Page 18

23 3 0
                                    

Kamal yana shigowa gida yaga hajiya samira ta canza yanayi tsarin komai na parlour ɗinta, yanayi zamansu da kuma sabbin kananun indoor flowers komai yayi dayaanayi gurin gwanin ban sha'awa...
Hajiya samira tace yakai bakace komai ba, kode gyaran beyi bane?

Kamal yace sosai ma mum, kin canza komai kamar gidan amarya kuma kema kinyi kyau sosai, yau daddy bazai ganekiba..

Maman kamal tace ka maidani kakar ka ko, namaka alƙawarin zan canza shiyasa na canza yanayin abubuwan  dan inaso komai yayi kyau sosai se kamal yace gaskiya naji daɗi mum, zanje ɗakina na huta dan kaina yana ciwo. Cikin nuna tausayawa hajiya samira ta kama hanunsa sannan tace  Allah sarki sannu, barin ɗauko maka magani kasha zaiyi sauki in sha Allah.
Idan kasamu sauki akwai albishir danakeso nayi maka..

Kamal yaɗanyi murmushi sannan yace albishir na meye mum?

Maman kamal tace naje na tambayi mahaifin safiya akaro nabiyu yasake amincewa zata dawo tazauna tareda mu, dan haka kafara tsammanin ganin amaryar ka in sha Allahu.
Take kamal yaji kaman an tsaga kansa gida biyu sabida ciwo dan haka ya buɗe baki da ƙyar yace mum yanzu ba lokacin maganannan bane kibari se wani lokaci please..

Maman kamal tace shikkenan ba komai, amma kamar bakaji daɗin maganarba?

Kamal yace  kawai de dan banajin daɗi ne shiyasa, Allah ya kaimu lokacin kinga kin huta zaman kaɗaici in bama gida. Maman kamal tace amin, ashede ka fahimceni

Bayan ya shiga ɗaki ya kwanta seya fara zancen zuci shikaɗai yana cewa hmm rayuwa kenan wacce nakeso daban wacce ake shirin auramin daban, ya Allah gani gareka kazaɓamun abinda yafi alkhairi ga rayuwata, addinina dakuma abunda zan haifa nan gaba..

Jim kaɗan kuma yasake nutso cikin kogin ƙauna yace kode nakira salma ne 🤔...

Can kuma yace nasan kona kira bazata ɗaukaba, yanzu ya zany? Sannan yaci gabada cewa wani lokacin zuciya bata adalci wajen soyayya duk da cewar salma da safiya kusan halinsu ɗaya amma ni salma nakeso, inda ace safiya ce toh da komai ya tafi daidai, wayyo Allah jinake kamar kaina zai fashe gashi bansan ya zanyi da mum ba intaji ina san salma... Huuuuuu what should I do????

Hajiya samira taɗauko magani da ruwa takaiwa ɗanta kuma shalelenta tsoka ɗaya amiya kmar yadda tasaba faɗa. Bayan yasha maganin setaji shigiwar baban shi yana sallama a parlou, cikin hanzari da murmushi a fuskarta tafito tace wa'alaikumus-salam barkada zuwa ranka ya daɗe..

Baban kamal yaɗanyi murmushi sannan yace yauwa barka, hajiya samira kode ɓatan hanya nayine?

Maman kamal tace bawani ɓatan hanya, me gida ai baya manta hanyan gidansa

Alhaji sameer yace toh ai naga komai bayanda na tafi na bariba shiyasa, amma komai yayi kyau sosai

Hajiya samira tace hakane, wanna duk dan kai akayisu ammade yanzu muje kaɗan watsa ruw, ga abinci nan yana jiranka

Baban kamal yaɗanyi murmushi yace ikon Allah, toh barin dau jakar tawa sai na shiga ciki. Hajiya samira tace haba kabarshi zan ɗauka ai batada nauyi

Baban kamal yace masha Allah toh nagode, amma my dear kinyi kyau fa sosai, sewani walƙiya kikeyi kina haske kamar farin wata daren goma sha biyar, gaskiya dolene nabiya tukuicin wannan kwalliyar

Maman kamal tace kaide baka rabo da zolaya, toh nagode ranka ya daɗe

Baban kamal yace ina kamal fah, ince de yaje makarantar islamiya? Hajiya samira tace eh yaje, gaskiya kamal yanzu Alhamdulillah duk ya canza kamar bashiba. shigarsa, kalamansa, yazama mutum sosai masha Allah

Baban kamal yace toh Alhamdulillah, ai haka akeso dama can ai... Kafin yaƙarasa setayi wuf tace nice na batashi ko?

