"daddy wai me Mutanen Nan suke fad'a ne? Wa aka kashe?" Ayrah keyi wa Daddyn ta da yake tuki tayi wa wannan tambayar, cikin inda inda yace "Don't mind them please,shirme ce da irin sharrin su da suka Saba"
"To Shikenan, Amma daddy har naji tausayin sa Wallahi, Ya haisam na da kirkii Sosai"
Taka birki yace "Tausayin..... Tausayi Kika ce"
Ganin yanda ya ke zaro Mata Ido kana Yana maganar cikin fad'a ya tsorata tata Sosai.Murya na rawa Tace "Am sorry"
Tsaki yayi yace "You better be, Banda wawiya irib rashin mutuncin da ya min baki ji tausayi na ba sai Tausayin sa? Kuma kul na sake jin kin ambaci sunan sa sai na sab'a miki shasha kawai"A dai dai Nan suka Isa gida zata fita yace "Dawo Nan" Dawo wa tayi ta zauna bata ce Masa komai ba, ganin bai yi magana ba Tace "Daddy gani"
"Mtsss ai na zaci Zama zakiyi kina Kallo na tunda na Zama sa'an ki, kina jina?"
Ta amsa da "Eh daddy"
"Good, Kar ki kuskura naji kin fad'awa maman ki maganar Nan"
"Toh"
"Wuce ki fita min a mota."Tur baki tayi kana ta fita, likowa yayi yace "Ni kike turawa baki ina zan Shigo gidan na same ki Sai na ci mutuncin ki"
Da guda ta shige gida, shi Kuma ya fita daga gidan.Bayan farfad'owar Abba da umma, Tunda mummy ta fad'a mata cewar Haisam ya Shiga comma ta bud'e sabon babin kuka Daddy kuwa yayi ta fad'a Yana fad'in "Ai dama sai da na Hana ki fad'a mata Amma kinki ji, yanzu ki ga halin da Kika sata a ciki"
Abba yace "haba Yaya ya Isa haka Mana tun d'azu kake ta fad'a Kuma, ai dama Dole ta sani ko idan bata sani ba Dole gaba zata sani so ni Banga abun tashin hankali anan ba"
Shiru kawai yayi bai ce Masa komai ba, Ma'isha na farfad'owa Meerah ta gani a gefen ta, da taimakon Meera Isha ta zauna abinci ta bata da ruwa da kyar ta karb'i spoon 3 ta Sha ruwa, ta tashi zata fita, Meerah ce ta rike ta had'e da fad'in "Ina Kuma zaki?"
"Gun Ya Haisam"
"Amma......"
Dakatar da ita tayi da fad'in "Yanzun ma hanani ganin sa zakuyi? Bayan d'azu maganin bacci kuka bani?"Sake ta tayi kana Tace " ya akayi Kika sani?"
"uhmn Kar ki manta fa Ni pharmacists ce nasan drugs" tana Kai nan ta fice d'akin da Haisam yake ta nufa taga wayam.Da sauri ta fito ta hango Bayan Meera Kiran sunan ta tayi ta tsaya, su Daddy najin Muryar ta Duk suka fito , da sauri ta Karasa inda take Tace "Ya ban ganshi ba?"
"To ta ya za'a yi ki ganshi ce miki akayi ya shiga comma to where do you expect za a Kai shi pharmacists?"
"Oh so that's mean yana ICU"
Hannu ta d'aga mata alamu oho, ta juya tayi tafiyar ta tana ganin su Umma ta nufi inda suke, dukannin su Sannu suke Mata ta amsa.Abba ne yace "Ya kamata mu koma gida ko tunda duk Mun farka"
Umma Tace "A bar Haisam d'in dawa?"
Ma'isha Tace "Umma Kar ki damu ina Nan, Kuma baza a bari a Rika Shiga kansa ba , kin san ba'a son motsi ko kad'an a ciki""Hakan na nufin bazan sake ganin sa ba ko?" Ta karasa maganar tana matsar kwalla, Ma'isha rungumar Umma tayi Tace "Please Umma ki rage kukan Nan haka Kinga nima na daina ko muyi ta Masa magana, Kuma Insha Allah zan nemi hanyar da Zaki Rika ganin sa lokaci zuwa lokaci, Kuma fatan mu shine Kar ya d'auki tsawon lokaci a ciki"
Mummy Tace "Allah yasa hakan ne don nifa Sam ban yarda da likitocin Nan ba, a Haka sukayi wa wata makwanbciyar mu ba Ashe kashe ta sukayi ance fa yawanci likitocin Nan mayu ne"
Ma'isha tayi saurin fad'in "Laaah mummy Kenan Nima mayya ce ko?"
Duk sukayi dariya a Haka suna Hira har suka fita, Umma da Abba suka Fara ajiyewa a gida kana su daddy suka wuce gida."Qawata ya akayi haka? Meyasa zakiyi wa Haisam haka? Dama ba son shi kike da Gaske ba?"
Mardiya ke yiwa Ayrah wannan tambayar, mikewa Ayrah tayi Tace "Na fad'a miki kwanaki a kwai wani buri nawa Wanda nake so na cika, Wanda Wannan burin nawa burin mahaifinane, Wanda na cika Masa burin sa Amma na rasa dalilin da yasa bana farin ciki da hakan"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali