Page 10

23 3 0
                                    

Baban Salma na zaune a ɗakinsa yana karin kumallo kamar yadda yace yana so yaci a ɗaki shi kaɗai, sai dai  Hajiya Bilkisu ta matsa sai ta zauna ko dan tasha labari domin duk sanda baban Salma zai ci ɗanwake to za'asha labari sosai.
Bayan yakai lomar farko sai ya juyo yace "wato Hajiya Bilki nakan yi mamakin yadda ɗanwake ya ke kasancewa mai daɗi haka."

Maman Salma kamar za ta yi dariya amma ta hadiye tace "gaskiya kam abun mamaki ne, amma baka ganin hakan ma wata rahamace ta Allah da yasa abinci mai sauƙin sarrafawa yake da daɗin ɗanɗano wanda marassa ƙarfi daga cikin bayinsa za su iya ci.

Baban Salma yaɗan gyaɗa kai sannan yace "gaskiya nima na yi tunanin haka, kuma abunda zaki duba shine a iya bincike na dana yi, wato Hajiya Bilki babu abincin da yake da tarin masoya irin miyar kuka da danwake"

"Ikon Allah, toh amma your Excellency akwai wani shafi ne na musamman da ake binciken ko ya a kai ka gane!?"

Baban Salma ya ƙara kai wani loman yace "babu wani shafi kawai a bakunan mutane naji"

Maman salma tace "hakane kam, to ai ina ganin saboda akwai alaƙa a tsakaninsu shi yasa"

Baban Salma yace "babu mamaki, Hajiya Bilki kin san dalilin da yasa haryanzu ban ƙara aure ba?"

Hajiya Bilkisu tace "na sani ranka ya dade, na farko dai zai yi wuya a irin yaran zamanin nan ka samu wacce za ka auro ta iya yi maka danwake mai taushi, santsi da kuma tsafta badan na kushe su ba. Na biyu kuma babu mai iya jure fushinka da yawan faɗanka in ba ni ba."

Baban Salma yace "hakane, Hajiya abunda ki ka faɗa koda zolayata ki kai toh gaskiya ne, na san kina hakuri dani sosai kuma ina miki godiya Allah ya miki albarka sannan ina alfahari da samunki a matsayi mata ta."

Maman Salma tace "harka manta fushin kenan, yanzu kuma alfahari ake yi dani?

Baban Salma yace "dan Allah ki yi haƙuri, kin sanni da saurin hawa kuma idan nayi fushi bana tauna magana nake furtawa; amma kema kin sani ina sanki kuma ina matuƙar ƙaunarki."

Maman Salma tace "idan ni na sani kuma na fahimceka, toh 'ya'yanka ba zasu fahimceka ba, bana so su yi tunanin kana muzgunawa mahaifiyarsu da harshenka domin hakan zai samar da tabo a zuciyarsu game da kai; da haka nake roƙonka dan Allah kana ƙokarin kame harshenka a gaban su."

Baban Salma yace "toh shikkenan zan gyara kuma a taya ni da addu'a please"

Maman Salma tace "kullum ina yi, kuma wato in da za kabi laduban da akace mai fushi yabi toh watarana zaka nemi saurin fushin gabaɗaya karasa"

"To fa, kaji manya, fushin har wasu ladubba yakeda shi?" Baban Salma ya faɗa.

Hajiya Bilkisu tace "kwarai kuwa, akace idan mutum yayi fushi to ya kori shaiɗan, in yana tsaye ya zauna, idan yana zaune to ya kwanta, idan abun ya gagara ya yi alwala ko ya ɗan fita daga gidan na ɗan wani lokaci in ya huce sai ya dawo."

Baban Salma yace "zan gwada in sha Allah, Hajiya Bilki ke ce fitilan dake haskaka gidana ranar da bakya ciki tabbas gidan zai yi duhu."

Hajiya Bilkisu tace "to mai zai hana fittullun su zama biyu ranar da aka rasa ɗaya sai ɗayan ya maye gurbinsa, ka tayani haskaka gidanka baban Salma."

Baban Salma ya ɗanyi murmushi sannan yace "ki fadi duk abunda ki ke so na miki alkawarin zanyi matukar zai faranta miki rai."

Tana jin haka ta gyara zama sannna tace "Da farko dai zan fara da yi maka godiya tsawon zama na a gidanka ban taba rasa ci, sha da sutura ba dangina, kawayena harda makwabta na alkhairinka ya yi naso ya isa zuwa garesu. Na gode baban Salma Allah yasa kafi haka, Allah ya karemun kai ya albarkaci rayuwarka da zuriyyarka."

Baban Salma yace "Aamin uwargidata Hajiya Bilki, wannan ai hakkine akai na da ya kamata na sauƙe dan haka dole nayi iyakar ƙoƙarina."

Maman Salma tace "duk da haka, ba kowani mijine ke yin hakan ba, sai kuma abu na biyu, baban Salma sallar asuba yana maka wahala baka iya tashi a kan lokaci kuma hakan ya samo asali ne saboda rashin kwanciya barci da wuri da za ka rage hiran dere musamman kallo in sha Allahu zaka samu barci wadatacce kuma za ka iya tashi salla akan lokaci."

Sai kuma abu na uku, ka yi nisa da Alqur'ani baban Salma zan so ace kana tilawan ko da shafi daya ne kullum, kuma a sati ace kana zuwa majalisin da ake karatun addini ko da sau daya ne."

sai abu na gaba shine yawan jin wake-wake a motarka, ka san kiɗa da karatu basa haɗuwa duk gurin da aka rike daya to tabbas dayan zai tafi zanso ace ka maye gurbin shi da wa'azin malaman sunnah da kuma karatun Alqur'ani mai girma."

Baban Salma yace "sai kuma abu ɗaya dakika manta"

"Me kenan?" Hajiya Bilkisu ta faɗa.

Baban Salma yace mata "sallan dare, duk sanda ki ka tashi mun nasiha sai kin haɗa da shi ya akai yau ki ka manta?"

Maman Salma ta ɗanyi murmushi sanna tace "yau ɗinma ban manta ba kawai dai na yi shiru ne kada na wuce gona da iri dan an bani dama."

Baban Salma yace "kaji sarkin hikima, Hajiya Bilki kenan! Kawo mun ruwan sanyi nasha."

Maman Salma tace "ko dai ruwan ɗumi kasanfa yanzu kaci maiƙo bai kamata kasha ruwan sanyi ba, barin kawo maka shayi"

"Duk abunda ki kace haka za'ayi" Baban Salma ya faɗa cikin murmushi.

"Har ta doshi kofar daƙin zata fita sai taji yace "Bilkisu, I love you for ever and ever and ever!"

"Kamar a mafarki Hajiya Bilkisu taji kalaman mijinta, cikin mamaki da farin ciki ta juyo tace masa "I love you more my dear."

Masha Allah, yaufa ɗanwake ya tada tsohon soyayya. Ku kasance da sauran labarin a @faty saje wattpad.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now