Page 30

67 4 3
                                    

"Bin dokar Allah ba ƙauyanci bane" na fatima saje ummu amna.

Alhamdulillah aure ya ɗauru tsakanin kamal sameer ahmad da amaren sa safiya abdullahi goni da salma abdulƙadir sulaiman a bisa sadaki dubu ɗari ɗari laqadan jama'a ku shaida Assalamu alaikum 💞💞💞

Alhamdulillah burin duk wani cikakken ɗan adam aure, muradin duk wasu masoya aure, alfaharin duk wasu iyaye aure, farin cikin dangi aure, ƙasaitar basarake aure, rabin addini mutum shine aure. Tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da duk abunda ke tsakani, mai duka mai komai ilahu, mai kowa mai komai maliku... "Wa ila hukum ilahuuwahid laaa ila ha illahuwar-rahmanur raheem".

Masha Allah aure ya ɗauru haƙiƙa zuƙata suna cikin farin cikin cikar burinsu. Misalin ƙarfe biyar na yamma bayan ribibin mutane ya tsagaita sai mahaifin safiya ya kirata a ɗakin sa, bayan safiya ta shigo ta zauna kusa da shi sai yace safiya ban taɓa jin matsanancin kewar mahaifiyarki ba irin yau kuma kema nasan kukan da kijeyi kenan amma ba komai in sha Allahu mamarki tana cikin aminci da rahamar Allah abun da ya rage muyita mata addu'a. Wato safiya tin da nake da mamanki bamu taɓa fishi da juna ba duk abunda ya faru mukan tattauna sai kowa ya fahimci ɗan uwansa shiyasa nakeso na miki wasici da kibar ƙofar tattaunawa a buɗe tsakanin ki da mijinki domin hakan shi zai kawo ƙarshen duk wata matsala a tsakanin ku. Sannan ita kuma salma dama can aminiyarki ce to yanzu ta ƙara samun matsayin zama abokiyar rayuwa ki na zaman aure dan haka ku haɗa kanku ku samar da farin ciki da nitsuwa ga mijinku. Cikin sheshsheƙar kuka tace to baba. Sannan yakara da cewa nasan abubuwa dayawa sun faru a zamanmu tare da ke a gidan nan amma duk da haka kika dawo gida dan ayi bikinki a nan wannan yaƙara nunamun tabbacin hankalinki safiya kuma nagodewa Allah da ya bani ke. Safiya tace ai baba banida inda yafi wannan gidan a duniya kowace mace tana alfahari da gidan mahaifin ta sannan kamar kowacce 'ya nima zanso na kasance tare da mahaifina a yau, nagode da dukkan kulawarka, tarbiyyan ka dakuma ƙaunarka a gare ni baba😭.
Haka ya dafa kan 'yarsa yana cewa kukan ya isa haka yau ranar farin ciki ne 'yata.

(Gidansu salma)
.....Salma ashe nan kika zo ina ta neman ki tin ɗazu" muryar maman 'yan biyu kenan da salma tajiyo a bayanta. Da gudu tazo ta rungune ta tana kuka tace ina ma ace mama tana nan😭.... Taake hawaye suka fara zuba daga idanun maman 'yan biyu cikin kwarin guiwa da sanyi murya tace wa salma haƙiƙa kina da 'yancin yin kuka a yau kuma bazan hanaki ba to amma shin kukan shine abunda hajiya bilkisu take buƙata? Salma tace a'a bashi bane maman 'yan biyu tace to ki share hawayenki kuma kiyi hakuri sannan kiyiwa mama addu'a Allah yasa ta huta salma tace amin nagode maman 'yan biyu. Ina afrah? Cewar salma" maman 'yan biyu tace afrah, khadija da baba hindatu da anty zara duk sun tafi gidanki sunje su ɗanyi goge goge kuma su sa tiraren wuta sannan su jira zuwanki, itama safiya wasu daga cikin danginta sunje dan haka ki kwantar da hankalinki kin kusa zuwa wajen masoyinki kuma mijinki salma tace kema tsokanata zakiyi maman 'yan biyu? Ba tsokana bace ina tayaki murna ne 'yata. Baban ki yana san ganinki a parlour yanzu dan haka kiyi maza kije ki sameshi, salma tace dan Allah ki rakani ji nake bazan iya zuwa ni kaɗai ba. Maman 'yan biyu tace to shikkenan muje...
Bayan sun shiga sai maman 'yan biyu ta zaunar da amarya ita kuma ta koma cikin gida wajen sauran baƙi. Alhamdulillah itace kalmar farko daya fito daga bakin mahaifin salma, bayan doguwar addu'a da nuna matuƙar godiya ga Allah jalla wa ala sai ya ƙara da cewa salma ina so zan miki wata tambaya guda ɗaya...
Jin haka yasa salma ta shiga tinanin wace tambaya ce wannan haka amma sai ta katse kanta daga tinanin tace to baba. Alhaji abdulkadir yaɗan gyara zama sannan yace salma mene aure?

