Page 2

84 10 0
                                    

(Makarantar su Salma)

Malamin koyarda harshen turanci kenan a aji, wayewar garin laraba; bayan kammla darasi ya cike lokacinsa da bawa ɗalibai aikin gida kamar haka...
"Your assignment question is "write a letter to your friend telling him/her how you spend your last term holiday" not less than 350 words, to be submitted on Monday morning."

Fitarsa daga aji keda wuya ɗalibai suka hau mita musamman ma Zubaida wacce ta fita zakka gurin fitina da rashin ji."

Zubaida tace "hmm" nifa abun malamin nan ya fara isata kullum a rubuta saƙo sai kace sabon shiga a soyayyah."

Khadija tace "ko kema kya fada, wannan shine karo na biyar kenan da ya bamu irin wannan aikin with different tittle."

Safiya tace "umm kanku ake ji, nifa tun yanzu zan fara nawa aikin; dan muna da biki a gidanmu nasan bazan samu damar yi ba a gida saboda hayaniyar jama'a."

Salma tace "kar dai bikin Anty Naja?"

Safiya tace "eh, kin san da yake hidiman bikin a zariya za'ayi shiyasa babanmu yace kawai baza'ayi wani fitina ba sai dai walima da wa'azi in munje can dangin mamanta dana angon zasuyi shagalin bikin." 

Khadija tace "tab kice bazamu jeba, biki ba shagali meye amfaninsa ki cireni aciki gaskiya."

Zubaida tace "kinsan mu gurin casu muka fi ƙarfi inda za'a baje kolin samari muci ado da kwalliya mu bawa kowa a jikinsa in da bazamuyi asaran jan baki da hoda ba."

Salma tace "Allah ya shiryeku ƴan wahala kawai, samarinda basu suke siyamuku kayan ƙwalliyar ba amma akansu kuke ƙararwa kuma abun haushinma ba'asan kunayiba!"

Zubaida ta ɗan juya ta rintse ido sannan tace "toh malama Salma muna godiya abar na gobe da safe, kinga khady zo ki rakani wajen zaman malamai."

Safiya tace "wai ke zubaida mai yake kai ki gurin malamai ne kusan kullum sai kinje?"

Zubaida tace "Oh Allah ka rabamu da ƴan sa ido na fili dana boye na kusa dana nesa, In kina san sani sai ki biyoni muje tare ki ganewa idonki in yaso kyaji dadin bada labari."

Safiya tace "mai ya yi zafi, adawo lafiya."

Zubaida tace "amin, in da gaske ki ke yi"

Bayan fitarsu Zubaida da Khadija sai Salma da Safiya suka ci gaba da firarsu kamar haka...

Salma tace "kinga rabu dasu kawai mufara aikin da malamin nan ya bayar tun yanzu, dan kin san akwai rubutun da bamu gamaba. Hm dama haka matakin sakandiren yake?  muna gaba yana kara wahala a yi ta tarawa mutum aiki kamar ba gobe?"

Safiya tace "ai gwarama ke Salma mamarki tana taya ki wajen koyan miki abubuwa dayawa, nifa da bani da ita komaina akaina yake wallahi Salma rashin uwa ba abinda ya kaishi zafi" ta fada tana hawaye.

Kalaman Safiya sun sosa zuciyar Salma, tausayin safiya ya kamata sabida Safiya marainiya ce kuma matar mahaifinta bata riƙeta a matsayin ƴa ba.

Cikin sanyin murya da alaman tausayawa Salma ta dubi kawarta Safiya tace "Safiya kiyi hakuri watarana sai labari haƙika kina cikin jarrabawa amma ki sani Allah yana tareda masu hakuri, mamarki kuma adddu'a take buƙata ba kukaba.
kuma ai abinda zaki duba babanku yana ƙaunarki sosai bayasan ɓacin ranki ko kaɗan, dan haka Ki godewa Allah da ya baki mahaifi mai sharemiki hawaye."

Safiya tace "hakane kam Alhamdulillah ala kulli hal, sonda babanmu yakewa mamana gabaya ya dawo kaina bayan rasuwanta. kuma gashi nice mai sunan mamansa wannan dalilin yasa antinmu bata sona wai kishi take yi da ni kuma dai  kin san halina bana mata rashin kunya wallahi ina bata girmanta kuma ina kula da kannena data haifa sosai."

Salma tace "hakane na sani ki ƙara hakuri kin ji ƙawata kuma in ba damuwa ko za ki zo muyi hutun karshen mako a gidanmu sati mai zuwa tunda kince babanki zai yi tafiya? Safiya tace "tab wane ni, yanzu ina zuwa zata samu abun faɗawa mutane tace nafara yawo harda barin gida, kinga shikkenan abun nema ya samu."

Salma tace "hakane kam, toh Allah ya rufa asiri."

Safiya tace "Amin ya hayyu ya qayyum.'

Safiya yarinyar kirki ce halayenta da ɗabi'unta sunyi kama dana Salma hakan ya sa suka zama ƙawaye kuma aminan juna basa rabuwa, safiya ta rasa mahaifiyarta tun batada wayo sosai hakan yasa salma take ƙara janta a jiki.
Sannan akwai Hajiya Samira 'yar uwar mahaifiyar Safiya wacce suka haɗa kaka ɗaya daga ɓangaren mahaifansu maza. Safiya tan kiranta Adda, itace take mata komai na abunda ya shafi gata na wajen uwa data rasa.

Adda ta kasance tana da ɗa guda daya tilo wanda bata kara haihuwa ba bayan shi saboda matsalar da ta samu a mahaifarta.
Mijinta Alhaji Sameer mutum ne mai kuɗi, ɗan kasuwa kuma dan siyasa ne mai gaskiya da amana mutumin kirki mai san taimakon al'uma, Adda tana da kishi sosai da kuma zafin rai shi kansa mijinta hakuri yake yi da al'amarinta amma duk da haka mutum ne tsayayye a gidansa kuma kishin Adda wato Hajiya Samira bai hana shi yi mata kishiya ba wato Hajiya A'isha.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now