Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?"
"Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta." Ta shige cikin gida.Basu zarce ko Ina ba Sai police station,bayan sun shiga ciki Kai tsaye office din DPO suka shiga bakin su d'auke da sallama,ga mamakin su suka tarar da Baffan Haisam a zaune a cikin office d'in,DPO ya nuna was daddy kujerar dake gaban sa yace "bismillah yallab'ai"
Ba musu ya nemi wuri ya zauna,bayan sun gaisa DPO yace "Nasan kayi mamakin Kiran ka da nayie ko?"
Ya amsa da "Eh sosai ma"
Gyaran murya DPO yayi yace "Dama malam Hassan ne ya bakaci ganin ka shiyasa ma na Kira ka"Daddy maida kallon sa yayi ga Malam Hassan yace "Ina sauraron ka"
Malam Hassan yace "Na yanke shawara ne zan maida musu da dukiyar su" a gadarance.Girgiza Kai kawai daddy yayi yace "Ni Kuma ban amince da hakan ba, a lokacin da nake ta bibiyar ka da ka dawo da duk abinda ka San nasu ne Amma kamin kunnen uwar shegu, maganar kotu Kuma bazan janye ba Sai munje"
Malam Hassan yace "A lokacin da kace na bayar banji zan iya bane ba Amma a yanzu na shirya" Daddy ransa yayi mugun 'baci sabida ganin yanda malam Hassan yake magana a gadarance, mikewa yayi yace "Haisam tashi mu wuce gida" ya nufi kofar fita, DPO yace "Yallab'ai Dan Allah ka tsaya" waigowa yayi yace "Na tsaya nayi me da na San sabida Shirmen Nan ka kirani wallahi da banzo ba"
"Hakane yallab'ai dole ranka ya 'baci Nima cemin yayi zakuyi Sulhu shiyasa na Kira ka" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Malam Hassan ba haka mukayi dakai ba, Ce min kayi zaka nemi gafarar su kuyi Sulhu Amma ya za'ayi Kai da kake Neman Abu daga gare su kana musu magana a gadarance? Ka bashi hakuri ka fahimci juna don wallahi idan ka bari kuka shiga kotu da dukiyar d'an uwan ka da naka duk za a had'a a karb'a, Amma fa ba tilasta maka nake ba shawarace idan kaso ka d'auka"
Malam Hassan Jin za'a raba shi da komai da komai ya Fara wiiki wiki da ido Nan take zufa ya Fara keto Masa duk da AC dake cikin office d'in, Chan ciki yace "Alhaji kayi hakuri Dan Allah" ya maida kallon sa ga Haisam yace yace "Dan Allah kasa baki Haisam"
Haisam dake tsaye Yana kallon su yace "Daddy mu saurare shi a gama abin Nan once and for all ko ba komai hankalin Umma zai kwanta"
Ajiyar zuciya daddy yayi ya koma ya zauna yace " Shikenan DPO wani formalities za a bi don a tabbatar da zai bada komai da komai don wallahi I don't trust him ko kad'an"
"Kar ka damu yallab'ai zan kula da komai, Na maka alkawari Nan da 2 days zan kammala komai,amma zamu ciga ba da ajiye anan d'in ne ko Kuma mu sake shi?"
" A a no need ai Ku sake shi" ya maida kallon ga Malam Hassan dake zaune a kasa ya nuna sa da manuniya yace "Mind you if try acting smart with me I'll deal with you and make your life miserable" Yana Kai Nan ya fice Haisam ya bi bayan sa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa gida.
Horn Haisam yayi Mai gadi yayi saurin bud'e musu kofa, parking lot ya nufa yayi parking motar, Mummy , Umma da Ma'isha na zaune a garden d'in gidan suna jiran dawowar su, daddy d'akin sa ya wuce abinsa suna mishi sannu da zuwa ko kallon su beyi ba bare ya amsa.
Haisam kuwa inda suke ya nufa ya nemi wuri ya zaunan, Mummy Tace "Son lafiya me ya Faru ne haka na ga ran Alhaji a 'bace?" Gyara Zama Haisam yayi ya fara jero musu yanda sukayi a police station, tunda ya fara magana suke kallon sa har ya Gama Babu Wanda yace komai, Mummy girgiza kai tayi ta tashi ta shige cikin gida, d'akin Daddy ta shiga taje tana ta aikin rarrashi.
Ma'isha ganin Umma ta shiga cikin damuwa Ta d'an dafe kafad'arta tace "Umma wannan ba abin damuwa bane ba, tunda shi da kansa yayi ra'ayin zai dawo da dukiyoyin ai farin ciki ya kamata muyi, matsalar kawai gani nake bazai dawo dasu duka bane"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali