Page 28

31 3 0
                                    

Da gudu kamal yaje ya rungume iyayensa sannan yamusu godiya akan wannan babban albishir dasuka masa, farin ciki, annashuwa marar misaltuwa da jin daɗi sun bayyana ƙarara a fuskarsa dakuma kalamansa. Hajiya samira tace to yanzude mungama namu finally you are getting married to salma in sha Allah! Baban kamal yace Allah ya muku albarka nizanje gidan hajiya aisha yanzu idan akwai wani abu semuyi waya. Hajiya samira tace to shikkenan Allah ya kaika lafiya kuma inkaje kace ina gaidata sosai kuma inda hali akawomin munir muyi weekend tare. Baban kamal yace to ranki ya daɗe, hajiya samira taɗan kau da ido tace agaban yaran, yaɗanyi murmushi sannan yace ai koyamasa nakeyi sai duk sukai dariya sannan suka tafi.
Cikin farin ciki kamal ya juyo yacewa safiyya kinga wani ikon Allah abun kamar a mafarki Alhamdulillah, safiya taɗan gyaɗa kai sannan yace kwarai naga abun mamaki kuma na maka murna Allah yasanya alkhairi. Kamal yace meya faru safiyya, yanaga kamar bakya farin ciki?
Safiya tace haba yaya kamal ko kara babu agabana kake irin wannan murnan dan kawai anmaka albishir na auren salma sai kace niba aurena zakayi ba, Ana yiwa mace kishiyane bayan aurenta amma ni zakai min kishiyane ranan aurena and you are expecting me to be happy? Kamal yace but tarefa muketa faɗi tashi akan aurena da salma kuma... Kafin yaƙarasa magana safiya tace yaya kamal saboda ina sanka shiyasa nayi supporting ɗinka badan inaso naganka tareda wata mace ba...

Kamal fa ya fahimci kishin safiya ya motsa sosai dan haka yaɗanyi shiru sannan ya numfasa kuma ya haɗiye murnadda yakeyi, cikin sanyin murya yace haba safiyya ba haka nake nufiba kema ina farin ciki da aurenki kawaide wannan ɗin yazomun abazata ne shiyasa amma ai kece uwar gidana in sha Allah. Safiya ta juyo tace "au" harna koma uwargidanka ma kenan, tin wata biyu dasuka wuce kake kirana amarya to be amma yanzu harna tsufa nakoma uwar gida in just a moment?

Kamal fa yafara rikicewa ganin yanda safiya ta rikiɗe lokaci ɗaya kamar ba itaba, yace safiyya kiyi haƙuri dan Allah ba haka nake nufiba. Safiya ta juya tace nizan shiga ciki sai da safe.

Safiya na tafiya kamal ya cire hula yafara fifita yana mai-maita inna lillahi wa inna ilai raji'un, sannan daga bisani yace kai gaskiya mata ba'a iya muku jiya take goyon bayana danna samu salma, yau nasamu kuma ta juyamun baya. Its impossible to understand a woman's mind🙄

shigar safiya ɗaki keda wuya sai taji wayarta na ƙara, tana ɗagawa sai taga salma ce. Bayan taɗaga wayar sai salma tacemata ƙawata yau ina cikin farin ciki wanda nikaina bansan iyakarsaba kuma nasan kinsan dalilin hakan. Safiya tace tayaya zan sani bayan baki faɗamunba! Salma tayi murmushi sannan tace "hm" safiya kenan kinmanta randa kikamin albishir nasa ranar aurenki da kamal?
Tonima yau irin abunda zanfaɗamiki kenan, kinata cikamin baki sewani rawar kai kikeyi zaki auri yaya kamal segashi yanzu labari ya canza yanzu na tabbata bakida abun faɗa😶

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace salma kenan, nide abunda nasani shine wannan ranar dakika faɗa ranace da akasa domin ɗaurin aurena dan haka haryanzu abayana kike, kuma sannan bakin safiya baya rasa abunfaɗa sai dai inbataso magaba. Haƙiƙa yaya kamal yayi murna da farincikin jin labarin aurenki hasalima ganin yadda yake farin cikin yasa banbar inda yakeba harsaida najawo hankalinsa gareni cikin ƙanƙanin lokaci, dan haka ayanzu nasan yaya kamal bawai tinaninki yakeba hasalima ƙoƙari yake yashawo kaina. Rufe bakin safiya keda wuya sai taji ƙarar text massage yashigo wayarta, tana dubawa taga saƙon kamal ne me ɗauke da rarrashi dakuma soyayya😍.
Farin ciki ya lulluɓeta sannan tacewa salma kinga ɗan halak ana maganarsa sai ga ahi, yanzu haka saƙon kamal ne yashigo wayata kinga kenan hasashena yazama gaskiya. Salma tace sai anjima kawai..
Ko jiran amsar safiya batayiba takatse wayar, bayan salma ta ajiye waya sai take magana dakanta takecewa gaskiya safiya senayi dagaske kafun na iya cin nasara afikin yaƙin nan, amma koba komai ina alfahari dake ƙawata wataƙila da badan ke ba da haryanzu ban amince da soyayyar kamal ba👥

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now