Page 23

19 3 0
                                    

Afra wallahi safiya duk ta canzamin tazama kamar ba itaba kokaɗan yanzu ba a matsayin ƙawa take kallonaba, a matsayin kishiya ta ɗaukeni kokuma nace  ta zama barazana ga soyayyata da kamal. Afra ji nake kamar sati mai zuwa a ɗauramana aure da kamal kowa ya huta..

"Hahhaha" alamar dariya kenan da afra tayiwa salma dake zaune a bakin gado cikin damuwa da tinanin yanda zatayi da rival ɗinta a soyayya kuma aminiyarta a al'amarin yau da kullum. Bayan afra tajawa dariyatta burki sai tace ke da safiya wanda ya shiga tsakaninku shi zai ji kunya amma faɗamun mai ya faru? Salma tace daɗina da ke sai ana abun arziki sai kiyita yiwa mutane dariya! Salma tacigabada bawa afra labari kamar haka"yau sati ɗaya kenan tinda nace mata ina son kamal shikkenan ta canzamin kusan kullum sai ta kirani kotamin text massage wai yaya kamal ya bata gift, ko kuma in tayi kwalliya sai ta turomin pictures dinta wai nagani ko wankan yayi sometimes kirana take awaya wai zasuje shopping koda abunda nakeso nafaɗa akawomin, Jiyafa picture shi tamin sending wai see how handsome he looked.
😂dariyar afra ce takatse salma daga magana, cikin ɓacin rai tace afra idan kika sakemin dariya zan dai na baki labarin nan dannaga alama ke ko kaɗan baki ɗauki abun serious ba. Afra tace i'm sorry! abunne kamar amafarki, wai anty safiya dama haka take? gaskiya akwai aiki jawur a gabanki dan gaskiya anty salma sai kinyi dagaske..
salma tace hmm na rasa yadda zanyi, kuma ba abinda yake ɗagamin hankali kamar idan na tina gidansu ɗaya kullum suna tare gashi tana masifar son sa..
Afra taɗanyi shiru naɗan lokaci sannan tace anty salma dole hankalinki ya tashi dan maganar gaskiya anty safiya yanzu rival dinki ce ba ƙawa ba, dan haka dolene kema ki waye kifara rama abunda take miki idan kuma ba hakaba to kinaji kina gani zata kwace miki yaya kamal tabarki da ciwon so! Salma tace to yanzu meye abunyi kenna?

Afra taɗan gyara zama sannan tace kingade yaya kamal yana sanki sabida haka matsalarki mai sauki ne, kawai ki nemi izini agun baba yafara zuwa gida kuna gaisawa kuma a ganina baba zaiji daɗi tinda ɗan abokinsa ne idan yaya kamal yazo sai ki faɗa masa abunda yake ranki gameda shi. Salma tace haba afra gaskiya bazan iya ba, kunyan shi nakeji kuma yanamin kwarjini gaskiya ki canza shawara🙄

Afra tace Allah nagode maka wai anty salma dan Allah yaushe zaki canza ne, dolenefa kisan yadda zakiyi yasan kina sansa inba hakaba zai karbi soyayyan Safiya ya aureta kuma babu yanda kika iya.
salma tace bar zancen Safiya yana tayarmun da hankali, shikkenan zankirashi ammafa bazan iya faɗa masaba sai dai nabi wani hanyar..

Afra tace to shikkenan ai dama yaren so yana dayawa, sai ki siya masa gift like tirare ko set na handkerchief da sauransu ko pen ma akwai masu kyau gwanin sha'awa. kuma bawai gift dinne abun dubawa ba abunda ke kunshe dashi na sako shine abun dubawa abunda akeso saƙon ya isa. Salma tace yauwa ƙanwata, yanzude muje ki rakani gun baban tukun.

