Page 8

32 5 0
                                    

(GIDANSU SALMA)

Misalin ƙarfe takwas na safe Salma ta gama shirya karin kumallo akan teburi, maman salma da baban salma su ka sauko ƙasa dan cin abinci; cikin ladabi Salma ta gaida iyayenta suka amsa cikin farin ciki.

Maman salma tace "masha Allah, ina autan nawa take?"

Salma tace "Afra tana ɗaki tana shiryawa, au gata can ma fitowa"

Bayan Afra ta iso kusa da iyayenta tamusu gaisuwa sannan suka zauna cin abinci cikin farin ciki da ƙaunar juna.

Baban Salma ya fahimci jikin salma haryanzu a sanyaye ya ke sai yace mata Salma ki saki jikinki mana, ai na hakura kinsan duk fushina baya wuce kwana ɗaya, kada ki manta wannan shine karo na farko da ki ka ɓatamin rai haka; ko dan haka na miki uzuri"

Salma tayi farin cikin jin haka daga mahaifinta, cikin murmushi tace "na gode baba, sannan taƙara da cewa"baba ina so in je sayayya anjima inka yadda"

"To ba komai, na yadda kuma zan bada kuɗi a mamanku in kunshirya sai ta baku" baban Salma ya faɗa.

Maman salma tace "idan ka amince zan raka su muje tare dan bana so suna fita su kaɗai sai driver"

Baban salma yace wai mai yasa ba kida yadda ne? Shekaru takwas kenan haladu yana aiki a gidanan amma baki yadda da shiba hajiya bilki?"

"ka yi hakuri ba haka nake nufiba kasan yaran yanzu da kuma yanda rayuwa ya canza dole mu sa ido mu kuka sosai"

Baban salma yace "toh shikkenan, amma dai Hajiya ku dawo da wuri dan tuwo nake san ci da rana inkuma Sabira zata yi toh shikkenan"

Maman salma tace "kaima dai Baban salma baka gajiya, ka san abincinka baya taba wuce hannuna"

Baban salma yaɗanyi dariya sannan yace "hakane na gode da kulawa ta musamman, afra my girl sai kun dawo ko; ki kula da kanki"

Afra tayi murmushi sannan tace "toh baba thank you"

Jim kaɗan misalin ƙarfe goma na safe Hajiya Bilkisu da yaranta suka shirya cikin shiga ta mutunci da kamala suka nufi inda zasu je."

Shigarsu shopping mall keda wuya su kai kiciɓus da Kamal da mamansa wato Hajiya Samira.

"Malama Bilkisu an jima ba'a haɗu ba, bayan haduwar 'ya 'yan mu kuma saai naji labari marar daɗi; Salma ashe kin yi girmanda za ki iya marin saurayi a tsakiyar taro?" Hajiya Samira ta faɗa.

Maman salma tace "Hajiya Samira kenan, ai ba Salma ba ce ta girma; Kamal ne ya girma tunda har ya iya kama hanun 'ya mace a tsakiyar taro.  kodayake ba laifinsa bane wataƙila tarbiyarda aka koya mishi kenan.
kai kuma Kamal kafi kowa sanin me ya faru kuma kasan ba laifin Salma bane toh amma ance durƙusawa wada ba gajiyawa bane dan haka duk muyi hakuri kuma a kiyayi gaba"

Kamal yaɗan sunkuyar da kansa ƙasa yace "na san laifi na ne kuma na yi nadama har cikin zuciyata dan haka Salma kiyi hakuri in sha Allah bazan ƙara yiwa 'ya mace haka ba, kin san ɗan Adam tara yake bai cika goma ba."

Hajiya Samira ranta ya ɓaci matuƙa tace "ashe abunda ka yi kenan Kamal?  haka na koya maka ka mu'amalanci mace!?"

Kamal yace "I'm sorry Mum na san ban kyauta ba."

Hajiya Samira ta juya ranta aɓace ta futa daga gurin shima Kamal ya bita yanata bata hakuri amma ko kulashi bata yi ba."

Bayan fitar Kamal da mamansa sai Salma "tace ina ma ace bamu futo sayayyar ba, na rasa me yasa maman Kamal take da faɗa sosai sannan bata ƙaunarki ko kaɗan Mama."

Hajiya Bilkisu tace "ya isa haka mu bar maganan, kuje ku ɗauki abunda ku ke so mu koma gida."

Bayan Kamal da mahaifiyarsa sun shiga mota sai yake lallashinta akan ta yi hakuri akan abunda ya faru, harma yake faɗim ai da ta yi hakuri sun gama sayayyan."

Me zan yi a gurinda Bilkisu take? wato ashe abunda kayi kenan shine kaƙi faɗamun gaskiya gashi kasa naji kunya agaban mutane."

Kamal yace "Mum ki bar maganan nan please nace kiyi hakuri sharrin shaiɗanne fa kuma kin san mu a can turai normal ne gaisawa da mata."

Rufemun baki, ka duba handbag ɗina ka bani magani na nasha, sannan kuma ka kaini gidan Hajiya Aisha."

Kamal yace Mum haryanzu baki bani amsar tambayata game da babanmu baba."

Maman Kamal tace "ka tambayi babanka sauran labarin. Sannan kuma ranar juma'a zaka raka ni gidansu Safiya amma tafiyar ba tawa bace, taka ce."

Kamal yace "kamar ya Mum, ni kuma?

"Ina so zan kai ka, ka gaisa da Safiya yarinyar tana da hankali sosai; zan yi magana da babanta tana gama secondary school a bani ita awajena kaga daga nan sai ku fahimci juna ayi tuwo na mai na."

Kamal ya dubi mamansa da sauri yace "amma Mum bance ina santa ba ai kuma yanzu an daina auren haɗi irin wannan kuma fa ƙawar Salma ce."

"To sai meye dan ƙawar Salma ce?  ko dai akwai wani abu ne tsakanin ka da Salma?

Kamal yayi maza yace "no, ba komai Mum, but i need some time to think about it please."

Maman Kamal tace "ba komai, zan baka lokaci kayi tunanin; amma fa bazan canja ra'ayi na ba."

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now