1&2

386 14 0
                                    

🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page


1 and 2

Haisam shine kad'ai d'a a gun Mahaifiyar sa Wacce ta kasance talaka, Mahaifin sa ya rasu tun Haisam na 'dan shekara biyu a duniya.Mahaifin sa mai kud'i ne sosai shiyasa wasu daga cikin yan uwan sa suke bakin Ciki. Duk da ya kasance Mai taimakon mutane sosai ga duk Wanda yake neman taimako daga gareshi, hakan bai Hana Yan uwansa Shirin kashe shi ba sabida su mallaki dukiyar sa.

Da sun so shi sabida shine kad'ai Wanda Allah Albarka ce shi da d'a na miji. A Haka, wani daga cikin su ya sa mishi guba a abinci.

Mahaifin Haisam yayi duk abinda yaga zai iya don ya ceci ransa daga guban Amma ya Riga ya Masa illa a jikin sa.

Bayan rashin lafiya na watanni biyu sai ya rasu, Amma Kan ya rasu ya bawa matar sa wasiya akan ta tabbar ta ilmantar da Haisam Boko da addini komin tsadan sa.

Bayan wata d'aya da rasuwar sa, wannan d'an uwan sa da yasa Masa guba yazo ya kwace dukkanin dukiyar, ya bar su ba ko sisin da za su rike.

Rayuwa duk ta lalace wa Haisam da mahaifiyar sa, da kyar suke samun abinda zasu sa a cikin su, Amma duk da wahalan da suke Sha Bai Hana ta sa shi a makaranta Mai kyau ba, sabida shine wasiyar Mahaifin sa.

Haisam yaro ne Mai kokari a makaranta, ya kasance shine yake zuwa na d'aya a cikin shekaru uku da yayi a junior secondary School, tunda da ga Nan ya kafa record. Ya cigaba da kokarin da ya Saba har ya Shiga senior secondary School. A yanzu Yana aji SS3 babban matsalar sa shine inda zai sami kud'in registration na W. A. E. C.

MAKARANTA

A ko da yaushe Haisam na Zama shi kadai, baya kula kowa harkan gaban sa kawaii yake yi sannan bashi da abokai, Duk da ya kasance Yan ajinsu sukan Zo gun sa don ya ganar dasu darasussukan da ya shige musu duhu ko basu gane ba, Yana da kirki sosai ga ilimi sannnan a shirye yake da ya ga ya taimaka musu, wata Rana a aji, darasin English ake musu, Haisam na zaune kusa da Ma'isha wacce ta kasance sabuwar zuwa ce a makarantar tasu, Ma'isha yarinyar kirkice daga gidan masu kudi, Bai dad'e da aka zabi Mahaifin ta a matsayin chariman na karamar hukumar su ba. A Lokacin da ake darasi malamar su Tace "Who can define phrase?" Duk Wanda suka amsa ba dai dai ba aka sa su kneel down. Haisam ya San amsan Kuma ya lura da Ma'isha na tsoro sabida bata San amsar ba, yayi saurin rubuta amsar a paper ya Mika mata. Nan take Ma'isha ta karb'a, malamar ta juyo gareta Tace "Ma'isha Mus'ab Aminu, answer the question, what is a phrase?"

Ma'isha mikewa tayi ta tsotsa keyan ta wasu daga cikin Yan ajin suka shiga yi mata dariya a ganin su baza ta iya bada amsar Amsar ba "A phrase is a group of words that does not contain a finite verb and cannot stand alone to make a complete sentence" ta bada amsar cikin hikima da basira, malamar Tace " Excellent, class give her a round of applause." bayan sun fita break cikin sauri ta sayi biscuits da soft drink wa Haisam.

"Hy Haisam, I want to thank you for your kind heartedness. You really saved me from the teacher's punishment and embarrassment." Ma'isha ke Wannan maganar.

"You are welcome"kawai yace mata
"Please take this snacks for my appreciation"
Murmushi yayi yace "No thanks, no need for these really"
Cikin murya kamar zatayi kuka Tace "But please am trying to show my appreciation, Dan Allah ka karb'a"

" Na sani I don't think I need it, ko da yake ban ga dalili da zaisa ki dami Kanki ba"
" Ban damu ba, ni dai Dan Allah ka karb'a Dan Allah, idan baka karb'a ba bazanji dad'i ba".

