Page 6

39 3 0
                                    

(Gidansu Khadija)

Wayewar garin alhamis kenan bayan an tashi daga makaranta Zubaida ta wuce gidansu khadija, a can ta yi wanka ta shirya tsaf ta can-cancaɗa kwalliya kamar ba gobe; shigowar Khadija ɗakin ke da  wuya taga ƙawarta kamar amarya cikin zolaya tace "gaskiya rigar nan ta yi miki kyau kin san an ce kayan aro yafi yiwa mutum kyau"

Zubaida tace "lalle Khadija wato abunnaki harda wulakanci, toh ki fada kowa yaji ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba"

Khadija tace "aiko dai wannan kalmar ba ta dace da mace ba, karki manta watarana ke uwace. Tashi mu tafi na san yanzu haka Ahmad ya isa wajen yana jiranki.

"Gaskiya kam, to muje" Zubaida ta faɗa.

(Gurinsu Ahmad)

Bayan sun isa gurin da suka yi alkawarin haɗuwa da ahmad sai Khadija tace "kinga ɗan halak yana cikin mota yana jiranmu"

Suna isa wajen motan Ahmad ya fito yace sai yanzu? Ai harna fara shirin tafiya dan na jima ina zaune ina jiranku sai kace bani da abun yi.

Zubaida tayi murmushi tace "toh yanzu dai kayi hakuri, kasan mata da kwalliya tun ɗazu nake gaban madubi dan kar na bayyana a gabanka bancika goma ba".

Sarauniyar kyau gaskiya nayi sa'a, ai wannan kwalliya ko ba kice na yi hakuri ba dole zanyi" Ahmad ya faɗa yana murmushi.

Khadija ta ɗan gyaɗa kai ta yi gyaran murya tace "tunda naga kamar banda wani amfani hasalima ba'asan ina gurinba to zai fi min alkairi na yi tafiyata"

Cikin hanzari Ahnad yace "wai dan Allah kiyi hakuri tuba nake ayi min afuwa, barka da yamma ya ya hanya kuma ya hakuri damu?"

Khady tace "lafiya lau, hakuri kuma anata yi kamar yadda aka saba"

Khadija na zo miki da tsaraba fa ina fatan ba za ki bani kunya ba?"

Tayi mamaki tace "ni kuma?, wani irin tsaraba kenan? Allah yasa abun arziki ne dan na sanka da tsokana"

Ahmad yace "wanna karon ba zolaya bane, amma dai bari ki ganewa idanun ki" Take ya buɗe kofar mota sai ta ga wani sarurayi kamar balarabe daganin alama dan gidan manya ne.

Zubaida na ganinshi ya fito daga mota hankalinta ya tash. Ahmad yace "khadija wannan shine tsarabarki, abokina ne ya dawo daga Sudan; ya kawomun ziyara jiya sai mu kai hiranku da shi harma ya ga hotonki a waya ta. Shi ne yace yana san ki kuka in kin amince zai aure ki.
Ni kuma kinsan bana ƙasa a guiwa wajen haɗa masoya saboda haka nace ya shirya yazo ku gaisa ki ji komai daga bakins. Dan haka ga abokina sunansa Zannurain kai kuma ga Khadija sai ku ɗan ja gefe kayimata bayanin saƙon zuciyar ka."

Zannurain suka ɗan ja gefe da khadija suna gaisawa. To amma Zubaida sam abun bai mata daɗi ba dan haka cikin fushi Zubaida ta kalli Ahmad tace masa "kai kuma Ahmad ya haka? Kawai sai ka haɗa mutane soyayya ba ko neman shawara ta baka yi ba?"

Ahmad yace "kinga ni fa ba haɗa su na yi ba, shi ne ya ganta yace yana so ni kuma na masa jagora dan haka banga abun laifi a nanba, kuma ma ke me ye matsalarki bayan naga ita Khadijan bata damu ba kiga yanda take murmushi kin san aboki na zai samu shiga"

Zubaida muryatta ƙasa tace "hm! gaskiya da sake"

Ahmad yace "me ki ka ce? Zubaida tace "ba komai, kawai maganar zucine ya fito fili"
"Amma ya naga duk yanayin ki ya canza ko dai akwai wani abune?"

Zubaida tace "ba komai kawai banajin dadin jikina ne, i think gara mu koma gida yamma tayi sosai"

Ahmad ya yi mamakin yanda Zubaida ta sauya lokaci guda, abun ya sosa masa rai amma sai ya yi ta maza "yace baku jima da zuwa ba fa; kibari suɗan gaisa mana su fahimci juna sai ku tafi." Zubaida tace "ai sun gaisa kawai zamu mutaf."

Ahmad yace "shikkenan, ke ki shiga mota na sai ita Khadija su tafi a motarsa sai su ci gaba da firarsu a hanya." Zubaida tace "a'a kubarshi kawai zamu shiga napep mu koma gida." Cikin nuna soyayya Ahmad yace "to, ai yanda ki kace haka za'ayi."

Zubaida taɗan ɗaga murya tace" Khady zo mu tafi, kaina yafara ciwo." Ahmad ya buɗe kofar mota ya ɗauko wata jaka ya miƙowa Zubaida yace mata "ga tsarabarki nan dana miki alkawari."
Babu murna ko farin ciki a fuskar Zubaida haka tasa hanu takarɓa kamar ba ta so ko godiya batai masa ba."

"Naji duk abunda kace amma ina buƙatan lokaci zanyi shawara, ka bani kwana uku za ka jini in sha Allah; amma kafinnan gaskiya sunnanka yamin tsawo dayawa zan so in kira ka da Nuur."

Zannurain ya ji daɗin yanda Khadija ta ƙarbe shi hanu biyu dan koba komai masu iya magana suka ce "shimfaɗar fuska ta fi ta taburma."

"kina da daman kira na da duk sunan da ki ke so Khadiha." Zannurain yaɗan sa hanu a aljihunsa ya zaro "ƴan canji ya mikowa khadija yace "ga wannan ku biya kudin mota ammafa kiyi hakuri ba yawa."

Khadija tace "daka barshi kawai munada shi"

Zubaida ta yi wuf takarɓa tace "ai ba'a maida hannun kyauta baya mun gode sosai. "

Khadija ta san halin Zubaida sarai shiyasa abun da ta yi bai bata mamakiba, amma ahmad sam bai ji daɗin abunda ta yi ba.

"Allah ya kaiku lafiya, sai munyi waya" Nuur ya faɗa.

Zubaida ta amsa da sauri tace to ba damuwa.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now