WASHE GARI
Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam.Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?"
Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa.
Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta.
Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday ne Babu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti"
"Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje."
Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta.
Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka?"
"Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta"
Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma"
"Eh Mummy""Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka"
Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa.
Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali