Kallon Baffan sa yayi yace "Dan Allah ka tashi baffa meyasa zaka durkuwa a gabana bayan kana matsayin ubane a gare ni, Ni na yafe maka duniya da lahira, maganar gida Kuma na bar maka shi halak malak hatta company d'in da kake aiki a Cikin na mallaka maka"
Malam hassan kirkirerren kuka ya Fara yi yana fad'in "Nagode, Nagode Haisam Allah ya maka Albarka" ya maida kallon sa ga Umma yace "Zainabu kiyi hakuri ki yafe min Dan Allah"
"Bakomai na yafe maka, Allah ya yafe Mana baki d'aya."
Duk suka amsa da amiin, Malam Hassan Banda godiya babu Abinda yake har suka fice daga gidan, Nan su Daddy suka shiga hirar su suna farin cikin nasarar da suka samu.Tana ganin shigowar sa ta mike tana fad'in "Daddy ya dai? Da fatan anyi nasara"
Murmushin irin zasu gane kuren su yayi yace "Yar daddy ai daddyn nakin ba daga nan, plan d'inmu zai Fara ne daga yau, na gama nawa saura naki"Murmushi tayi Tace "Insha Allah Daddy kasa ranka anyi an gama kawai"
"Allah ya miki Albarka Yar Daddy"
Ta amsa da "Ameen."Umma da Haisam hankalin su kwance ko bakomai sun karb'i hakkin su, Basu da sauran damuwa a rayuwar su, duk wanni abu da suke bukata na jin dad'in Rayuwa suna dashi.
Wannan Kenan
Haisam da Ma'isha shakuwace Mai karfi ta shiga tsakanin su tare suke zuwa makaranta su dawo tare, kullum Haisam ke Kai su school, ko da kuwa bai da lectures yakan kaita ta idan sun tashi ya koma ya d'auko ta wasu lokutan Kuma ya jira ta har sai ta gama su koma gida.
Umma da Mummy komai tare suke hatta unguwa zasuje tare suke zuwa shopping, har kauyen su Mummy tare suke zuwa.
Haisam ke zaune a Cafeteria yana cin abinci,Yana jiran Ma'isha ta Gama lectures,cin abincin sa yake hankalinsa kwance yayin da d'ayan hannun sa yake Kan wayar sa, wata budurwa da baza ta haura shekaru 20 ba ta nufi inda yake, da sallama ta karasa inda yake a hankali ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar ta, kallon ta ya tsaya yi, Murmushi tayi Wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar fuskar ta Tace "Sannu dai"
Dai dai ta nutsuwar sa yayi ya amsa da "yauwa sannu da"
"Dan Allah idan baza ka damu ba zan iya Zama anan?" Tana nuna kujerar da ke fuskan ta nasa.Yace "Eh... Eh zauna Mana"
Tace "Nagode, ta jaa kujerar kana ta zauna tana Murmushi, waige waige ta Fara yi kana ta hango wata ta d'aga Mata hannu had'e da fad'in "Waiter!!!"Cikin sauri ta karaso inda take Tace "Welcome ma what will I offer you?"
Kallon Haisam budurwan Nan tayi da ya maida hankalin sa Kan wayarsa, Murmushi tayi Tace "Ki bani irin abincin da yake"Haisam d'an d'agowa yayi ya kalleta ya girgiza Kai had'e da Murmushi ya cigaba da cin abinci sa, ba a d'au lokaci ba ta dawo plate d'in chicken and chips, tasa hannu ta karb'a.
Ganin Haisam bai kulata ba tayi gyaran murya Tace "Ni suna na Aysha kaifa?"
Ba tare da ya d'ago ya kalleta ba yace "Haisam"
Tace "Wow Nice name, kai a school d'in Nan kake ne?"
"Eh"
"Wani department?"
"Medicine"
"Nima a medicine nake Amma ban tab'a ganin ka ba, Amma aji nawa kake?"
"200 level"
"Oh shiyasa ni a 100 level nake"
Yace "Maybe"
Duk maganar Nan da suke bai d'ago ya kalleta ba."Lalle gayen Nan akwai rainin hankali duk yanda nake so muyi Hira ya kasa sakin jikinsa , dama ance kyawawan mazan Nan haka suke da girman kai" duk maganar Nan a zuciyar ta take.
Bata lura ba har ya Kira Waiter ya biya su kud'in su ya Mike zai tafi, karar kujeran da ta jaa Ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula da murya mai d'an karfi Tace "Ina Kuma zaka?"
Kallon ta yayi cike da rashin fahimta yayi d'an Murmushi yace "Gida" ya juya zai tafi tayi saurin mikewa Tace
"Dan Allah ko zaka iya bani number ka?"
"Number ta Kuma?"
"Eh number ka"
" Da fatan dai ba laifi nayi bako?"
Murmushi tayi Wanda hakan yasa Beauty point d'inta ya nuna tace "A a kawai so nake muyi wata magana da kai idan bazan takura maka ba"
Yace "Okay" ya Mika hannun sa alamun ta Mika Masa wayar ta, cikin sauri ta Mika masa wayar Yana sawa ya Mika Mata ya fice daga gun, bata samu damar yi Masa Godiya ba, Yar karamar tsaki tayi Tace "Anya gayen Nan zai Soni kuwa?"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali