Page 19

20 3 0
                                    

Safiya na zaune a aji sai salma tashigo tace mata safiya ya akai kika zauna a class kowa na waje ana shan iska? Sai safiya tace salma yanzu dan Allah abinda hanifa da salifa sukai yayi daidai, wai ace su fidda anko har anfara siya amma basu faɗa manaba?

Salma tanami guri tazauna sannan tace gaskiya koni banji daɗi ba, amma mai zai hana in sundawo mutambayesu dalilin dayasa sukai hakan, dan karmu yanke musu hukunci batareda munji daga bakinsuba..

Safiya taɗan numfasa sannan tace hakane kam malama salma, shikkenan bari sudawo muji. Sai salma tace kema yau tsokanata zakiyi ko?

Safiya tace a'a ba tsokana bane gaskiyane malamar ce dagaske. Salma tace ɗaliba de bankai malamaba tukun

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace toh shikkenan na bar miki, yauwa gasunan shigowa. Bayan salifa da hanifa sun ahigo harma sun zauna sai safiya tace munji anfidda anko kuma harkun fara siya amma baku faɗamanaba shin meye dalilin ku nayin hakan?

Salifa tace hmm kunfi kowa sani ai, last two weeks fah da'akai maganan anko cewa kukai ayi hijabi maroon color har ƙasa, sai kace matan limamai ko wanda zamuje gaisuwan mutuwa

Hanifa taɗan juya ido tacewa salifa ke harma kin kulasu, tinda bazaku waye kushigo gariba seku koma gefe kusha kallo dan ku biyar ne bakwa cikin ankon dake safiya, salma, zara, habiba, da ilham

Safiya tace lalle ma hanifa da salima wato waremu kukai ashe abunnaku har yakai haka?

Salma taɗan riƙe hanun safiya tace shikkenan safiya ƙyalesu kawai tinda munkai biyar ai sai muyi namu kawai, ammade salifa kunsan sa polo da skirt da ɗan ƙaramin gyale ba mutuncin ƴa mace bane, musamman ma dayake akwai ɗaukan hotuna kuma za'a yaɗa social media kowa yagani. ashawarce bekamata kuyi hakanba.

Hanifa tace salma wai ke bakya gajiya ne dan Allah, haba wa'azinnan tin shigarmu SS1 kikeyi gashi harmuna shirin gamawa amma bazaki denaba, ai yakamata kibari haka for god sake kibari bama san ji

Salifa takalli salma da safiya tace ai sekuyitayi..
Sannan tajuya gurin ƙawarta tace kinga hanifa nayi magana dame lalle tace zata mana dan haka zo muje mufaɗawa sauran semu haɗa kudin guri guda inmunje mubata a dunƙule, sai hanifa tace to kitsofa kinsan fa ni sai nayi ƙari dan gaban goshin duk ya cinye..

Hanifa taɗanyi dariya sanna tace nima ai zanyi dan bazaki barni abaya ba ƙawata

Safiya tace Allah ya shiryeku, yasa kugane gaskiya.
Salma tace amin. Bayan su banifa sunƙara ficewa daga ajin sai salma tace zan ɗauki nauyin siyamana hijaban guda biyar seki kifaɗawa sauran please karsu Saya

Safiya tayi murna ƙorai sannan tace masha Allah mungode Allah yaƙarawa mama da baba budi. Salma tace amin ƙawata.

safiya taɗanyi shiru naɗan lokaci sannan tace niko salma inaso muyi wata magana, se salma tace toh ina jinki safiya Allah yasa lafiya

Safiya tace lafiya lau. kinsan ina baki labarin yayar mamana wacce nake kira adda, salma tace eh nasanta mahaifiyar kamal ko? Sai safiya tace kwarai kuwa ai maganarma akan kamal ɗinne, sai salma tace to inajinki

Safiya tace dama addan ne takeso ta haɗani da yaya kamal aure inna gama secondary school kuma harma sunyi magana da babana kuma ya amince

maganar ya gir-giza zuciyar salma sosai dan seda kanta ya sara taji kamar an soketa a zuciya dakyar ta amsa tace mata kamal kuma?

Safiya taɗanyi murmushi sannan tace eh kamal, meya faru naga kin razana kuma kina zufa salma lafiya kuwa?

Salma taɗanyi ajiyan zuciya sannan ta numfasa daƙyar tace ba komai kawaide kainane yafara ciwo sosai shiyasa.. amma kuna san juna ne?

Safiya tace ayya sannu ƙawata.. Sannan taƙara dacewa bansan shi yaya kamal ɗinba amma nide ina sanshi duk dade banfaɗa mishiba dan yace mubari sai na gama school kafinnan munyi tinani akai. amma salma nide ina sanshi fiyeda yadda nayi tsammanin zanso wani mutum arayuwata, salma bansan daɗin uwaba kullum ji nake kamar ina kurkuku cikin sarka, banida buri daya wuce nasamu miji wanda zan soshi dan Allah na rayu dashi cikin farin ciki da ƙaunar juna, bansan ya akai ba kuma bansan yaushe nafara ba amma nayi nisa acikin kogin soyayyar kamal, jinake kamar bazan iya rayuwa ba shiba salma

Salma tace amma safiya anya bakiyi kuskuren faɗawa soyayya da Kamal ba tinda haryanzu bakisan ko yana sanki ba kobaya sanki?

Safiya tace salma kenan, inma kuskuren ne to sai dai akiyaye gaba amma yanzuka nayi nisa sosai, sai dai bazanga lefinkiba dan haryanzu so be miki ɗaurin mintiba, amma salma ai shi so dama ɗan kasada ne, sannna baya jiran umarni ko shawara kafin ya dasa kansa acikin zuciya musamman idan ya samu zuciya irin tawa wacce take tamkar sabuwar gona a lokacin damana

Salma tace subahanallahi! amma safiya ana iya cire so daga zuciya konace ana iya mantawa da wanda akeso?

Safiya taɗanyi murmushi tace ya danganta sabida ai so kamar shukane akwai wanda shuka shi da tuge shi yanada sauki, akwai kuma wanda shukar da sauki amma tuge shi ko kadan baida sauki musamman inya samu inda yakeso, sai kuma wanda shukashi da tugeshin duk ba sauki, amma dai based on experience gaskiya bazan iya mantawa da kamal ba, salma ayanzu banda wani sauran buri dayawuce naganshi cikin farin ciki, duk yanda nashiga damuwa ko tinani dana tina fuskarsa senaji hankalina ya kwanta

Salma tace safiya dama haka so yakene?

Safiya tace nima bansaniba salma ammade ni haka nakeji, musamman yanzu da adda tabani waya bansan sau nawa nake kallon hotonsaba arana, wani lokacin ko cikin dare nafarka senaji duk na kasa bacci, amma duk yanda nake sanshi bazan iya faɗamishiba dan haryanzu bamu gama school ba shikuma yafisan senagama sannan yaji amsar

Salma taɗan dafa kanta dake mata ciwo sannan tace ya isa haka safiya mubar maganan, I think banda lafiya inajin zuciyata tana bugawa sosai kuma daƙarfi kuma kaina yana ciwo jinke kamar zai faɗi

Cikin tashin hankali safiya ta kama salna tace subahanallah, sannu barin siyo miki magani karki kasa rubuta jarabawar yamma

Salma tace kikaini clinic kawai. Sai safiya tace to shikkenan muje.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now