Tayi kamar daƙiƙa biyar batace komai ba sai daga bisani tace baba aure kamar da'ira ce da ta ƙunshi zaɓin mutum kuma take juyawa bisa addu'a da kuma ƙaddarawar ubangiji wacce ta ƙunshi kusurwar misalai kuda huɗu na siffofin auratayya dakuma ma'aurata... To fah wannan amsar da salma ta bawa mahaifin ta shi kansa sai da ya ƙara gyara zama domin bai fahimci abun da take nufi ba. Shin zaki iya yimun fashin baƙi akan abunda kika faɗa? Inji mahaifin salma " salma tace eh baba, sannan taƙara da cewa..
... da'ira yana nufin auren kansa, kusurwa guda huɗu suna nufin halin rayuwar aure na farko shine misalin auren da ya ƙunshi soyayya, fahimta, tausayi dakuma neman ilimi da aiki dashi wanda hakan shi zai bawa ma'aurata damar sauke hakkokin da yake kansu...
Kusurwa ta biyu shine misalin auren da ya ƙunshi soyayya, dogun buri ko kwaɗayi da kuma san zuciya...
Kusurwa ta uku shine misalin auren da ya ƙunshi ƙiyayya, hassada, jahilci da cin amana...
Kusurwa ta huɗu shine misalin auren da ya ƙunshi ƙiyayya, fahimta, sadaukarwa, tausayi da yiwa juna adalci..
Duka wannan akwai zaɓin mutum sannan akwai kaddara to amma kamar yadda nace da'ira ce tana juyawa bisa ƙarfin addu'a dakuma ƙaddara a karo na biyu. Wannan yasa aure ya keda zaɓin ɗan adam dakuma abunda Allah ya rubuta masa "li kulli ajalin kitab"
Dogun numfashi tare da ajiyan zuci mahaifin salma yaja sannan yace "you are indeed bilki's daughter " Allah ya miki albarka salma jeki ki shirya bayan sallar isha'i zan ɗaukeki muje gidan su safiya mu ɗauketa da mahaifinta mu kaiku gidan ku.

Hakan ko akayi salma da babanta, safiya ma da babanta kowacce aka kaita ɓangaren ta akai musu nasiha aka ɗebo sauran dangi kowa ya dawo gida shima ango aka rakashi gurin matansa.

***()**() ***() ***.

Alhamdulillah laifin daɗi ƙarewa anan nakawo ƙarshen wannan labari mai suna"Bin dokar Allah ba ƙauyanci bane" amma akwai cigabansa mai suna...

"INGANTACCEN KISHI" zai zo muku bada jimawa ba in sha Allah.

Godiya ta musamman ga masu bibiyan rubutuna ina fata ya amfane mu baki ɗaya. Amin.

.... Comment ɗinku nada matukar mahimmanci a gare ni, kuma zai bani kwarin guiwa aduk lokacinda zan yi rubutu.

Ga masu sha'awar taimakamun ga account details dina 0091869462 fatima Abubakar saje access bank.

Na gode😊💞
Fatima Abubakar Saje (ummuadam wa amna).

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now