Page 14

17 2 0
                                    

Bayan shigowa alhaji sameer gida wato mahaifin kamal kenan kai tsaye ya wuce ɓangarensa ya shiga ɗaki yazauna kasancewar yasan matarsa na bacci kamar yadda tasanaddaahi a waya kafin yaƙaraso, hakan yasa beje gurintaba ya wuce ɓanagarensa. Bayan kimanin mintina talatin se kamal ya taso yazo gurin mahaifinsa kamar yadda saƙo ya isa gareshi cewar babansa yanasan yi magana dashi. Kamal yana isowa bakin ƙofa yayiwa mahaifinsa sallama sannan yanemi izinin shiga gurinsa..

Baban kamal yace wa alaikumus-salam, shigo ka zauna, bayan kamal yazauna seya ɗora da gaisuwa cikin ladabi, sannan yace mum tace kana san ganina

Baban kamal yace akwai islamiya da'aka buɗe na manya a unguwar filin jirgi,so nayi mana registration zamu fara zuwa next week weekend in sha Allah, sannan akwai karatun hadith da'akeyi a masallacin kofar gidan baba dafa duk ranan Monday tsakanin magriba da isha zamu fara zuwa tareda kai idan Allah ya yarda.

Kamal yace amma dady da girmana zaka sani islamiya sekace wani yaro

Baban kamal ya ɗaga kai ya kalleshi sannan yace tsakanin ni da kai waya haifi wani?

Kamal yace kaine dady, kai ka haifeni

Baban kamal yace to nima nashiga islamiyan balle kai, har nawa kake dakake ganin ka girma lokacinda musulunci ya zo ba ƙananan yara aka barwa suyiba, hasalima annabi da sahabban sa irinsu sayyidina abubakar da umar sa'annine kuma sunkai shekara arba'in in akwai abinda ya daura ko ya rage kadan ne tsakaninsu, a lokacin basuce sun girma ba sahabbai sunyi haddar Alqur'ani sun rawaito hadithai sunyi jihadi, sunyi hijira, sun yaɗa adddinin Allah ko ina a faɗin duniya kuma cikinsu akwai tsofi, matasa, dakuma masu tasowa

Kamal yace to ai dad sahabbai fa kace su ai daban suke

Baban kamal yace hakane daban suke kuma bazamu iya zama ɗaya dasuba har abada domin su na musamman ne, amma kuma kamal abunda zaka duba shine sahabbai suma mutane ne kamarmu suna da buƙatu irinnamu, sunada iyalai, sunada sana'a, suna noma suna kiwo, suna kasuwanci, amma kasan mesaa suka zama daban?
Kamal yace a'a
Se baban kamal yace saboda musulunci da zuciyar su sukeyi bada fatan bakinsuba. karfin niyyarsu Allah yagani ya sauƙaƙa musu dukkan lamarinsu kuma yamusu albarka acikin lokacinsu, mutanene jajirtattu a kowani fanni na rayuwa, duniya a tafin hannun su take ba'a zuciyarsuba shiyasa ko kadan basa ganin duniya wani abu bare har ƙele-ƙelen ciki ya ruɗesu, mutanene masu gaskiya da amana, masu tsoron Allah, kamal sahabbai sun wuce duk inda muke tsammani, idan akai maganar so tsakaninsu da manzon rahama(S.A.W) kuwa sune sukai masa ƙololuwar so wanda inda za'a hada dukkanin son da muke masa na mutanen duniya yanzu bazamu kama kafarsuba, Allah yakara musu daraja, yadda, da rahama, ya hadamu dasu a gidan aljananah gabadaya badan munkaiba sedan rahamarsa, tausayinsa da jin ƙansa ga bayinsa.

Kamal yace amin dady

Baban kamal ya kukada yanda kamal ya maida hankali wajen sauraron sa seya ƙara dacewa wato kamal abinda nakeson ka gane shine duk abinda zanmaka is for your own good, duk mutumin da ya nemi ilimi, kuma yayi aiki dashi bisa koyarwan Alqur'ani da sunnah, kuma yayi shi da ikhlasi ma'ana dan neman yardan Allah toh tabbas yayi sa'a kuma ya dace kuma ya kyuatawa kansa, domin duk wanda kaga yana kokarin gyaran lahirar sa kansa yakeyiwa babu abinda zai ƙari Allah koya ragi Allah dashi, shiyasa duk wanda yakeyin aiki dan wani ko wata ko wasu to hakika yazama abin tausayi tamkar gini ne da ake yinshi da tubalin toka...

Kamal yace toh dady, nagode sosai da wannan nasiha Allah yasaka da alheri

Baban kamal ya amsa da amin, sannan yace ga takaddun ka nan seka fara dubawa kafin ranan dazamu fara fita makaranta.

Kamal yasa hanu biyu yakarɓa yace nagode dady. harya yunƙura zai tashi seya koma ya zauna sannan yace dady inaso muɗanyi wata magana in bazaka damuba?

Baban kamal yace to inajinka

Kamal yaɗan numfasa sannan yace  mesa kuke yawan samun matsala da mum kode ba auren soyayya kukai bane dady?

Bayan alhaji sameer ya ja dogon numfashi sai ya kalli kamal yace yaro de yaro ne yanzu kamal a tinaninka ana samun matsala a zaman aurene kawai idan anyishi babu soyayya ko?

Kamal yace eh haka nake gani dady, sabida idan har akwai so mezai kawo matsala kuma?

Baban kamal yace rashin fahimtar juna, duk yanda ma'aurata suke son junansu idan basu fahimci yaran junaba ta bangaren soyayya, zamantakewa, shawarwari, da sauransu to tabbas zasuna samun matsala especially idan akwai rashin yadda a tsakaninsu. wato kamal soyayya a zaman aure jigo ne amma fahimtar juna shine tushe....

Kamal yaɗanyi zugum sannan yace baba mene ne jego da tushe kuma?

Baban kamal yaɗanyi dariya sannan yace ba jego ake cewaba jigo, zaman waje ya ɓata maka harshe ko? idan akace jigo kamar jagora kenan wanda idan ba shi toh zaman aure bazaiyi daɗi ba, za'a rayu tamkar rayuwa cikin sarƙa daneman ƴanci a kowani lokaci..
Idan akace tushe kuma shine abunda idan babu shi to zaman auran ma gabadaya bazaiyi yanda ake soba... may be bazaka fahimtaba yanzu amma with time zaka fahimci menake nufi.

Kamal yace kenan dady ba rahin soyayyah bane yakesa saɓani tsakaninka da mum rashin fahimtane?

Baban kamal yace kwarai kuwa, your mother is my first and true love kamal...
Sannan se baban kamal yace kode kafara soyayya ne?

Kamal yaɗan sunkuyar da kansa ƙasa alamar kunya sannan yace a'a, ai tukun da saurana ko dady?

Baban kamal ya amsa dacewa gaskiya kam, seka kara hankali tukun.
zaka iya tafiya idan tambayan sun ƙare

Kamal yace sun ƙare dady, bye dad
Baban kamal yace ok son

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now