Da gudu suka shigo d'akin suna fad'in "Umma kin ganta ko, mun fad'a miki bata tafi ba" Aymana da Aima ke Wannan maganar.
Umma dake biye dasu Yar karamar dariya tayi had'e da fad'in "Eh lallai Kun fini Gaskiya" kallon inda Isha ta ke tayi Tace "Daughter Kince min Zaku fita Ashe Kuna Nan?"
"Eh wallahi Umma, munzo fita ne muka had'u da Mardiya da Ayrah"
Umma jin ta ambaci sunan Ayrah hakan yasa tayi saurin kallon inda suke, tana ganin fuskar Ayrah ta gane fuskar ta sabida tana Kama sosai da mahaifiyar ta.Jiki na rawa suka durkusa har kasa a tare suka ce "Ina wuni?" A d'an yasine ta amsa da "Lafiya" riko hannun Aima da Aymana tayi suka fice daga d'akin, jiki a Sanyaye suka koma ma zaunin su, Meerah dad'i taji wani irin Murmushi tayi Mai d'an sauti.
Isha Tace "As I was saying zan auri Yayan kine on one condition, and the condition is zamuje inda kuka binne Wannan layan ku kona shi da hannun ku"
Ayrah zaro ido tayi tana kallon Isha Tace "Amm.... Amma ai... " Sai Kuma ta kasa karasa maganar da take son yi Isha Tace "Amma me"
Cikin Murya Mai sanyin Tace "Babu komai"
A zuciyar ta Kuma Tace "Ya Rabbi ya zanyi zasu ruguza min shiri gashi yanzu ina son Haisam sosai" muryar Meerah taji tana fad'in "Kunyi Shiru? Bazaiyu bane?"Mardiya Tace "Me zai Hana yanzu ma sai muje in Kun shirya"
Mikewa Meerah tayi had'e da fad'in "Good Sai ku tashi muje bari na Shiga kitchen nasha ruwa" sai ta fice.Isha, Ayrah da Mardiya fita sukayi suka tsaya a katafaren compound na gidan suna jiran fitowar Meerah , fitowa tayi hannun ta d'auke da jakar ta tana wasa dashi ta karaso inda suke Tace "Muje ko?"
Tafiya suke ganin Su mardiya da Ayrah sun nufi motar su cikin Muryar fad'a Tace "Excuse me ina Kuma zaku? Wai Kuna nufin motar ku zamu shiga Bazaiyu ba"
Ayrah Tace "Uhmn to kin San inda aka binne abin ne? Idan kin sani to bismillah mu shiga motar taku"
Kawar da kanta kawai tayi Isha Tace "Meerah you know they are right let's use their car"
Meerah Tace "Oh stop it please Duk abinda sukace sai kice they are right? Ai mu ba baki bane a garin ko? Gombe fa garin mune anan aka Haife mu so zamu sani"Mardiya Tace "zaiyi wuya kusan gun gaskiya Amma babu komai mu yi amfani da motar taku sai na Rika nuna muka hanya"
Isha Tace "A'a ai wannan wahalane goma da ashirin muje kawai" jaan hannun Meerah tayi tana bata hakuri dakyar ta shiga motar, Meerah da Isha a baya suka zauna Mardiya ke jaan motar sai Ayrah a kujerar Mai zaman banza, fice wa sukayi daga gidan suka kama hanya.
Tafiya suke Babu Wanda ke magana da d'an uwan sa, Meerah ganin tafiyar taki karewa Tace "Irin Wannan tafiya haka kamar zamu bar gari are we safe?"
Murmushi Mardiya tayi kana Tace "Of course you're safe, kusa da makabarta ne"
Zaro Ido Isha da Meerah sukayi a tare suka ce "Makabarta dai?"
Ayrah Tace "Eh Makabarta" shiru sukayi basu ce komai ba, ko wacce da abinda take tsakawa a ranta, a Haka har suka Isa gun.A bakin hanya sukayi parking motar su, kana suka Fara Shiga wani daji sun d'auki tsawon mintuna 20 suna tafiya mardiya ce Tace "Mun iso ganan gun" tana nuna gun da d'an yatsan ta.
Meerah Tace "kin tabbata Nan ne?"
"Eh Nan ne"
Isha Tace "But ya akayi Kika gane gun shekara kusan bakwai Kenan fa ko?"
Ayrah tace "da wannan bishiyar muka gane shiyasa muka binne a karkashin bishiyar"
Isha girgiza kai tayi alamun ta fahimta had'e da fad'in "Oh."Ayrah Tace "To yanzu ya zamuyi mu tona Ni shaf na manta ma da Mun d'auko ko da wuka ne"
Meerah Tace "Worry Not na d'auko" had'e da zaro wuka a Jakarta ta mikawa Ayrah, Ayrah hannu tasa ta karb'i wukan tana juyashi tab'a Kara kallon wukan tace "Mardiya gashi ki tone"
Tana Mika mata wukan, banka Mata harara tayi Tace "Kila kin manta ko,kece Kika binne Kuma kece zaki tona shi bani ba"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali