Page 29

22 2 0
                                    

Safiyar litinin kenan mahaifin salma zaune a ɗakin taro a ma'ai katarsa suna gabatar da tattaunawa akan al'amarin company sai ya ga kiran waya daga mahaifin kamal amma sai ya tura masa da saƙon rubutu kan yayi haƙuri zai kira shi anjima kaɗan.
Bayan misalin ƙarfe goma da rabi na rana sai baban salma yakira mahaifin kamal kamar yadda yayi alkawari. sun ɗauki kimanin mintuna biyar suna tattaunawa akan al'amarin kasuwancin su sannan daga bisani mahaifin kamal yace dama na kirakane akan maganar auran yaran nan, mahaifin salma yace lafiya dai ko? Alhaji sameer yace lafiya lau sai alkairi. Wato akan abunda yashafi al'adu na hidimar biki nakeso muyi magana, a gaskiya ni fahimtata shine bai kamata muɗaura muku nauyin kayan ɗaki dana kitchen ba..

Baban salma yace ai wato alhaji sameer wannan ai ba wani abu bane tinda Allah yarufa asiri akwai ɗan abunda baza'a rasaba. Mahaifin kamal yace hakane kam to amma gaskiya ni sam ban aminta da hakan ba domin nafi fahimtar ace shi namiji shi ya dace ace yayi wannan hidimar, domin shi tanadin gurin zaman iyali bawai ana nufin ginin gidan bane kawai cikar ma'anar wajen zama shine samar da gidan dakuma duk abunda mazauna gidan zasu buƙata. Dan haka mu ɓangaren maza zamu samar da gida dakomai nacikin gidan a taƙaice hatta tsintsiya da bulugarin kaɗa miya za'a tanadar musu dashi, sai dai dayake kasan ance mata da ƙeke-ƙele ba'a rabasu anan ina iyacewa in sunje gidan sukaga akwai abunda suke ɓuƙata to sai a kawo musu.
Mahaifin salma yace to ai niharna rasama mai zance, amma kanaganin yanzu sai in naɗe hanu kenan babu wani abu dazamuyi? Gaskiya ni inaganin kamar wahalar zatai muku yawa...
Baban kamal yace ai haka ya kamata domin kuwa muda aka bamu kyautar 'ƴa mu yakamata mubada tukuici dan haka kada ka damu. to amma kana iya saya mata ɗan kayayyaki na sawa a hidimar biki tin da naga haka yaran yanzun suke yi, sannan kuma in dai dan ita yarinyar ake wannan hidimar kayan ɗakin to ai zan iya cewa ba ai dabara ba domin kuwa duk waɗannan kayayyaki da aka siya mata tare zasu kashe kuma su ƙarar ita da mijin. Dan haka mai zai hana ayi amfani da kuɗin a siya mata abun da zai amfaneta misali fili, gidan da zata sa haya, motar haya ko sarƙar gold da sauransu. Mahaifin salma yace to amma meye fa'idar yin hakan kenan dan maganarka gaskiya ta kama hankalina sosai. baban kamal yace wato kai dai baka rabo da abun dariya! Ai fa'idar wannan maganar a fili ta ke musamman a wannan zamanin. To amma tinda ka tambaya barin faɗa maka wasu daga ciki...
Na farko dai iyayen yara mata zasu samu nitsuwa da kwanciyar hankali saboda a zamanin yanzu haihuwar mata ana so a maidata kamar haihuwar mata a lokacin jahiliyya. Su mutanen baya tsoron talauci yake sa su kashe matan na yanzukuma tsoron ɗawainiyar biki sai yasa uba rashin jin farin ciki a ransa idan Allah ya bashi yara mata musamman in sunkai biyu uku zuwa huɗu....
Abu na biyu akwai samun amintuwa na iyaye wajen yadda da iya ƙarfin arzikin da Allah ya basu kuma hakan zai fidda kwaɗayi daga zuciyar iyaye da kuma yara matan, domin yawanci iyaye suna so yaransu mata su auri mai kuɗi dan su samu na gado da katifa a hannunsu, to idan ya fahimci ba shi zaiyi ba hakan zai sa ya maida hankali wajen zaɓen mijinda ya dace wa 'yarsa itama kuma yarinyar kwaɗayin ta tara kuɗi dan bikinta zai ragu in sha Allahu...
Na uku shine za a samu saukin tallace tallace na yara mata dan kaso casa'in cikin ɗari suna yi ne dan tara kuɗin sayayyar kayan aure wanda garin haka ne mafi yawa daga cikin su suke rasa budurcin su tin basuyi auren ba...
Na huɗu shine za a samu cikakken kulawa da ƙokarin inganta tarbiyyan yara mata idan aka ɗaukewa iyayensu kayan ɗaki domin an ɗauke musu wani nauyin da kullum suke taradda dinsa a cikin zuciyarsu hakan kuma zai basu daman kula da matan yanda yakamata...
Na biyar shine su kansu mazan zasu ƙara nitsuwa da al'marin aure da kuma saki musamman in ya fahimci irin wahalan farko na yin komai hakan zaisa ya jure ya kuma zama mai hukuri da hangen nesa sannan kuma za a samu kekkewan girmamawa da ganin ƙimar juna tsakanin ma'auratan musamman ita macen idan ta fahimci duk kayan gidan na mijinta ne to hakan zai sa taji a ranta cewar ita ce a ƙasa da shi ba kamar ace komai nata bane domin wata ko matsala suka samu da mijin sai ta hanashi kwana kan gado in ya koma parlour nan ma tace ai kujerunta ne in ba sa'a akai ba to a sallayarsa zai kwana 😁
Abu na shida wanda shine na ƙarshe shine za a samu sauƙin yawan gori tsakanin dangi wajen kushe na kayan aure da akeyi musamman mata.

Mahaifin salma yace masha Allah gaskiya abokina na gamsu kuma in sha Allahu yanda kace hakan za ayi ina fatan wannan aure yayi albarka yasa yazamo abun alfahari. baban kamal ya amsa da amin.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now