Page 7

42 4 0
                                    

(Dawo war Khadija da Zubaida gida)
A hanyarsu ta zuwa gida suka samu saɓani saboda karɓan kuɗin Nuur da Zubaida ta yi ba tare da yardan Khadija ba.

Suna shigowa gida sai maman Khadija ta fahimci akwai matsala, sai tace "ya kun fita cikin farin ciki kuma kun dawo rai a ɓace kamar an muku mutuwa?"

Zubaida tace "mama wai dan an bamu kyautar kudi na karba shine take fushi dani wai na fiye san abun duniya kuma naga babu kyau maida hannun kyauta baya shi yasa na karɓa."

Maman khadija ta kalli "ƴarta tace "lalle ma Khadija wato duk huɗubar da na ke yi miki baya shiga kanki ko? a zamanin nan da muke ciki har za'a yi miki kyautar kuɗi ki ce bakya so, wai ke wace irin 'yar ƙauye ce?"

Mama na san dama laifi na za ki gani ba na Zubaida ba, ta yaya daga haɗuwan farko da saurayi zai bani dubu ɗari kuma in karba? Mama kin manta cin kuɗin saurayi bashi ne watara za'a biya?"

Maman Khadija ta kau da kai kamar bata ji abunda 'ƴarta take faɗamata ba, ta kalli Zubaida tace "dauko mata bulala ta zane ni kawai dan naga alamun na ɓata mata rai"

Khadija tace "haba mama, mai ya sa zaki ce haka? kada Allah ya nuna mun ranar da zan ɗaga murya ta a kan taki ballantana hannu na. Kawai dai ina ƙoƙarin fahimtar da ku ne duk budurwar da ta ɗauki dawainiyarta ta ɗaurawa saurayinta tamkar mijinta wata rana shima zai nai mi hakkinsa a wajenta kamar matarsa. Kullum ana faɗamana a islamiyya mu guji abun hanun maza dan mafi yawa ba alkhairi bane."

Maman khadija ta dubi zubaida tace "Allah ya miki albarka da ki ka karɓo kudin, miko mun su in ba ki rabonki."

Zubaida, da jin haka ta haɗa rai dan ta san ba abun arziki zata samu ba, watakila bazai wuce dubu ashirin ba. tana miƙa kudin sai ta ci gaba da bayani kamar haka...

"Mama saurayinda yace yana santa daganin shi ɗan manya ne, sai ma kinga irin shigar da ya ke yi dan na saba ganin hotunasa a wayar Ahmad kuma Mama in dai Khadija za ta aure shi to fa kin huta dan watakilama ba'a Nigeria zasu zaunaba dan daga sudan yazo."

Maman Khadija ta buɗe baki ta yi shewa cikin farin ciki harda guɗa sannan ta kalli Zubaida tace mata "ai aure kamar an yi shi an gama, dan anjima zan tafi da kuɗin nan gidan dan iyaa ya kama mana shi a hannun mu dan kada ya kuɓuce mana"

"Cikin tashin hankali da nuna damuwa Khadija tace "haba mama bakyau zuwa gurin boka fa, dan Allah kar ki je; na miki alkawarin zan bashi daman samun soyayya ta kuma zan kira shi a waya in sha Allahu."

Maman khadija tace "rufemun baki, wayace miki boka ne? tai mako yake badawa kawai, dan haka sai na je baki isa ki hana ni ba."

Zubaida tace "gaskiya kam Mama, dan in ya kuɓuce ba ƙaramun asara zamu yi ba."

Mugun kallo Khadija ta yi wa Zubaida sannan tace "Zubaida ta shi ki fi ta, ki koma gidanku dan Allah nasan inna tana jiran ki."

Maman khadija tace "rabu da ita Zubaida je ki gidan zan ne me ki, ki mun ƙarin bayani gobe, ke kuma Khadija zan yi maganin ki muddin ki ka ƙi amincewa da sairayin nan; dan baki isa ki rusa mun mafarki na a kanki ba. In da a garin nan na haife ki zance an canza mun ke watakila Zubaida ce 'yata ba ke ba dan halinmu yafi zuwa ɗaya."

Muryarta a sanyaye Khadija "tace mama bana jin daɗin abunda ki ke faɗa! amma dai ki yi hakuri kin san ɓanasan ɓacin ranki ko kaɗan."

Khadija, kinfi kowa sanin halin da muke ciki babanku ya rasu tun kuna yara dangin shi sun ƙi ɗaukanku kuma basa kula da ku, haka na yi rainonku ni kaɗai.
Dangin babanku basa son aurena da shi wai ni musulunta nayi, haka na rayu dasu cikin bakin ciki, mugunta da kuma hassada; ba abunda banganiba na wulaƙanci.
Na aurar da yayunki biyu da taimakon ƙanin mahaifinku wanda Allah ya masa rasuwa mako uku da suka wuce. Mazajen yayyenki ba suda komai sai talauci da tsiya, na yi ta ƙoƙarin fahimtar da su amma suka zabi soyayya akan mahaifiyarsu.
Dan haka ke bazan taɓa bari ki watsamun ƙasa a ido na ba, dan haka dole ne ki auri mai kuɗi damin da ke zan yi alfahari kuma na futo duniya ta sanni."

Khadija tace "mama duk wani wahala da ki ka sha a baya jarrabawa ce, Allah ne yake gwada imaninki. Ki yi haƙuri kuma ki yi ƙoƙarin cin jarrabawar in sha Allahu sa ki samu lada kuma za ki huta a gidan aljannah domin a gurin Allah kaɗai hutu yake ba'a dukiyaba."

"Hm! Khadija ke yarinya ce bakisan rayuwa ba, dan haka wannan wa'azinnaki bai samu shiga zuciyata ba kamar dai kullum." Mama ta faɗa.

Khadija tace "shikkenan, amma Mama ina neman alfarma awajenki"

Maman khadija tace "ina jinki, wani alfarma kenan?"

Khadija taɗanyi ajiyan zuci sannan tace "ina so na rabuda Zubaida dan bata dace da ni ba, bana san ƙawance da ita."

Maman khadija tace "wannan kuma tsakanin ku, ai kwalliya ta biya kudin sabulu daman na hadaku ne dan naga ta fiki wayewa zata taimakamun wajen samo miki miji nagari mai arziki."

Jin haka daga bakin Mamanta ya ba ta mamaki matuƙa, sai tace "dama dan haka ki ka haɗamu ƙawance da ita? haba mama wai mai ya sa baki damu da halinda na ke cikiba?
Na yi ta hakuri da Zubaida dan bana son halayenta kuma duk sanda na fadamiki bakya damuwa, Mama ni ce 'yarki ba Zubaida ba fa.

Maman khadija tace "na sani ai tunda ni na haifeki."

Khadija tace "shikkenan, yanzu dai ba za kije gurin dan iyan ba ko?"

Maman khadija tace "ba zan je ba, tunda kince za ki bashi dama, amma fa in har naga kin saɓa alƙawari to ni ma zan saɓa nawa alƙawarin."

Khadija tayi murna sannan tace "in sha Allahu bazan saɓa alƙawarina ba. na gode mama."

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now