Page 13

17 2 0
                                    

Misalin ƙarfe takwas da rabi kenan bayan sun kammala cin abincin dare, sai mahaifiyar salma tabata izinin yin magana akan matsan dakeso su tattauna akai. Salma ta mce mama daman...
Kafin tace komai sai afra tace barin baku guri..
Sai salma tace ƙanwata base kintashi, sai salma tadubi mamanta tace mama daman khadija ce take so tayi ƙawance dani shine nake neman izininki idan kin yarda tazama kawata?

Maman salma taɗanyi murmushi sannan tace gaskiya naji daɗi sosai dakika tambayeni, shiyasa takiraki awayana ɗazu kenan? Sai salma tace eh mama shine dalilin kiran kuma gaskiya nafahimci tana cikin damuwa. Sai hajiya bilkisu tace mesa takesan yin kawance dake bayan a iya sanina kince kawar zubaida ce kuma ita Zubaidan batada tarbiyyan ƙwarai?

Salma tace mama tun farko daman zubaida ce takejan khadija ajiki, amma yanzu khaidijan tace bazata iya ko wani irin alaƙa da ita ba, shiyasa takeson nida safiya muzama kawayenta dan tasan halinmu na kirki ne

Maman salma tace ok, amma ke mai kike ganin yadace,(do you like her as a friend?) salma tace eh mama inasanta a matsayin ƙawa. Hajiya bilkisu tace mesa?

Salma taɗan numfasa sannan tace mama khadija tana cikin damuwa tana buƙatan rarrashi, sannan ajata ajiki, kuma idan har muka juya mata baya zata iya komawa gurin zubaida wanda hakan hatsarine ga rayuwatta... Inaso na amince da ita a matsayin kawa kuma na tai maketa dan tafita daga halin data tsinci kanta aciki

Maman salma tace masha Allah, lalle salma angirma sannan ta juya takalli afra tace autan mama mena faɗamuku gameda ƙawance?

Afra tace kince ƙawa tamkar ɓarin jikine ga mutum tana tasiri adukkan wani gaɓa na rayuwarmu dan haka muzaɓi wacce zata temakamana adukkan lamuran mu sannan ƙawancen da akayi shi dan Allah shine ƙawancen da baza'ayi dana sanin haɗashiba, sannan kince ba duk wancce muka haɗa aji ɗaya da ita tazama ƙawarmuba, ma'ana aji ɗaya daban ƙawa daban, ana zaben ƙawa base on hali,nagarta,tarbiyya,addini dakuma good background....

Maman salma taɗan sunkuyar dakai ƙasa tace Allah nagode maka, sannan ta ɗago kanta tace Allah yamuku albarka yarana! Suka amsa da amin. Sannan yaƙarada cewa shikkenan salma zaki iya yin ƙawance da Khadijan  Allah ya muku albarka baki ɗaya. To amma abunda nakeso naja hankalinku akai shine kusani shawara amana ce duk wanda yanemi shawaranku to yabaku amanan sirrinsa, kukuma yazama wajibi kufadi gaskiya koda baza'a soba.

Salma da afra sukace toh mama munagodiya, kuma in sha Allah zamu amfani da duk abunda kikace. Hajiya bilkisu tace to nagode. Sannan afra tace mama yaushe baba zai dawo?

Maman salma tace se gobe in sha Allah... Afra da salma sukace Allah ya dawo dashi lafiya

Maman su tace amin. Bayan sun ɗanyi shiru sai hajiya bilkisu tace wato salma da afra bawai ina tsananta mukubane, abota dakuma ƙawance sunada matukar mahimmanci a rayuwar ɗan adam wanda hartakai ƙawa zata iya sa ƙawar ta a shirka ta hanyar tsafi da sauran su, ƙawa zata iya sa ƙawa ta bijirewa iyayenta, mijinta, al'adanta dakuma addinin ta, akwai mutane dayawa dasukayi nadamar kasancewa da gurbatattun ƙawaye ko abokai amma awani bangaren akwai mutane dayawa dasukayi alfahari da ƙawance ko abota. kenan abun ya danganta da wa kika zaɓa a matsayin ƙawarki, shiyasa ina mamakin masu neman best friends a social media kuma harsuna fadamusu sirrinsu dansu basu shawara...
Sannan ana iya rabuwa da ƙawa idan ta nemi tarabaki da hanyan neman yardan Allah

Salma da afra sukace gaskiya mungodewa Allah dayabamu uwa tagari, Alhamdulillah

Maman salma tace harkunsa natinada wata ƙawata damukai secondary  school tare, class dinmu ɗaya amma sam halinmu ba ɗayaba hasalima nayi ƙawance da ita dan nasamu daman canza ta amma sam hakan besamuba, sannan akantane na fahimci me ake nufi da ƙawance dakuma me ake nufi da sadaukarwa a soyayya!

Hajiya bilki batasan sanda hawaye yafito mata ba, se salma tace ina ma ace zaki bamu labarin t. Amma yanaga hawaye a idonki mama?

Mamansu salma tace ba komai,... Mubar maganan kawai, dare yayi kuje ku kwanta kuyi bacci sannan kada ku manta da alwala, adddu'a, dakum karanta suratul mulk

Suka amsa da toh mama, sai da safe

Maman salma tace Allah ya tashemu lafiya.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now