Bayan salma da afra sun samu izinin zuwan kamal gida sai suka siyowa kamal abunda take ganin ya dace dashi, sannan ta kirashi a waya tamasa gayyata ta musamman. Kamal yayi farin cikin jin haka daga salma annashuwa ya bayyana karara a fuskarsa hakan yasa Safiya ta fahimci akwai wani abu, bayan dawowar kamal gida daga gun aiki misalalin karfe shida na yamma sai ya shirya cikin ado yanata faman kai koma a parlor yana duba yanayin shigarsa. Cikin dabara safiya taɗauko shayi takawo masa , kamal yace nagode da shayi amma kiyi hakuri bazan iya shan komaiba yanzu dan zanje sallan magrib amma innadawo zankiraki sai ki kawomin. Safiya taɗanyi murmushi sannan tace ba komai yaya kamal Allah yadawo dakai lafiya kamal yace amin, harta juya zata fita sai ta juyo tace anya yaya kamal sallan kaɗai zakaje kuwa? Se kamal yace zanje anguwa amma sai nayi sallan isha'i, akwai abunda kike buƙatane?

Safiya tace a'a ba komai Allah ya tsare hanya nizan shiga ciki. Safiya tana shiga ɗakinta sai ta ɗau waya takira salma, a daidai wannan lokacin salma na alwala taji wayanta na ƙara bayan tafito daga bayi sai ta duba wayan tana ɗagawa sai taga missed call ɗin safiy, bayan salma ta idar da salla sai ta kirata, tana ɗagawa tace dagajin muryarki kina cikin farin ciki ko dai wani abun kike shiryawa ne salma. salma tace kwarai kuwa! nayanke shawaran bayyana masa saƙon zuciyata shiyasa nace yazo gida inasan ganinshi dan haka nan da wasu mintuna zaki nemeshi a gidan ki rasa. Tsoro ya bayyana a muryar safiya in da take cewa salma me kike nufi? Salma taɗanyi murmushi sannan tace inada abun yi sai anjima.

Bayan salma ta katse wayan sai safiya tashiga tinanin yanda zata sa yaya kamal ya fasa zuwa gun salma, akarshe dai ta yanke shawaran faɗuwa kasa tayi suman karya. Tana ganin maman kamal tafito sai tasa salati da karfi ta yanki jiki ta faɗi kasa, hankalin adda ya tashi sosai kamal ya ɗauko mota suka tafi asibiti.  bayan shuɗewan wani lokaci salma na tajira sai ta yanke shawaran kiran kamal a waya, nanfa ya mata bayanin abunda ya faru kuma ya bata hakuri,hakan yasa ta nemi izinin mamanta taje asibitin, bayan sallar isha'i sai salma da hajiya bilkisu suka shirya sukatafi asibitin.  Shigarsu keda wuya salma ta zauna kusa da safiya taƙara matsowa kusada kunnenta tace nasan lafiyarki ƙalau babu abinda yake damunki...

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace gara da kika gane hakan dama kina tsammani zanbarshi yaje gurinki ne?

Salma tace ina baki shawaran ki daina haɗa kanki dani sabida namiki fintinkau dan kuwa nice na mallaki soyayyar sa kekuma lalube kikeyi cikin duhu.
Safiya tace wannan shine matsarki kina maidani ba komaiba kinmanta ance ɗan hakin daka raina shi zai tsonema ido, kuma idan kikaji makaho yanacewa ayi wasan jifa toh ba shakka ya taka dutse. sai salma tace to ai sai mu zuba mugani, ga fili ga me doki.😏

kamal da maman salma sunfahimci yanayin maganar safiya da salma akwai abun dubawa aciki amma sai suka kauda kai. Salma da mamanta sukai sallama da safiya. sun tashi dan su koma gida sai kamal ya rakasu harsuka shiga mota sai da yajira har ya dai na ganin bayan motar sannan ya dawo, yana shigowa ɗaki ya samu mamansa ta dawo daga gurin likita. Kamal yana shigowa ɗakin sai mahaifiyarsa ta masa wani irin kallo sannan tacewa kamal wacece naganku tare?

Kamal yaɗanyi shiru naɗan lokaci sannan yacemata salma ce da mamanta sukazo duba jikin safiya Basu jiraki saboda suna sauri amma sunce a gaidake sosai.. Maman kamal tace ba abunda yashafeni da gaisuwansu sannan ta ɗora dacewa wato haryanzu baka rabuda zancen salma ba ko? to bari kaji yau dinnaan mahifinka yayi magana da baban safiya kuma yace baya san aurenku ya wuce wata ɗaya dan haka ka mance da Salma arayuwarka dan safiya itace matarka ba salmaba.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now