Baban kamal yace ba haka nayi niyan faɗaba ina nufin rashin tsayuwa wajen karatun addinin yasa yazama wani iri amma yanzukuma Allah shiryeahi kuma ina fatan Allah yasa ya ɗore akan hakan dekema baki ɗaya sannan Allah yamuku albarka. Hajiya samira tace amin kaikuma Allah yakara maka hakuri damu.

Baban kamal yace wai ikon Allah kenan anya kece kuwa? maman kamal tace nice mana....

Bayan kamar minti talatin, Maman kamal da babansa sunfito cin abinci a dining table

Maman kamal tace yaude Inada tarin abun fada amma narasa ta ina zan fara..

Baban kamal yace to ina tinanin kifara ta kasa sai kiyi sama kinga ko haddace akace ta kasa yafi sauki

Maman kamal tace shikkenan dafarko dai iname baka hakuri dan gaskiya nayi nadaman duk abinda nayita maka, tin baka mayarmun har na ƙureka kafara tankawa, dan Allah kayi hakuri kuma namaka alkawarin bazan sake ɗaga maka hankaliba

Baban kamal yace Alhamdulillah, gaskiya bansan wani irin farin ciki zanyiba da Allah ya nunamin wannan rana me albarka, kuma wato duk wanda ya rike Allah toh tabbas shine ya dace duniya da lahira, wato samira tafiyan nan danayi naga abun mamaki da ido na

Maman kamal taɗan gyara zamanta tace meya faru?

Baban kamal yace wani bawan Allah ne nagani washe garin tafiyata daga nan ya kwana ajikin mota na, to nazo zan shiga mota da safe sai na ganshi nayi zaton mahaukaci ne ashe lafiyarsa ƙalau, da yaga nazo zan shiga mota seyacemin Assalamu alaikum! Sai na amsa masa seyace dan Allah alhaji katemakeni yanda Allah ya tai makeka! Sai nace mai ya faru. 

sai yake bani labarin dashi da matarsa da yaransu biyar suna daf da mutuwa, nace subahanallah meya faru haka? Yace yau kwana uku kenan ba abinda sukaci sai ruwa shiyasa ya fito nema amma shima seya kasa tafiya ya kwana a nan yanzu bai san ya sukeba. Hajiya samira ta taɗan nuna alamar tausayi sannan tace ikon Allah kenan..

Baban kamal yace dafari naji tsoro sabida yanda rayuwa yazama, ammade senayi addu'a na nemi tsarin Allah daga sharrinsa. Bayan nadaukeshi a mota sai mukaje gidan shi nasamu iyalan duk akwance sun gala baita na ɗaukesu muka tafi asibiti akayi treating nasu suka kwana washe gari muka dawo gida, muhallin zaman ba laifi kasancewar wani mutumne ya basu aro kafin yasamu gurin zama lokacinda aka koreshi daga haya, gaskiya mutumin yaban tausayi sosai

Maman kamal tace Allah sarki koni naji tausayinsu gaskiya. Aamma wani temako kamusu?
Seya amsa yace nazo dasu nabasu gidana dayake babban layi sannan abinci, sutura, da sauran abun buƙata nasa ankai musu, maganan makarantar yara kuma sai daga baya in sun samu nutsuwa, zuwa gobe zankaiki kugaisa dasu kuma nabashi Takaddun gidan, nafadamikine sabida halin mutuwa

Maman kamal tace masha Allah, gaskiya kayi kokari, Allah yasa kafi haka kuma Allah yasakamaka da gidan aljanna

Baban kamal yace amin my dear, amma kinsan me? tace a'a sai in ka faɗa..

Baban kamal yace adduan danayi agurin bayan nafito daga gurin mutumin nan shine, nace Allah ya karɓi aikin danayi kuma yasa yazama sanadi nasamun fahimtar juna tsakanina dake da hajiya aisha baki ɗaya, kuma gashi ina dawowa naga ikon Allah Alhamdulillah.

 BA ƘAUYANCI BANEWhere stories live. Discover now