Page 26

19 3 0
                                    

Tabbas jikin hajiya samira yayi sanyi sosai,hakan ya bashi damar cigabada yimata nasiha akan rayuwa dakuma yadda mutuwa take ratsa lungu da saƙo tana ɗauke mutane masoya na rabuwa, iyaye na rabuwa, ma'aurata na rabuwa ba dare ba rana a kowani lokaci. Hajiya samira tasake cewa baban kamal ya kaita wajen hajiya bilkisu dan ta bata hakuri kuma su sasanta tsakaninsu.
hakan kuwa akai bayan sallan azahar baban kamal ya ɗauketa a mota ya kaita.
Isar su gidan keda wuya sai suka ga motar asibiti a tsaye a ƙofar gidansu salma sannan ga taron mutane a tsaye carko-carko kowa jikinsa a sanyaye baban kamal yace meyake faruwa kuma haka? Allah kadai yasani cewar Hajiya samira, sannan taƙara decewa amma Allah yasa lafiya, bayan sunyi ajiye mota a gefe, kawai sai sukaga anfito da gawan Maman salma wato hajiya bilkisu daga motan, take hajiya samira ta koma baya zata fadi sai baban kamal ya tareta, ahankali yariƙeta suka ƙarasa ƙofar gidan.  Maman ƴan biyu ce tafito da salma daga motan tana kuka idonta yayi jawur hijabinta sharkab da hawaye fuskarta duk ya kumbura zuciyarta cike da damuwa da alhini da bakin ciki amma bakinta ba abinda ke faɗa se Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un, hasbiyallahu wa ni'imal wakil, la haula wala kuwata illa billah,  rabbigfirli wali walidayya rabbi rahamhuma kama rabbayani saghira...

Cikin sanyin jiki suka shiga gida aka kwantar da gawan hajiya bilkisu a side ɗin mijinta kamar yadda yayi musu umarni.
A ƙofar gida kuwa baban kamal ya dafa kafaɗun abokinsa yana masa ta'aziyya tare da nuna damuwa akan babban rashi da akayi, cikin ƙarfin hali baban salma ya shiga gida inda aka ajiye hajiya bilkisu, da ƙyar ya danne zuciyarsa yayiwa matarsa wanka kamar yadda addini ya tanadar salma ta kawo likkafani ta miko masa tabakin kofa, yasa hanu yakarɓa yayiwa matarsa sutura a dai dai lokacin ana kiran sallar la'asar. Bayan anyi sallah aka bada sanarwan sallan jana'iza a masallaci, wani abun mamaki shine tsakanin azahar da la'asar mutane suncika gidan da waje har bakin titi duk anguwan ya cika makil da mutane.

Safiya, kamal da hajiya aisha sun iso amma ba hanyar shiga gidan saboda cikowa kasancewar ana shirin yimata sallah, amma ahaka kamal yaƙarisa cikin mutane yasamu sahu, sukuma su safiya suka shiga wani gida a gefe harseda akai ma hajiya bilkisu sallah aka tafi da ita sannna su hajiya aisha suka samu shiga gidan, safiya tana ganin salma sai ta tina da nata maraicin duk da lokacin da ta rasa mamanta batada wayo sosai..

"Salma" cewar safiya ta kirata cikin sanyin murya, dajin muryar safiya ta juyo da sauri ta rungumeta da karfi tace safiya mama ta tafi kawai suka sa kuka afra itama ta jonasu akarasa mai bawa wani hakuri, hajiya samira ta jawosu ajikinta tana rarraahinsu har suka ɗan samu nutsuwa, zuwa dare ƴan uwa da dangin alhaji da hajiya sun fara isowa daga garuruwansu, bayan sallan isha'i hajiya samira tayiwa salma da afra sallama zata koma gida seda safe zata dawo amma safiya zata kwana tareda su, shima baban kamal yayi sallama da abokinsa, hajiya aisha da hajiya samira suka fiyo Baban kamal ya ɗaukesu a mota suka tafi, shima kamal ya ɗauki matarsa ya wuce gida duk da aransa ba wanda yakeson gani irin salma amma hakan bazai samuba se sakonnin waya yaketa aikamata masu cikeda nuna mata tausayi, ta'aziyya, da kuma kulawarsa agareta.

Mahaifin kamal yafara sauke hajiya bilkisu agida seya wuce da hajiya aisha kasancewar kwananta ne yau, bayan sun isa gida se hajiya aisha ta fahimci irin damuwar da yake ciki dakuma yanda zuciyar sa ta koma kan hajiya samira da tinanin halinda take ciki, bayan sun zauna a parlor sai hajiya aisha ta dafa hannunsa tace abban kamal mezai hana ka koma wajen maman kamal dan yau tana ɓukatarka sosai naga alamunta tamkar wacce aka sallamo daga asibiti jikinta sam ba ƙarfi.

Baban kamal yace nagode dakika fahimceni hajiya aisha, na tabbata hajiya samira bazata taɓa mantawa da wannan alfarmanba, cikin sanyi murya hajiya aisha tace badan ita nayiba dan kai nayi kijina. Baban kamal yace nagode matata barin je insameta...

Bayan kamar minta talatin alhaji sameer ya isa gidan uwar gidansa hajiya samira, yana shiga yaganta a parlour ko ɗaki taka shiga, baban kamal yaɗan kaɗa kai alamar tausayi yace my dear... Se lokacin tadawo hankalinta ta juyo taga mijinta cikin hanzari hajiya samira ta iso gareshi ta rungumeshi tana kuka daƙyar tabuɗi baki tacemasa bilkisu tatafi ta barni bannemi yafiryataba kuma banyi sulhu da itaba yanzu ya zanyi😭

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now