Page 22

19 3 0
                                    

Safiya tace hmm salma kenan, duk randa kika faɗa soyayya zaki fahimci abunda nake fadamiki. Salma tayi murmushi sannan tace meye abun daɗi a soyayya banda wahala da damuwa dakuma kuncin zuciya, babu abunda soyayya ya iya irin tarwatsa zuciyar masoyi da buri marar misaltuwa da mafarkin samun abunda kakeso koda kuwa babu damar hakan, safiya inda ace inada iko to bazanbari soyayya ta rabi zuciyataba balle har nakasa cireta, so baya neman izini sannan baya neman ɗan jagora sannan baya karɓan uzuri balle yayiwa mutum kara koya mahimmance shi..

Safiya tayi mamakin jin wa'en nan kalaman daga bakin ƙawarta sai tace salma maganganunki ya nunamin alamun akwai wanda kike so kuma kinyi zurfi cikin sansa hasalima kin kasa mantawa dashi to amma gaskiya ni dai a nawa ganin soyayya shike samar da farin ciki azuciya, soyayya yake maida bawa yazamo tamkar sarki sannan ya maida baƙo tamkar dangari. watakila bansan abubuwa dayawaba a soyayya ba amma tawa soyayyar ta dabance kuma ina alfahari da ita💖

Salma tayi murmushi sannan tace safiya kenan kada ki yaudari kanki keda haryanzu bai san kinayi ba shine kike wani jin daɗi dan kina sanshi meye amfanin san maso wani kuma mesa kike son kamal sosai haka?

Safiya tace salma ai ita soyayya baruwanta da dokoki ko sharuɗa, duk dacewar yaya kamal bai san inayiba kuma yaki bani daman mu zauna muyi magana kodan na faɗamasa irin sanda nakeyi masa. ba dare ba rana kullum ƙara sonsa nakeyi araina, wallahi salma ina matukar kaunarsa kuma shirunsa agareni naɗaukeshi ne amatsayin amsar yana sona sai dai akwai abunda yake dakatar dashi daga nunamun wannan soyayyar. Salma tace mai sa kika bari sonsa ya shiga zuciyarki haka harkike tinanin yana sanki duk da bai faɗamiki ba? 

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace so baya neman izini kafin ya shiga zuciya, so kamar shukace da take yaɗo a gona musamman lokacin damuna, dalilin dayasa nake san yaya kamal bazasu kirguba. yaya kamal shine irin mijin da nayiwa kaina tanadin samu sannan shine irin ubanda nayiwa 'ya'yana burin samu, salma ina sanshi sabida mutumin kirki ne, yaya kamal ya canza fiye da tsammanin ki yazama tamkar zuma ko madara, dabi'u me kyau, halaye nagari, kamala, sanin yakamata, neman ilimi da kokarin aiki dashi, hankali, nitsuwa, sannna ga kyan sura da halitta, salma bana fahimtar irin narkewanda zuciya tayi akansa sai naji yana tilawar Alqur'ani mai girma, wallahi duk jikina sai ya amsa take hawayen daɗi da farin ciki ke zuba daga idanuwana. Sannan idan yayi murmushi sai kiga fuskarsa tacika da annuri da sheƙi yana walkiya, salma bana gajiya da kallonsa dare ko rana duk sanda na dauki wayata sai naga hotonsa gashida kamun kai ga biyayya da girmama nagaba, tinda muke bai taɓa ɓatamun raiba. Salma kamal shine irin mijinda idan yana sona zai riƙeni da soyayya idan baya sona zai riƙeni da mutunci da girmamawa dan haka bazan taɓa sarewa akan soyayyar saba💕

Tirƙashi salma tafaɗa a zuciyarta sannan tace anya zan iya sadaukar da soyayyata kuwa

Safiya taɗan bugi salma tace tinanin meye kikeyi haka?

Salma tace safiya zakiya iya sadaukar da soyayyarki ga wata macen daban musamman ma idan kamal yace ita yakeso?

Safiya tazabura tace har abada bazantaba yiba, sabida mutum kamar yaya kamal ba irin sauran maza bane samun irinsu bashida sauki salma, dan haka bazantaɓa bari wata mace ta kwacemin shi ba. Salma bansan sau nawa nayi istikhara akan yaya kamal ba amma duk kwanan duniya ƙara shiga raina yakeyi, mutumne mai wasa da dariya akwai fara'a da zolaya yana da daɗin zama sabida ya iya zama da mutane shiyasa duk dacewar inajin zafin kasancewar bai taba cewa yana sona ba amma inajin daɗin kasancewar ina jiran wanda ya dace ajirashi, dan haka babu wacce ta isa nabarmata yaya kamal aduniyan nan koda ace yana santa💘

Salma tace safiya koda kuwa Salma ce?

safiya tace koda kece salma😒. Bazan taɓa barmiki yaya kamal ba I'm sorry💔sannan safiya tace salma kada kiyi mamaki dan nace haka, soyayya ta tanada tsadadda tafi karfin nabarta sabida wata mace, sannan yaya kamal mijin mace huɗu ne mai sa zan hakura alhalin inada daman samun Shi koda matansa uku ne! zan iya shiga gidansa ata huɗu.
Salma banso yaya kamal dan watarana na barshi ba, na soshi ne dan narayu da shi a duniya da kuma aljannah in sha Allah, idan kuma yaso wata macen sai ya auremu duka.

Salma tace kenan zaki amince amiki kishiya? Sai safiya tace eh zan amince sabida farin cikin sa shine nawa, matuƙar zai samu kwanciyar hankali daga wajenta kuma yana santa to banda damuwa danni "all what i care for is his well being" 💞

Salma tayi murmushi sannan tace  tabɗi jam, gaskiya safiya kina san kamal sosai

Safiya taɗanyi dariya sanna tace kamar yadda kema kike sansa ba..

Salma tace "bad joke" mainsa kikace haka?

Bayan tayi ɗan ajiyan zuciya sai tace salma najima ina hasashen ke da yaya kamal kuna son juna gashi yau naji daga bakinki dan haka yanzu ya rage tsakaninmu ni da ke mu auri yaya kamal muzauna a matsayin matansa ko kuma kowacce nata ya fishsheta..
Salma tabuɗe baki tana kallon safiya cikin mamaki, daƙyar tace wai yaushe na cemiki ina sanshi ne?

Safiya tace nagane hakan akalamanki dan haka idan yaya kamal yace bazai iya aurenmu duka ba zanjanye maganar aurensa dan ya aureki mutukar hakan shine zai samar masa da kwanciyar hankali, burina shine yakasance cikin farin ciki duk da cewar burin masoya ne son kasancewa tare da juna amma ba dukkan masoya ne suke iya sadaukar da burinsu dan farin cikin wanda sukeso ba!

Salma dai ba abunda ya rage tayi face ta yaye labulen dake tsakaninta da soyayyarta, cikin ƙwarin guiwa salma tace safiya nayita ƙokarin mantawa dashi amma nakasa, kowani lokaci yana raina sannan duk abinda ke zagaye dani suna tinamin dashi, ina matukar kaunarsa kuma ayanzu I feel like i can't give up on him anymore...

Safiya ta dubi salma tace mata then fight for it, fight for your love...  but remember i cant let you take him away from me so easily my dear💕💞

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now