Tafiya take kanta a kasa, hannun ta rike yake da Yar karamar jaka Wanda bazai wuce handout biyu bane aciki, a hankali take tafiya hankalin ta kwance har ta Isa inda suke sallama tayi had'e da jaan kujerar dake gefen Haisam ta zauna.Murmushi Haisam yayi yace "Barka da zuwa the only princess in Haisam Palace"
"Uhmn Yaya Kenan princess kawai ashe da saura na"
"Wa ya gaya miki? Ke Kanki kin San ke ta dabance"Murmushi tayi sai Yanzu ta maida kallon ta ga su Aysha dake aikin kallon ta Murmushi tayi Tace "Sannun ku fa"
Mardiya ce ta amsa da "yauwa"
Ganin Aysha tayi nisa a tunani ta d'an tab'a ta, a d'an razane Tace "Yauwa sannu ya kike"
"Lafiya Lau"
Haisam yace "Princess meet Aysha and Aysha this is My princess bani da tamkar ta a Rayuwa"
Kirkirerren Murmushi Aysha tayi Tace "Nice To meet you, to Amma ita d'in bata da suna ne?Haisam Yar karamar dariya yayi yace "Tana dashi Mana kawai dai sunan ne yayi min nauyi bana iya Kiran sa sai on special occasions"
Aysha zaro Ido tayi sannan Kuma ta tab'e baki had'e da girgiza Kai Tace "oh lallai"Yace "Sai dai idan ita zata fad'a miki da bakin ta"
Aysha Tace "Ya sunan ki?"
"Ma'isha"kawai Tace a takaice."Suna Mai dad'i"
" Thank you"
Ma'isha ta maida kallon ta ga Farukh da aikin cin abincin sa kawai yake, Ma'isha dariya tayi Tace "Haba Ya Farukh duk don Kar naci ne kake ta sauri ko?"
Sai da yasa hannu ya kurb'i ruwa kana yace "Na Isa Ma'isha kawai dai naga baku da niyar gama surutun nakune kin San ance kowa da damuwar sa Ni abincin ne damuwa ta"Haisam yace "Zaka ji da shi ai"
Cikin sanyin Murya Tace "Yaya My promise yunwa nake ji"
"Me Zaki ci?"
"Ka zab'a min komai ma nikam"
"To kin San Ni abinci na d'ayane idan Zaki ci sai a kawo miki"
"Ai Yaya tun bana son chips ka sa na Fara son shi"
Murmushi yayi yace "Barka na kinnga ko ba komai Zaki Rika yi Mana a gida"
Murmushi kawai tayi Nan da Nan yasa aka kawo Mata ta hau ci, har ya karb'i spoon d'in ya Fara Bata baki.Aysha kamar zata had'iyi ranta ta Rasa abinda yake Mata dad'i tsinta kanta tayi da mikewa ta bar wurin ba tare da Tace komai ba, mardiya ma ta bi bayan ta.
Haisam kuwa bai ma San sun tafi ba , Yana Nan Yana feeding princess d'insa Saida taci ta koshi ya lura ba su Nan, kallon Farukh yayi dake Kallo a wayar sa yace "Haa'ah yaushe Kuma suka tafi?"
"To ka Zama Romeo ina zaka ji tafiyar su? Duk da ma na ga Kamar sauri suke don Nima ba kulani sukayi ba suka tafi"
Tab'e baki yayi ya d'aga kafad'ar sa irin halin ko in kula d'in Nan ya maida kallon sa ga Ma'isha yace "Karfe nawa zaki gama lectures d'in?"
"Karfe 4"
"Ni Kuma sai 6 ya zamuyi Kenan? Zaki jirani ko Zaki koma da napep don bazan barki Kiri driving ba"
d'an turo baki tayi Tace "sabida me Yaya?""Umarnin daddy ne, akan Kar na barki kiyi driving sai kin Kara girma"
"Yanzun wai ni yarinya ce?"
"Eh Mana sosai ma Amma..... "
Farukh ne ya dakatar dashi da fad'in "Malam kana da niyar Shiga lectures d'in Nan kuwa ko kuma na tafi na Barka da kanwar ka ku gama surutu?""A a tashi muje, princess ki jirani kinji?"
Kai ta d'aga Masa alamun to basu fita ba sai da ya biya su kud'in su, a tare suka fita ta nufi Lt din da zata yi lectures Suma suka nufi nasu.'Bangaren Su Aysha
Aysha Rai a 'bace ta nufi garden d'in cikin makaranta inda d'alibai sukan zauna su Sha iska, wasu suna karatu wasu Kuma hirar su suke Maza da mata.Zama tayi ta dafe kanta da hannun bibbiyu, ji take kanta ba tsarawa Kamar zai rabj gida biyu, mardiya ce ta zauna a gefen ta tana kallon ta ba tare da tace Mata kala ba.
Aysha ta d'ago kanta ta kalli mardiya kana ta maida kanta kasa cikin Muryar kuka Tace "Mardiya I need your help ki taimaka min wallahi Ina son gayen Nan har cikin Raina Dan Allah give me advice"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali