kallon Yayan ta Mardiya tayi kana ta sunkuyar da kanta kasa tace "Tun ranar da na ganki a cafeteria da Haisam na gane ki, sabida nasha ganin hotunan ki a wayan Meerah, Ayrah ta nuna min tana son sa nice na zugata mukaje gun Boka aka asirce shi, sannan ta bini akan muje mu tona naki, Haisam bazai tab'a son wata ba in har Wannan layan na kasa"
Isha Mikey tayi cikin Muryar kuka tana ambaton sunan Allah tana fad'in "Mardiya why? Mardiya me muka miki haka da kike son ganin mun wulakanta?"
Kai a kasa tace "Meerah Qawata ce tun muna Yara dake unguwar mu d'aya ke Kuma kawar Tace a makaranta, Meerah tana samun Duk wani gata da jin dad'in Rayuwa iyayen ta sunfi nawa karfi bayan hakan Kuma suna sonta sosai kasantuwar ita kadaice Yar su shiysa da Usu ya Zo min da bukatar sa na amince sabida nasan Dole iyayen ta zasu tsane ta, maganar ki da Haisam Kuma hoton ku na gani ke dashi a wayar Meerah sai naji na kamu da son sa ganin irin Soyayyar da kukewa junan ku nasan bazan tab'a samun Soyayyar sa ba, shiyasa na yi kokarin raba ku, duk Wanda ya ganku zai gane Kuna son junan ku Amma, Haisam bai gane ba shiyasa mukayi amfani da wannan damar wurin rabaku,amma Wallahi tallahi ban san Shirin rabuwa take dashi ba plan d'inta ne da mahaifinta Wanda ni ban sani ba, Amma a yanzu nayi na dama kuma na miki alkawarin yau d'in Nan zanje na cire layan Nan"
Cikin Muryar kuka Tace "Kin cuce ni kin cuci masoyina bazan tab'a yafe miki, a dalilin Kune na kamu da ciwon zuciya, sannan a dalilin kune Yayana Yana chan yana kwance Rai a hannun Allah, bazan tab'a yafe muku ba"
Durkusawa mardiya tayi ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko Tace "Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min, wallahi alhakin kune yake ta bina gashi na gama makaranta sama da 3 years Amma babu Wanda ya tab'a zuwa gidan mu da sunan yana Sona, in ko an min zancen Soyayya to jikina suke so Dan Allah kuyi hakuri ku yafe min"
Meerah itama mikewa tayi a tsawace Tace "yafiya? Har kina da bakin neman yafiya a wurin mu? Shin zakiyi iya Dawo min da budurcina da kimata da na rasa a dalilin ki?" Isha ta d'aura da fad'in "Shin Zaki iya Dawo min da Yayana? Zaki iya sa ya tashi? Ko Kuma zaki iya bani lafiya" Cikin tuhuma suke mata maganar.
Meerah Tace "Baza ki iya bako? To kamar yadda baza ki iya Dawo da wa'an nan abubuwan da muka rasa a dalilin ki ba Haka baza mu iya yafe miki ba" riko hannun Isha tayi da niyar barin d'akin har sun Isa kofar fita, Ma'aruf yace "Isha please " a hankali suka juyo suna kallon sa, ya karasa inda suke yana matsar kwalla yace "Nasan an zalin ce ku, har abada abinda kuka rasa baza su Dawo ba, Dan Allah ina rokon ku, ku yafe mata on my behalf, and please Isha Kar abinda Kanwata ta aikata a gare ki ya sa ki janye maganar aurena dake"
Murmushin gefen baki tayi kana Tace "It can never happened"
Cikin rashin fahimta a d'an kid'ime yace "What? Isha please Kar kice baza ki aure ni ba Dan Allah"
Girgiza Kai kawai tayi ta fice Meerah na ta bi Bayan ta yana Kiran sunan su basu juyo ba bare su saurare shi ya dad'e a tsaye a gun ya rasa abinda ke Masa dad'i d'akin shiru yayi Banda sautin kukan Mardiya babu abinda kake iya ji a parlorn, cike da takaici ya kalle ta Kiran sunan ta yayi da d'an karfi "Mardiya!!!A d'an razane ta d'ago kanta had'e da mikewa jikin ta na kyarma cikin rawar murya Tace "Na...naaa..... Na'am Yaya"
Cike da takaici ciza leb'en sa yayi yace "Are you happy now? Kinji dad'i ko? A dalilin ki na rasa masoyiyata"
"Wallahi yaya ban sani ba, ban San itace wacce kake so ka aure ba da ban....... "A tsawce ya katse yace "Da bakiyi me ba? Oh sai kin San cewar zan aure ta ne tukkunna kisan abinda ya kamata? Who gave you the right to mingle in someone's life? Me suka miki? Nace me suka Miki?" Ya karasa maganar cikin tsawa har Saida ta razana ta jaa da baya a tsorace cikin Muryar kuka Tace "Yaya please" daka mata tsawa yayi ya nuna ta da 'dan yasa yace "This will be the last day da zaki sake kirana da wannan sunan Ni ba Yayan ki bane, daga yanzu na yanke ki daga jikina" ya Kama hanyar fita da gudu ta karasa inda yake ta rike kafafun sa tana kuka had'e da bashi hakuri, hankad'e ta yayi da kafar sa ta buge bakin ta a Kan tiles d'in dake gun Nan da nan bakinta ya Kumbura ganin ya fice ta bi Bayan sa cikin sauri.
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali