'''Continuation.......''' cike da mamaki suke kallon sa, murya chan ciko Isha Tace "Yaushe ka Dawo?"
'dago kansa yayi ya Kuma maida kansa Kan wayar sa kana yace "Yanzun Nan shigowa na"
Meerah cikin tsigar tsokana Tace "Ango Ango kasha kamshi"
Yar karamar dariya yayi yace "Meerah manyan gari ashe kina Nan gaba ki d'aya kin kimu""Aaaaahhh wane ni kawai dai na baku lokacine kuci amarcin ku da kyau, Amma har sai kun gaji dani"
" Baza mu gaji ba gaskiya, so ya aikin dai?"
"Alhamdulillah, Amma ba Dad'i Wallahi aminiyata bata Nan so wurin ya Zama min so boring,ya Kamata ka bar min ita haka ta Dawo bakin aiki"Murmushi yayi yace "Zata Dawo ai da zaharan hutun ta ya kare"
"To Shikenan, Allah ya nuna Mana"
Ya amsa da amiin, Tace "Sai anjima"
Ya amsa da "A gaida gida"
" Gida zaiji"Tayi gaba Isha Tace "Bari na rakata"
Yace "Alright"Har wurin mota ta rakata, sai da taga fitar ta kana ta Shigo cikin gida, ta iske shi Yana zaune a inda ya bar shi, Zama tayi yace "Ba Zama zakiyi ba ki d'auki mayafin ki, zamu fita" magana yake ba tare da ya kalli inda take ba
Tace "Ina zamu?"
'dago kai yayi kalle ta kana yace "Sayar da ke zanyi" sai ya ki cigaba da danna wayan sa.Tab'e baki tayi ta mike ta shige ciki, bata d'auki lokaci mao tsawo ba ta dawo jikinta sanye yake da hijab, d'ago kansa yayi ya kalle ta, Murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau "
Murmushi tayi Tace "Thanks"
Mikewa yayi yace "Mu tafi ko?" Yayi gaba bai tsaya jin abinda zata ce ba, kallon sa tayi ta girgiza kai kana ta bi Bayan sa.Motar sa ya Shiga baka sidik Mercedes Benz sai sheko take, ganin ta nufo shi ne yayi saurin fita ya zaga ya bud'e mata kofar motar ta Shiga, ya maida ya rufe zagayawa ya kuma yi kana ya Shiga, Yana Shiga bai Tsaya 'bata lokaci ba ya sa wa motar key, tun Kan ya Isa yayi wa Mai gadi horn, da sauri ya wangale kofan Yana musu a Dawo Lafiya, suka fice daga gidan.
Kallon ta yayi kana ya maida Kan sa Akan tukin da yake, yace "Isha" cikin wani irin low voice , kallon sa tayi had'e da fad'in "Na'am"
"Kina so na kuwa?"
"Uhmn Haba Ya ma'aruf wanann wace irin tambaya ce?"
"Don't feel bad kawai akwai abinda nake so na fahimta ne"
"Uhmnn ina sonka Mana , idan bana son ka me zai sa na aure ka?"
Wani dogon ajiyar zuciya yayi bai ce mata komai ba ya cigaba da tukin sa itama ganin bai da niyar magana tayi shiru abin ta.Ganin sun doshi hanyar FTH ne hakan yasa Tace "Kar dai yaji maganar da muke d'azu da meerah?" A zuciyar ta take ayyana hakan.
A bayyane kuma Tace "Me Kuma zamuyi a anan?"
"Gani nayi kin kwana biyu baki ga Yayan ki ba"
Kallon sa kawai tayi tana mamakin Hali irin na Ma'aruf "shi ko irin kishin Nan baya yi Kuma yasan irin soyyayar da nake yi wa Haisam?"Muryar sa taji yana Fad'in "Nasan zakiyi tunaniin ko bana sonki ko Kuma bana kishin ki, Isha Ina son ki Kuma ina kaunar ka babban burina shine na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali, n aure kine a ganina zan iya Zama wani 'bangaren rayuwar ki Amma Naga alaman hakan bazaiyu ba"
A dai dai Nan suka Shiga cikin asibitin sai da yayi parking kana ya kwantar da kansa a Kan kujera yace
"Isha" d'ago Kai tayi ta kalle sa kana yace "ko yau d'in nan Haisam ya farka in dai zai karb'i soyyayar ki sannan ya soki kamar yadda kike son sa a shirye nake da na sake ki"
zaro Ido tayi tana kallon sa, hannun yasa ya share mata hawayen da ya ke gangarowa daga fuskan ta Wanda ita kanta bata San sun zubo ba kirkirerren murya yayi "Isha I can sacrifice anything for you in this world har da ni kaina"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali