Page 16

17 2 0
                                    

Bayan khadija ta kauracewa zubaida a makaranta dakuma gida hakan ya ɓatawa zubaida rai sai ta ɗauki matakin sauka ta inda aka hau, ma'ana ta kaiwa mahaifiyar zubaida ziyara na musamman..

Misalin ƙarfe huɗu kenan bayan sallar la'asar sai zubaida taje gidansu khadija, tana shiga ta taradda maman khadija bakin rijiya tana wanki. Ko sallama zubaida batayiba tabankaɗe ƙofa tashiga sannan ta dubi maman khadija tace mata sannu de...

Maman khadija tabuɗe baki alamar mamaki sannan tace zubaida yau kuma ko sallamar ma babu?

Zubaida taɗan juya ido alamar rashin kunya sannan tace ai baki nemeta ba, nazone naji dalilin dayasa ƴarki ta ƙauracemun takoma ƙawance dasu salma!

Maman khadija tace to marar kunya kina magana dani kamar sa'arki, to cewa tayi tagaji da ƙawance dake shiyasa, nikuma naga bazan tilastata ba dan ba dole bane

Zubaida tace hehehe lalle kam, amma dai kinsan kinyi ganganci ko?

Maman khadija tace wai ke zubaida bakida kunya ne, nafa haifeki amma kike faɗamun magana san ranki..

Zubaida tace toh ai wanda ya rike girma shi ake bawa girma kekuma kin yada girmanki nikuma na take shi, nazone namiki kashedi ƴarki ta koma ƙawance dani inko ba hakaba zakiyi nadaman rabuwar mu, kuma maganan auren me kudi kima dena mafarkinsa domin nima ina sansa kuma ke kinsan bantaba nema na rasa ba, dama nayi tinani zan iya barmata shi tinda ƙawata ce, to amma yanzu babu sauran mutunci matukar bataje tabani hakuri ba...

Kuma mahaifina yabani sako infaɗaiki, yace idanhar kika bari nayi kuka sanadiyyarki to kema zakiyi kukan dayafi nawa kuma sannan sirrin daya tayaki bunnewa shekarun baya zai toneshi kowama yasani.

Maman khadija tanajin haka gugan dake hanunta yafaɗi ƙasa tasa hanu biyu ta riƙe kanta sannan tace na shiga uku, dan Allah zubaida kiyi haƙuri kuma kibawa babanki haƙuri kice mishi na tuba, kuma maganan khadija abune ne sauƙi tana dawowa daga islamiya zataje har gida tabaki hakuri..
Hjijhk
Zubaida ta kwashe da dariyar mugunta sannan tace to shikkenan, wato har islamiya ma takoma hmm lalle to ai se'ayi mugani in tusa zata hura wuta...

Maman khadija tace ki gaida gida Kinji. Zubaida ta juya cikin ɗagawa da isa tace gida yaji

Bayan tafiyar zubaida sai maman khadija tasmau guri tazauna hankalinta duk ya tashi, cikin takaici tace nashiga uku, yanzu abinda mutumin nan zai mun kenan, shekara da shekaru ina zaune akan sirrina amman zai tonemun, gaskiya bazantaba bari hakan yafaruba.

Bayan komawar zubaida gida bata tsaya ko inaba se gurin Babanta, aiko tasamashe zauna akan taburma aɓangarensa yanajin redio.

Zubaida tana isa gurunsa tasa dariya sannan tace baba kaga yanda fuskanta ya canza kuwa dana fadamata wannan maganar, tindaga gidan nake tinanin wani irin sirrine wannan mai girma haka. haƙurifa tarinka bani kuma harda cewa zata turo khadijan dakanta tazo tabamu haƙuri..

Babanta ya ɗago kai yace hmm nasani ai, barmaganan idan lokaci yayi zaki sani, yanzu abinda nakeso dake shine kiyi amfanida ƙawancenku da ita Khadijan da wasu dabaru ki kƙwace soyayyar dan sudan dinnan dan dake yafi dacewa

Zubaida tace ai karkaji komai baba sekace baniba, shiyasa nakeso tadawo kusa dani tayadda zan rika samun bayanai akanshi

Baban zubaida yace yauwa 'yar gari shiyasa nake sanki, haihuwar mace mai kyau jarin talaka.  yanzu babu ɗan wani abune agunki, kinsanfa garin sai a hankali

Zubaida tace gashi akwai dubu goma jiya Ahmad yaban, ammafa rabawa zamuyi. Baban zubaida yace kinga kawo dubu takwas ki ɗauki biyu kinsanfa cefane zanyi kuma dake za'aci abincin

Zubaida tace to shikkenan baba, kasan idan Ahmad yace mu hadu cemasa nake kasamin ido shiyasa bana fita amma ai da kuɗin zasufi haka

Baban zubaida yanaajin haka ya zabura ya zauna yace ammade anyi mashirmaciya, keda duk haɗuwanku dashi alkhairi ne kuma zakina mana baƙin ciki, toh nan gaba ko sau biyu yace zaizo kicemasa injini na'amince

Zubaida taɗanyi burus sanna tace to amma baba nifa yanzu bana sanshi dan sudan nakeso

Baban Zubaida yace na fahimceki, shiyasa nakeso kigama tatsan rabonki kafin ki sallameshi

Zubaida tace toh shikkenan baba nagane..

Suna cikin magana setaji inna tana kira tanacewa zubaida wai banace miki kidaura girki bane tindazu, ina kika shiga haka?

Zubaida tayi sauri ta ɓoye kudin tace mama naje karban takardane gidansu khadija dannayi karatu kinsan zamu fara jarrabawar karshe a makaranta, ina shigowa kuma baba yakirani..

Baban zubaida yace hakane nakirata dan namata nasiha akan tayi karatu kuma tayi jarabawa da kyau

Inna tace hmm da ace bansanka bane, karatun yarinyar nan sam bedamekaba, kai dai kawai mai zaka samu ta hanyarta

Baban Zubaida yace haba kekuwa karkice haka mana, ai wannan saninda kikaimun yanzu na canza..

Inna tace Allah yasa, amma de banga alamaba, zubaida kibar girkin zanyi jeki kiyi karatunki abunki Allah yamiki albarka

Zubaida taɗanyi murmushi sannan tace to amin inna

bayan shigar zubaida ɗaki sai inna tacewa baban Zubaida gaskiya kaji tsoran Allah akan tarbiyan yarinyar nan, kasani ƴaƴa amanace agaremu dolene mukula da tarbiyyan su amma na kula kai sam babu ruwanka, kome zaka gani agunta bazakai bincike inda tasamuba, haka kwanaki naga waya agunta amma kacemin wai anbakane se kabata, kuma ninasan bahaka bane, gaskiya ka canza halinka ka kulada amanar Allah a hannunka

Baban Zubaida yace toh kingama? Inkuma akwai saura se in dauko miki turmi ki zauna...

Harzakice naji tsoran Allah to da tsoran ki zanji, kuma ni dai bazan dai na gayamiki gaskiya ba kullum kika tashi magana sai kita fadamun abunda kikaga dama karkimanta aljannarki tana ƙasan ƙafata inko nagadama taketa zanyi sai inga ta inda zaki shiga, haka kawai kiyitamin fada sai kace danki na fari

Inna tace dolene nafaɗamaka gaskiya amma shikkenan kayi hakuri, Allah yana tareda me gaskiya

Baban Zubaida yace kuma nine me gaskiyan...

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now