'''Continuation........''' Su Ma'isha na Isa asibitin fita tayi ba tare da ta kashe motar ba, gudu take sosai har ta isa ICU Dr Ali ta gani yana kaiwa yana kawo wa murya na rawa Tace "Dr Ali ina yake? Yana ciki ne?"
Kan ya Bata amsa da sauri ta kusa kanta cikin d'aki Meerah, Ayrah da Mardiya Suma suna kokarin Shiga ciki yayi saurin d'aga musu hannu had'e da fad'in "A a please ku jira ta anan" sai yabi Bayan Isha.
Isha inda ake Canza Kaya ta nufa ta cire takalmin ta,ta sanya Wanda ake Shiga cikin ICU dashi, da sauri tayie inda Haisam yake, ganin Haisam tayi yana rarraba idanu yana son gane inda yake Isha tsuman tsaye tayi tana kallon sa, suna had'a Ido dashi ta masa Murmushi shima Murmushin ya mata sannan ya rufe idanun sa.
A dai dai Nan Dr Ali ya Isa inda suke fuskar Haisam ya kalla cikin kid'ima ya nufi kansa duba nakurar da ke Kan Haisam ya Shiga yi ajiyar zuciya yayi ya fita, Isha ma tabi Bayan sa.
Sai da suka fita waje tace "Dr ya naga Kuma ya rufe idon sa?"
Ya amsa da "I don't know isha, ban San ya akayi hakan ya Faru ba, baifi mintuna 30 da farkawa ba fa, ina ganin ya farka na Kira ki"Dafe kanta tayi Tace "This is not what I asked you Dr meyasa ya rufe idanun sa?"
Kallon ta yayi kana yace "I don't know and I just told you that, look Isha hakan na faruwa dama Kinga Kenan akwai alamun ya kusa ya Dawo"
Cikin murya Mai d'an kara tace
" What? Kana nufin ya sake Shiga comma ne?"
Kai ya d'aga Mata alamun eh.Jiki a Sanyaye ta zauna a kasa hawaye d'aya na bin d'aya daga nesa suka hango su da sauri suka karasa gun, Meerah ce take kokarin d'aga ta Amma ta kasa hakan ne yasa Ayrah tayi saurin riko ta, Ma'isha da dukkanin karfinta ta ture ta har sai da ta Fadi a kasa
cikin zafin nama Ma'isha ta Mike cikin tsawa tace "How dare you Ayrah? Who gave you the audacity to touch me?"Meerah baki a bud'e take kallon Isha don Bata tab'a ganin 'bacin ran Isha har haka ba, cikin sanyin Murya Meerah Tace "Isha calm down please,muna asibiti ne fa ki duba kiga kin sa ana ta kallon mu"
"A kalla Mana I don't care,gara su kalle mu su san cewa akwai Mutane mugaye azzalumai kamar Ayrah a dalilin ta na rasa d'an uwana kuma masoyina ta rabani dashi,Kuma kice min I should calm down?" ta karasa maganar cikin kuka.
Meerah Tace "Na sani Isha Amma kiyi hakuri Insha Allah, Allah zai bashi Lafiya,but ba Kince ya farka ba?"
"Eh ya farka don har na kalli cikin idanun sa Amma ya sake rufe idanun sa,Ayrah bazan tab'a yafe miki ba Idan wani abu ya sami Ya Haisam"
Ayrah da tun d'azu take durkushe a kasa ta Mike had'e da kakkab'e Kuran da ke jikin ta tace "To hell with You Isha,so what Idan baki yafe min ba? Did I asked for your Forgiveness? Haisam d'an uwana ne jinin da ke yawo a jikin sa shi yake yawo a jikina,na fiki son sa"
Dariya Isha ta Shiga yi sosai harda rike ciki Amma fa hakan baisa ta daina zubar da kwalla ba sai da tayi mai isarta kana Tace "Su d'an uwa manya,so tell me Soyayyar da kike masa ne yasa Kika Masa hakan? A dalilin ki ya Shiga wannan halin shima Duk Soyayyar ce?"
"Ai ba'a..........." Da sauri mardiya Tace "Please ya Isa Haka,Ni Banga amfanin chachan bakin da kuke ba Kar ku manta fa a asibiti Muke Kuma akwai marasa Lafiya moreover a bakin ICU Muke kunsan ba a son surutu Dan Allah ku yayyafa wa zuciyar ku ruwan sanyi please"
Dr Ali yace "Finally" ya maida kallon sa ga Isha yace "Kamar yadda nace miki ya kusa farkawa inshallah zai farka......." Maida kallon sa yayi ga Meerah yace "Please ki maida ta gida"
Riko hannun isha kawai tayi suka bar wajen ba tare da ta ce Masa komai,ba girgiza kai yayi had'e da fad'in "Allah shi kyauta." Ya bar wajen.
Mardiya na ganin yayi d'an nesa da su ta finciko Ayrah magana kamar rad'a Tace "Wai meyasa ke Sam baki da hankali ne"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali