se yayi kamar besan meya faruba, yana isa gurinta yayita mata raha yana bata labarai na barkwanci har ɓacin ranta ya gush. daga bisani ta isar masa da saƙon mahaifinsa..

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now