Haisam duk a kage yake a tashi sabida shi Sam bai fahimci Ma'sha ba, bayan an tashe su ne ya shiga neman ta, ai kuwa yana hangota da gudun sa ya nufi inda take Tana ganin sa tayi Murmushi, ya "Ma'isha wai me ke faruwane?"
Cikin muryar dariya Tace "Ga Nan driver yazo" shiga tayi ya tsaya Yana kallon ta, ganin baida niyar shiga Tace " Haisam come in Mana"
Ba musu ya shiga.Bayan ya gaida driver ya Maida kallon sa gare ta, yace "Ma'isha please tell me Mana"
Dafe kanta tayi Tace "Ya Salam, Haisam Dan Allah ka kyaleni Idan muka je gidan zaka ga koma mene ne."Gyara Zama yayi yace "Tell me something Ma'isha"
"Uhhmnn ina jinka"
"idan Kika fada min mutuwa zakiyi ne kome?"
"A a ko 'daya baza ka mutu ba"
" So tell me"
" No I won't."Cikin muryar dariya driver yace "Haisam ga naci, Ma'isha Kuma taurin kai to duk kuyi hakuri in muka koma gidan zakaji Kan zancen"
"Hakan na nufin kaima kasan abinda ke Faruwa kenan ko?"
"A a ba abinda na sani nikam"Girgiza kai yayi babu Wanda ya furta komai har suka Isa, Kai tsaye parlor suka nufa, Haisam duk ya kasa sakin jikin sa, ganin Umman sa a zaune a gun yasa mamaki ya rufe shi.
Cike da mamaki yace "Umma kina kema Nan aka kawo ki?"
Murmushi tayi, Mummy tace "Eh Nan aka kawota"
Tsosa keya yayi ya durkusa ya gaida su,Daddy dake zaune yayi Murmushi ya amsa ba yabo ba fallasa.Yace "Tashi ka zauna akan kujera"
Kai ka sa yace "A a Alhaji Nan ma yayi"
Murmushi yayi yace "Haisam wannan umarni ne, ba shawara ba ne ba."Tashi yayi ya zauna gyaran murya yayi yace "Haisam naji tarihin ka, mahaifiyar ka Bata boye Mana komai ba hakika na tausaya muku, sannan na nemi ganin kune sabida ina so ku dawo Nan da Zama,sannan zan dauki nauyin karatun ka daga yanzu har Allah yasa ka gama"
'daga kansa yayi da sauri ya kalli Daddy sannan ya Maida kallon sa ga Umma, 'daga Masa Kai tayi alamun eh, a zuciyar sa yace "Wato Umma ta ta San da zancen"
Gyaran murya Daddy yayi ya daura da fad'in "Nayi maka alkwarin zan dauke ka a matsayin d'an da na Haifa da ciki na, sannan kofa Bud'e take duk Sanda kake neman wani Abu kar kaji tsoro ko shakkar tinkarata ko Maryam"
" Nagode Alhaji Allah ya saka, ya biya ka da gidan aljanna"
" Umm Haisam, daga yanzu bana so na sake ji ka kirani da alhaji, ka Kirani da Daddy kamar yadda Ma'isha take kirana kaga Kenan Ma'isha ta samu wa"" To Alhaji, auu daddy nagode"
Duk sukayi dariya, Maida kallon sa yayi ga Ma'isha yace "Daughter kuje kuci abinci, don zamu fita da Haisam din"Mikewa tayi Tace "Ya Haisam Tashi muje ko?"
Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayanta, Umma tace "Alhaji, hajiya nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ban San wani irin godiya zan Muku ba"Mummy Tace "haba ke kuwa tun dazu fa kike ta godiyar nan, ya Isa haka, mu Dan Allah mukayi ba don komai ba, sannan mun lura akwai shakuwa a tsakanin yaran Nan Baki ga yanda ta tada Mana hankali ba nikaina mamaki ne ya kamani"
"Ikon Allah, Amma ni Haisam bai tab'a min maganar ta ba ko da da wasa ne"
"Ai bazaiyi ba don na lura Haisam na da zurfin ciki"Murmushi tayi tace "haka yake kamar ubansa"
Alhaji dake Danna wayar sa, jin ta ambaci uban sa, yace "Yauwa please a ina baffan Nan nasa yake?""Ya Nan cikin garin Nan"
" Kina nufin cikin garin Gombe?"
"Eh"
" Abun zaizo Mana da sauki insha Allah"
Mummy da Umma a tare sukace
" Allahu yasa"
Ya amsa da amin ya daura da fad'in "Maryam ku samu kuje shopping din Nan kar dare yayi, sannan please kar su d'auko komai a chan, za a Saya musu duk abubuwan da suke bukata, sannan idan kudin Bai Isa ba ki Kirani"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali