Page 25

30 3 0
                                    

Cikin sanyin jiki safiya tayiwa maman kamal sallama a ɗakinta, hajiya samira ta mata izinin shiga, sai ta fara mata magana cikin girmamawa. "Adda dama nazo nayi magana dake akan yaya kamal... sai hajiya samira tace wani abun ya miki?

Safiya taɗan gyara zama sannan tace a'a bai mun komai ba, amma ina so ne namiki godiya akan dukkan tai makon da kika min a rayuwata, kin mayemun gurbin mahaifiyata kin ɗauki dukkan ɗawainiyata kuma kin zaɓamun abokin rayuwa nagari kuma abun alfahari ga duk macen da ta sameshi, gaskiya banda kalamanda zasu iya nuna farin cikin da na ke ciki sai dai kawai nayita miki addu'a da fatan alkhairi...

Maman kamal tace safiya kenan, ba komai ai nice nayi sa an samun suruka kamarki Allah dai ya nuna mana bikinku da rai da lafiya dakuma imani..

Safiya tace amin, sannan taƙara dacewa adda nasan kinasan yaya kamal fiye da tsammanina kuma babu abinda kike so kamar farin cikin sa, shiyasa nazo nai man alfarmarki,  nasan cewar yaya kamal Allah ya jarabceshi da san salma kuma salma. Kuma adda na san salna ƙawata ce nasan halinta mutumiyar kirki ce sannan zatasa farinciki a rayuwar yaya kamal kamar yadda nima zanyi,  shiyasa nake san dan Allah kiyi hakuri ki bashi daman aurenta na miki alkawarin zamu zauna lafiya..

Cikin kakkausar murya hajiya samira tace ashe safiya bakida wayo? Yanzu ke ce ki ke cewa kamal ya auri salma ayimiki kishiya kenan?

Safiya ta tsorata!  muryatta na rawa tace bawai ina san kishiya bane kawai dai inaso yaya kamal yasamu abunda yake so ne, farin cikin sa shi ne nawa. kuma salma mutumiyar kirki ce tanada hali mai kyau ga tarbiyya...

Maman kamal tace rufe mun baki ai kasancewarta babu abinda ta rasa shine zai zama barazana ga soyayyar ki sannan zata iya amfani da dukkan abunda zata iya dan kwace kamal daga gurinki

Safiya ta sake cewa nima zanyi iya ƙoƙarina wajen mallakar zuciyar sa, abunda nake nema shine adda dan Allah kada ki hana yaya kamal auren salma.. safiya tagama ƙure haƙƙurin hajiya samira dan haka tace mata  tashi ki fita safiya, dan na fahimci bazaki taɓa fahimtar yanda mace takeji yayinda take rayuwa da mijin da zuciyarsa ke tare da wata ba...

Safiya tace kiyi hakuri adda amma idan na auri yaya kamal zai rayu da nine azahiri amma a zuciyarsa da salma zai rayu, shiyasa nakesan gara ya aureta dan muzauna tare kinga sai na samu daman mallakar zuciyarsa. 

tirƙashi yau tarihi yana mai-maita kansa. Adda tagama zuwa wuya saboda ɓacin rai abunda ta iya faɗa shine "you may leave" ta nunawa safiya hanyar ƙofa.. Safiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tace I'm sorry, i'm so sorry!

buɗe kofar ɗakin ke da wuya sai tayi kiciɓis da baban kamal zai shiga, cikin girmamawa ta gaisa dashi ya samata albarka sannan ta koma dakinta shikuma yashiga ciki. Bayan shigarsa ɗakin sai yace mata naji duk abunda kuka tattauna tsakaninki da safiya, sannan sai yayi ƙoƙarin shawo kanta amma kishinta da hajiya bilkisu ya hanata fahimtar gaskiya (yaude tsohon hali ya tashi)

Baban kamal ya ci gaba da rarrashinta harma yake cewa hajiya samira bansan waye yafi sa'a tsakaninki da kamal ba akan samun Safiya, kinsamu surakadda farin cikin ɗanki shine priority dinta bakamar mafi yawa daga matan zamani ba sannan shikuma kamal ya samu matarda ta fahimci soyayyar sa ga salma harma take tai maka masa wajen mallakar abunda yakeso duk da hakan yana sosa mata zuciya amma ta daure, duk dacewar tana kishin sa...
Maman kamal tadubi mijinta tace wato yasamu wacce ta fahimce shi bakamar niba ko?

