Page 4

56 4 0
                                    

(Gidansu Zubaida)

"hello, Ahmad" Zubaida ta faɗa bayan ɗaga wayar ɗaya daga cikin samarinta. "Sai yau ka tuna dani?"

Ahmad yayi murmushi sannan yace "wanda aka manta shi ake tunawa, ke kuwa ban manta da ke ba ballantana in tuno ki; Kawai dai yanayin aiki ne sai ahankali shiyasa ki ka ji ni shiru.

Zubaida ta ɗan juya idanu sannan tace masa "kullum dai haka ka ke faɗa amma sai a jika shuru kamar an aiki bawa garinsu, kasanfa daga cikin farillan soyayya akwai kulawa da kuma damuwa da juna."

Ahmad yace "gaskiya ne Zuby na, ke ko dai iya hausa kamar jakar kano"

"Yanzu wannan zagi ne ko yabo?" Zubaida ta faɗa.

Ahmad yaɗan gyara zama yace "yabo kai, ke kin fi karfin a zageki ai.
Kinga mubar maganan wasa meye labiri ne, yaushe zamu hadu?

Zubaida tace "gaskiya bansan yaushe zan fito ba dan jiya ma na fita kuma cikin kwanakin nan Baba ya samun ido wai anata kawo ƙarata na cika yawo kasan mutane sun iya gulma"

Ahmad yace "to gaskiya tsaraba na kawo miki amma tunda ba za ki samu fitowa ba, ya zama ba rabonki ba kenan dan jibi zan koma wajen aiki"

Cikin hanzari zubaida tace "kamar ya ba rabona ba! kaima Ka san ai bazai wuceni ba mu hadu a inda muka saba haɗuwa gobe da yamma"

"Yauwa 'ƴar gari, yanzu naji magana, wata wayace nagani zata dace dake na siya miki da wata doguwar riga mai bala'in kyau"

"shiyasa na ke ji da kai nawan, sai mun hadu, barin fara tunanin yanda zan ninke Inna kasanta da sauƙin kai"

"Lalle Zuby ke wato abunnaki harda mamarki ko? Ahmad ya faɗa.

Zubaida tace "manta kawai, sai goben, saura kuma ka ɗebo jamfa nasanka da san dogin kaya"

Ahmad yace "gimbiya kenan, to ai jamfa yanamun kyau, toh amma tunda ba ƙya so shikkenan bazan saka ba"

Zubaida tace "ya dai fi kam, sai anjima barin samu Inna a waje"

bayan ta katse wayar sai ta fito tsakar gida gurin Inna tace mata "Inna sannu da aiki, ai da kinbari nayi"

Inna tace mata "ke da ki ka ce za ki yi karatu, jeki abunki ba komai, ai karatunnaki yafimin komai.
Wato Zubaida karatu a wannan zamanin ba abun wasa bane, shiyasa a shirye nake ko nawa zan kashe in dai ina da shi akan iliminki kinga babanku baida hali ɗan jarinnashi ma ya karye dan sana'an ƙosan nan dashi muka dogara, dan Allah Zubaida ki yi karatu ki sharemun hawaye na kin gade ku takwas na haifa amma yanzu daga ke sai ƙaninki Abdul da ku zanyi alfahari gaba, kuma abunda nake so dake kada duniya ta ruɗeki, ki yi hakuri akan abunda bakida shi; ki godewa Allah daya baki lafiya kuma ya ba ki iyaye biyu dan su sharemiki hawaye buri na ki yi karatu ki yi aure nima naga jikokina"

Zubaida ta ɗan gintse ido tayiwa Inna kallon jeka na yi ka alamar dai abunda Inna ta faɗa bai samu gurbin zama a zuciyarta ba.

"Inna kenan bakya gajiya da wannan maganar, in sha Allah bazan baki kunyaba. Inna akwai takarda da zan karɓo daga gidan su Khadija gobe daga makaranta zan wuce gidansu in kin bani izini"

Inna tace "toh ba komai, babanki ma yaje kauye sai gobe ko jibi zai dawo, yaje maganan gonansu na gado kinsan ance fatara mai tada tsohon bashi"

Zubaida tana dariya tace "kai babama dai yanzu dan Allah mai zai samu a wannan gonar, toh Allah ya dawo dashi lafiya"

Inna dai kanta ƙasa tana aikinta tace "amin"

Bayan Zubaida ta koma ɗakinta sai ta sake ɗaukan waya ta kira ƙawarta khadija, har sau biyu tana kira bata ɗagaa ba sai a na ukun taɗaga, "wai ina kika shiga ne?" Cikin gajan hakuri Zubaida ta tambayi khadija.

khadija tace "hmm ina can inata wanki, yau sani akai agaba da fada wai na fiye ƙazanta ni kuma kin san na tsani wanki gaskiya shine mama ta kwace wayan wai sai na gama tabani"

Zubaida tace "kekam ai kin saba daman ga san wanka ga kazantar tara wanki, angirama ba'asan angirmaba"

Khadija tadan haɗa rai tace "kinga yaufa nima a sama nake jina kina mun zan tanka miki, gara kibini ahankali"

Zubaida tace "ke ba wannan bama dan Allah ki gogemun kaya seti daya mai kyau acikin naki, zamu haɗu da Ahmad kinsan bansan raini so nake ya ganni a haɗe daga sama har kasa"

Khadija tadan juya baki sannan tace mata "tabɗi lalle ma, sai dai in kin zo ki goge da hanunki; wankinma da yaya na yi shi gaskiya bazan iya miki guga dan ki yi wa wani ƙato kwalliya ba"

Zubaida tace "shikkenan naji ke dama ba'a abun arziki dake"

Khadija tace "auu hakama zaki ce? sai na fasa baki aron kayan naga ya zakiyi"

"Kiyi hakuri ƙawata kema kinsan ba'ajin kanmu, sai mun haɗu goben kawai"

Khady tadanyi murmushi sannan tace "shikkenan, sai mun haɗu ki gaida inna"

Zubaida tace "to inna zataji"

Bayan tayanke wayan sai take magana da kanta kamar haka... "toh an kauda wannan matsalar barin kira khalifa ya turomin kati a waya, gida biyu maganin gobara".

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now