Musaddiq, da tun dazu yake kallon su ya matso kusa yace "He does not want it, is it by force? Ko da yake, ni ina bukata bari na taimaka masa. " Haisam da Ma'isha hararar sa sukayi Rai a 'bace, ganin hakan yasa yayi saurin barin wajen, Haisam karb'a yayi sannan ya mata godiya, Ma'isha ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.

"Na sani dama ka na jin yunwa, but you're just pretending" ta yi maganar a sigar tsokana. Yace " Kul, ki iya bakin ki",hakan yasa ta bar zancen.

Haisam na ci suna Hira suka gabatar da Kan su wa juna ba dad'e wa aka tashe su, wasu iyaye na zuwa d'aukan 'ya 'yan su, Driver a ka turo ya Zo d'aukan Ma'isha, Haisam na daga cikin yaran da, da kafa suke zuwa makaranta sannan su Koma da kafa, A Lokacin da Ma'isha ta ganshi ta umurci driver da ya tsaya Tace "Haisam ban San sanda ka tafi ba, Amma ka shigo mota , mu ajiye ka gida."

"A a nagode, hanyata da Taki ba d'aya bace, Kuma na ma kusa Isa gidan namu baida Nisa da Nan" " Kar ka damu zamu Kai ka, komin kankancin nisan gidan naku" ganin tana neman takura shi, yayi tafiyar sa. Suman tsaye tayi tana bin shi da kallo, tana mamaki "wai shin Haisam wani irin mutumne haka?" A zuciyarta ta ayyana hakan, d'aga kafad'a tayi ta shige mota, d'aliban da suke gun Wanda suka ga abinda ya faru suna cewa ina ma ace sune Haisam, idan suka samu wannan damar baza su bari ya wuce su ba.

Bayan ya Isa gida ya tarar babu abinci a gidan nasu kamar kullum, uniform d'insa ya cire sannan ya nufi kasuwa don ya taimakawa mahaifiyar sa, Koko take yi da kosai dashi suke rufa wa kansu asiri, Bredi ta saya Masa, had'awa yayi da kosai yaci Shine abincin ranar nasa.

Da yamma, Kosai da doya ya d'auka a Tray ya fara talla a bakin titi, Yana cikin tallan ne ya hango wata mota kamar wacce aka Zo d'aukan Ma'isha da shi d'azu yayi saurin 'buya a bayan wani shago yana kallon motar ga mamakin sa sai yaga Ma'isha ce da mahaifiyar ta, sun Zo sayayya a kasuwar gwari.

Kasa motsi yayi don baya son Ma'isha ta ganshi yana tallan Kosai a bakin titi, Ma'isha da mahaifiyar ta sun d'auki lokaci sosai Wanda hakan yasa shi kasa sakin jikinsa, Wani mutumi Wanda ya kasance kullum sai ya saya kosai da doya a gunsa ya hango shi ya shiga kiransa sunan sa Amma Haisam yayi burus kamar bai jishi ba,sabida idan yaje Ma'isha zata iya ganin sa.

"Ka kyale ni don ni ba zuwa zanyi ba,gara ma kayi Shiru " zancen zuci yake. Mutumin ya zago ta bayan sa,dafe shi yayi a kafad'a yace "Haisam lafiya kuwa? Ko Kuma ka kurmance ne?" "Eemm... kiyi hakuri nayi nisa ne a tunani" "Mene haka da har yafi kasuwancin ka muhimmanci? Ko da yake kosai zaka bani na naira saba'in sai doya na talatin" ba musu ya sauke tray din ya sa a bakin leda ya mika masa.

Bayan Ma'isha da mahaifiyar ta sun gama sayayyar da zasu yi a Lokacin gari har ya fara duhu, hakan yasa bai sayar da kosan ba, hakan yasa yaji duk ransa a 'bace. A hanyar sa ta komawa shagon su ya hango Ma'isha da mahaifiyar ta na sayan kosai a gun Mahaifiyar sa. Iska mai zafi ya hura ya kuma neman wuri ya 'buya.

" Wai meyasa mutanen Nan suke bina duk inda naje? Hmm Allah yasa ba kullum zasu Rika zuwa Nan wurin ba, mutuncina da Ma'isha take gani zai zube" ya fad'a a bayyane. Sai da ya jira suka tafi sannan ya Koma shagon,
Mahaifiyar sa tayi matukar mamaki da ganin bai sayar da kosan ba.
_____________________________
Comments and Share
Milhat ce
Yar Terawa

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now