Baban kamal yace ai kinji matsalarki!  hajiya samira ki dai na azabtar da ɗanki akan abunda ya wuce, kuma ni banga amfanin kishi da bilkisu ba ke ce kika aureni dake nasamu ɗa abun alfahari sannan har yau muna tare kuma ina ƙaunarki, abunda baki ganeba shine soyayya idan ba aure baida amfani sannan shima aure idan ba soyayya da ƙaunar juna kamar abinci ne babu ɗanɗano dan haka ki amince da auren yarannan dan Allah

Maman kamal tace "hm" cikin sauki kake faɗa saboda bakasan irin ƙunci da wahalar dana sha ba bayan aurenmu, kullum kana cikin tinanin bilkisu ba dare ba rana ko magana zakai mun sai naji ka ambaceni da sunanta cikin dare baka iya bacci sai dai kasa hotonta agaba kana zubadda hawaye sekace itace autar mata, nadauka  kana sona shiyasa ka aureni amma sam ba hakabane bilkisu kake so ba samira ba..

ganin yanda hankalinta ya tashi sai ya kwantar da nashi ya matso kusa da ita ya kama hannunta ya zaunar da ita yasa hanunsa ya share mata hawaye sannan ya ɗauko ruwa ya bata a baki tasha bayan ya ajiye cup din ruwan sai ya juyo yana kallon fuskarta yace hajiya samira ina miki rantsuwa babu wacce nakeso a zuciyata ayanzu kamarki nasan nashiga jarrabawar soyayya abaya amma tin lokacin da bilkisu tayi aure nayita rokon Allah ya ciremun ita a raina sannan ya mayemun gurbinta da ƙaunarki matata.
kiyi hakuri nasan ban kyauta mikiba a baya amma yakamata kimin uzuri ki fahimce ni rabuwa da wacce zuciya takamu da santa cikin ƙaramin lokaci ba abu bane mai sauki

Maman kamal tace shikkenan, amma yau zanyi maka tambayadda ban taɓa yimaka ba, mai ya sa baka auri bilkisu ba ka aureni?

Baban kamal yakoma bakin gado yazauna sannan yacemata mahaifinta ne yaƙi amincewa da auran..

Dafari yabani damar turo magabatana, nayi murna sosai hakan yasa cikin sauri na sanar a gida sai mahaifina da ƙaninsa sukaje har gida wajensa amma bayan sunje sai yace bai san da maganar ba harma ya ce musu shifa yayiwa 'yarsa miji cikin ɓacin rai suka dawo gida sukaitamin faɗa a zatonsu ƙarya nayi musu, hankalina ya tashi sosai naje gida gurinta dannaji me ke faruwa sai nasamu tana kuka takasamun bayani, kuma babanta yamin koran kare kamar bai sanniba, bayan wani lokaci takirani tafaɗamun cewar kishiyar mamantace tahaɗa munafunci har baban ya fasa bani aurenta.

Bayan kaman wata uku sai ta sake kirana dan tabani labarin irin sanda ki ke mun tin muna school kuma tace dan Allah nakarɓi soyayyar ki na aureki zaki kula dani kuma dukkanmu zamu kasance cikin farin ciki, dafari naji nauyin hakan saboda kawayene ku amma daga baya sai na amince saboda kema kinkai a soki samira kuma bazanso ki rasa wanda kike so ba kamar yanda na rasa, sai dai kash mai makon ki maida hankalinki wajen mallakar zuciyata sai ki ka sa kishi a ranki kullum faɗa,  hakan yasa kullum nake cikin tinanin bilkisu kuma zuciyata ta keta nesa da ke, amma danayyita addu'a sai komai ya yayi sauƙi sannan namanta da komai..

Haƙiƙa wannan labarin ya sosa zuciyar hajiya samira, take hawaye suka fara zuba daga idanunta da ƙyar ta buɗe baki tacewa mijinta inaso naga bilkisu dan Allah kakaini gurinta😭

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now