Page 20

21 3 0
                                    

Rayuwa kenan! Akwana atashi bayan shudewar shekara biyar kenan kamar wasa salma ta kammala karatunta nagaba da secondary harta fara aikin koyarwa awata makaranta dake unguwarsu..

safiya ma tayi nasarar kammala katunta a makarantar horar da malaman lafiya wato nursing school. kazalika shima Kamal ya ɗaura daga inda ya tsaya haryazama korarren likita me lasisi kuma likitan sunnah domin kamal ya canza yazama ahlussunnah nagaske kai kace wani kaml ɗinne daban bashiba, farin cikin hakan yasa mahaifinshi ya buɗe masa private hospital nashi nakanshi anda zai fara aiki a matsayinsa na likita.

To amma ko ya labarin soyayyarsa da salma dakuma aurensa da safiya?

Salma na kwance aɗaki takasa bacci misalin ƙarfe biyu da rabi na dare sai taji mahaifiyarta hajiya bilkisu tayi sallama, salma ta amsa da walaikummus-salam sannan tacemama bakiyi bacci ba?

Maman salma ta dubi fuskar ƴarta dake cikeda damuwa ga alaman hawaye a kuncinta gakuma idanunta duk sunyi jawur. Bayan hajiya bilkisu tazauna kusada ita seai tace salma kenan ai nice yamata namiki wannan tambayar. me kikeyi haryanzu bakiyi bacci ba?

Salma tace na tashi nayi sallah ne sai kuma baccin yaƙi zuwa shine kawai nafara karatu

Maman salma taɗan numfasa sannan tace salma kenan, ina iya karanta damuwa a fuskarki, kuka kuma daga muryarki, dan haka faɗamun maya faru?

Salma tace jiya safiya ta karbo results dinta kuma yayi kyau sosai sannan Kamal zai bata aiki a asibitin shi, yanzu ba abinda ya saura face safiya ta cika burinta na auran kamal, su rayu cikin farin ciki da ƙaunar juna..
hajiya bilkisu tace hakane kam, wato salma rayuwa dakike gani tana juyawane tareda kaddara kowa da abinda Allah ya tsara masa, kamar yau na haifeku gashi harkun girma afra tayi aure da ɗanta sultan, wai nima nazama kaka ikon Allah kenan. Salma tayi murmushi sannan tace hakane mama, lokaci yana tafiya da sauri. Sai maman tace ba lokacine ke tafiyaba mune muke tafiya dan shi lokaci kamar guzuri ne yayinda na wani ke ƙarewa yayinda wani ke fara haɗa nas.
Salma mai zai hana kibawa alhaji kabir daman aurenki, mutum ne me nagarta, har yau bana manta kyautar dubu goma, goma daya baku ranar bikin kammala secondary school dinku ku biyar sabida shigar kamala da kukai ya burgeshi kuma haryanzu yanata binki amma sam baki bashi damaba

Salma tace hakane mama mutumin kirki ne, amma yakasa mayemun gurbin kamal a raina, haryanzu ina sanshi inasan kamal sosai mama amma zan cigabada addu'a danna manta dashi..

cikin sanyin jiji haijya bilkisu tasa hanu tashare hawayen dake zuba a fuskar salma sannan tace nakasa fahimtar al'amarinku, Kamal yana sanki kema kina sanshi amma kinkasa karbar soyayyar sa sabida safiya tana sanshi....

Sannan shima kamal ɗin yakasa karɓar soyayyar safiya sabida yana jiranki kibashi dama. wannan halinda kike ciki yayi kamada halinda na tsincikaina aciki lokacin ina budurwa kafin na auri kahaifinki

Salma tanajin haka sai ta ɗan gyara zama sannan tace mama kema kinsamu jarrabawa a soyayya ne?

Maman salma tace ai jarrabawar soyayya wani matakine na rayuwa dakusan kowani ɗan adam yake shiga lokacin kuruciya...

Mahaifiyar salma tafara bawa 'ƴar ta labari kamar haka, akwai wani saurayi mai kyan dabi'u da halaye da aka kaishi makarantarmu ya rubuta waec tareda mu shine saurayinda nafara so a rayuwata kasancewarsa mutum ne shiru shiru kuma haziki, yayita bina danmuyi soyayya kullum cewa yakeyi ina burgeshi dan halinmu yazo daya amma bantaɓa bashi daman hakanba kasancewar kawata tafadamun tana sansa, bayan mungama school bai hakuraba nikuma alokacin nakasa jure rabuwa dashi sai na karɓi soyayyarsa, sai yace zai turo gidanmu neman aurena dan haka nafaɗawa babana inya amince se ayi mana aure mutafi ƙasar waje tare muci gabada karatu, dafarko har babana ya amince amma bayan iyayensa sun zo sai ya nuna bai san maganarba, sai dai lokacinda kishiyar mahaifiyata take fadamasa batasan auren dan haka kada ya amince dukna jisu, kamar wasa haka aka rabani dashi, amma bayan wasu lokaci sai na nemeshi awaya na nemi alfarman ya nemi auran kawata dannasan tana sanshi kuma zata karbeshi, dafari yaki amincewa amma dana nace masa daneman alfarman seya amince bayan watanni uku zuwa huɗu inaji ina gani aka ɗaura auren ƙawata da wanda nakeso

Salma tace ikon Allah kenan, amma mama ya kikai?

Sai maman salma tace; "bayan wasu shekaru na haɗuda da babanku seya mayemun gurbin wanda na rasa kamarma bantaba sonshi ba, shiyasa nake fadamiki kibawa wani dama sai ya maye miki gurbin kamal dan soyayya shiyake maye gurbin sayayya. Salma tace to mama zan gwada kozan iya. Maman salma tace zaki iya in sha Allah, Allah ya miki albarka. Salma tace amin mama.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now