*WASHE GARI*
Alarm d'insa ne ya fara bugawa mikewa yayi ya kashe, d'akin su ya nufa ya Shiga babbuga mata kofa, zumbur ta mike a d'an tsorace, bedside lamp ta kunna kallon d'akin ta shigayi tana mamakin a wani d'aki take, sunan ta da taji ya Kira ne kamar rad'a yasa ta kalli kofan shiru Bata komai ba, a karo na biyu ya Kuma cewa "Isha!!!
Cikin Muryar bacci Tace "Na'am"
"d'an bud'e kofar asuba tayi"Mikewa tayi jiki ba karfi ta bud'e Masa kofar,Kan gado ta koma ta zauna shi Kuma ya Shiga ban d'aki,alwala yayi Bayan ya gama ne ya fito ya wuce Masallaci ba tare da yace Mata uffan ba.
Itama mikewa tayi ta Shiga ban d'aki tayi alwala ta shimfid'a sallah ya Shiga yin sallah,Bayan ta idar ta zauna Akan sallayar tana azkar.
Ma'aruf Kuma bai dawo cikin gidan ba har sai da gari ya fara haske,ya Shigo har cikin d'akin bakin sa d'auke yake da sallama,tana zaune akan sallaya, d'ago kanta tayi ta kalle shi suna had'a ido ta kawar da kanta a hankali, amsa sallamar sa tayi had'e da fad'in "Ina kwana"
Ya amsa da "Lafiya how was your night?"
Tace "Alhamdulillah" had'e mikewa,sallayan ta nad'e kana ta Shiga ban d'aki, Jin saukar ruwa a shower ne yasa ya fice daga d'akin,Bayan ta gama ne ta leko taga baya d'akin fita tayi cikin sauri ta nufi kofar ta sa key.Gaban Mirror ta nufa ta zauna,kallon kanta tayi a mirror ko me ta tuna Naga ta girgiza kai had'e da Yar karamar dariya mai d'an sauti,Mai ta Shiga shafawa a jikin ta Bayan ta gama ne ta ciro kayan da zata sa, Riga da skirt d'in atamfa ta sanya a jikin ta, ba tayi wani kwalliya ba powder ta shafa sai kwallin da ta saka a idon ta sai lip glow.
Fita tayi daga d'akin, parlor ta nufa kallon d'akin ta tsaya yi tana ganin kokarin iyayen nata had'e da sa musu Albarka, komai na d'akin Royal Blue ne da Sky blue ya haska d'akin sosai ga wani uban kamshi da d'akin keyi.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin maida kallon gun, a hankali take ta fiya har ta Isa kofar da take jin karar,a hankali ta Turo kofar had'e da kusa kanta ciki, kallon kitchen d'in ta tsaya yi tana Murmushi,ta shagala da kallon kitchen d'in har ta manta dalilin da yasa ta Shigo.
Ido hud'u sukayi,kallon kallon suka Shiga yi wa juna,wani irin kallon yake binta dashi ganin yanda tayi matukar kyau Duk da ba wani cika take dashi sosai ba kayan yabi jikin ta,kamar a jikinta aka d'inka shi.
Ganin kallon da yake mata yayi yawane yasa tayi sauri juyawa da niyar fita cikin Murya mai sanyi yace "Isha!!!
A hankali ta juya tana kallon sa murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau" Murmushi itama tayi had'e da fad'in "Thanks" ta juya zata fita yace "Hold on mana" ajiye spoon d'in dake hannun sa yayi ya nufe inda take hannun ta ya riko ya jaa ta izuwa gun gas cooker da yake girki da ita.
Marfin tukunyar ya bud'e yace "Look Waifa gwanin ta zan miki Kuma sai naga baiyi yanda nake gani idan Mama tayi ba"
Isha kusa dariya ta Shiga yi Tace " Me ne wannan d'in?"
"Bakya gani Irish potatoes ne"
"Eh na gani ina nufin me kake son girkawa?"
"Chips Mana ai tunda kwanaki ka ka fad'a min kina son chips sosai sai na kudiri aniyar yi miki shi da kaina"
Dariya take yi sosai shi Kuma ya rungume hannun sa yana kallon ta cikin Muryar dariya Tace "chips fa kace" ya ama da "Eh Mana"Dariya ta kumayi Tace "ba dai chips ba sai dai pourage" yace "Pourage Kuma gwate kenan fa?"
"eh Mana ina ka tab'a ganin chips haka,ai da ka dage ka koya Kan irin ranar Nan tazo"" Uhmn Gaskiyar ki,ai ni yanzu ma gani nake kamar mafarki nake" Jin abinda yace ne yasa ta daina dariya kamar anyi ruwa an d'auke Tace "Ban gane kamar mafarki ba?"
"Umm na d'auka bazan tab'a samun ki ba Isha" Murmushi tayi Tace "Kasan mene ne?"
Yace "A a sai kin fad'a"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali