29&30

121 5 0
                                    

Hannun ta ta sauke daga kirjin ta, ta sauke ajiyar zuciya Tace "Kai Yaya ka tsoratani yaushe ka Shigo?"

Tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake yana kallon cikin idonta tabbas ta tsoro ta, yace Mata "Yanzu na Shigo, Ashe dama kin ganni?"

Kawar da kanta tayi kamar bata ji abinda yace ta hard'e hannun ta, ba ganin bata da niyar bashi amsa ya taso ya nufe ta, dab da ita ya tsaya ganin har yanzu bata kula shi ba ya hannu ya riko hannayen ta, wani abu taji yarrrr tun daga tsakiyar kanta I'xuwa tsakiyar kafan ta, da sauri ta zare hannun ta.

Murmushi yayi yace "Princess wai haryanzu fushi kike dani?"
'dan ja da baya tayi ganin haka Shima ya matsa kusa da ita ta Kuma yin taku biyu ta baya shi Kuma yayi Taku biyu ya iso ta haka sukayi tayi har ta Kai jikin bango, hannu yasa ya riko hab'arta ya juyo kanta ta kalle shi.

Idonta cikin nasa, idanun ta sun taro ruwa kiris suke jira su zubo ganin hakan yaji duk ba dad'i kasa da murya yayi yace "I Know I hurt you, Dan Allah ya Isa Haka bana jin dad'in hakan duk kin Canza min kamar ba princess d'ina ba"
Hawayen da dama jira suke suka fara bin juna suna sauka da sauri yasa hannu yasa ya fara share mata yana girgiza kansa, ya kuma cewa "Am sorry My princess"

Ma'isha runtse idanun ta tayi tana Jin dad'in sunan My princess wani 'bagaren Kuma ji take kamar zuciyar ta zata fashe sabida gani take kalmominsa na yaudara ce kawai.

Haisam ganin hawayen Ma'isha ba karamin tada masa hankali yake ba ji yake kamar yasa harshen sa ya lashe hawayen ta yana Kuma ji kamar ya rungumeta a jikin sa ko zata ji saukin abinda take , amma bazai iya hakan ba sabida tun ba halaliyar sa bace.

Riko hannun ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado, ya durkusa a gaban ta hannun ta d'aya ya rike yasa hannun ta a tsakiyan hanyen sa, murza hannun nata yake a hankali yana kallon ta, banda hawayen dake zubiwa daga idanun ta Babu abinda take yi, har sai da ya ga ta daina kukan ya sake hannun nata sannan ya mike ya zauna a gefen ta.

Still yana kallon ta yace "Please ki daina kukan haka bana son ganin ki haka, sannan dama na kawo miki labari ne Mai dad'i Amma na fasa" ya karasa maganar kamar yaro d'an shekara 3.

Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Na daina kukan fad'a min me ya faru?"
"Zan fad'a miki but da sharad'i"
"Ina jinka"
"Sai kin min alkawarin kin daina fushi dani tukunna zan Sanar dake"
" Toh ai Yaya Kaine kake fushi dani bani ba, tunda ko magana ma ka daina min ko da na maka ma amsa mara dad'i nake Samu ko Kuma kaki kulani, Kuma in ba Ni na maka magana ba bakayi min"

"I Know, kin 'bata min raai ne wallahi, Amma yanzu komai ya wuce am sorry kinji?"
"Hmm Shikenan"
Mikewa yayi Tace "Haa'ah ina zuwa Kuma?"
"Sallah zanyi kema na San bakiyi ba, so ki tashi kiyi"
" Labarin da kace zaka fad'a min Kuma fa?"
"zan fad'a miki anjima ki tashi kiyi sallah, bye" ya d'aga mata hannu kana ya fice.

Murmushi tayi tana kallon hannun ta da ya rike ta dad'e tana kallon hannun ta tana shafawa da d'ayan hannun nata, sai gani nayi ta Mike firgit ta shige ban d'aki ko me ta tuna oho.

Haisam Bayan yaje Masallaci ya dawo ya koma d'akin sa yayi wanka, wando three quarter baki ya saka sannan ya saka Riga armless Shima baki kana ya fito yazo part d'insu Daddy zaman sa ke da wuya daddy ya Shigo da Baki sun Kai su Shida cikin girmawa ya gaidasu suka amsa, Kai tsaye dinning suka wuce, mummy da Umma suka fito daga kitchen da sauran abincin Nan aka Shiga gaishe gaishe, Bayan sun ajiye suka koma d'akin mummy suka fara hirarsu a chan.

Bayan su Daddy sun gama cin abinci suka d'an zanta har karfe takwas da rabi kana suka gama meeting d'in, fita sukayi duka a tare har wurin motocin su ya raka su duk suka wuce Amma banda mutum d'aya a tare suka sake shigowa a parlor suka zauna Haisam ya musu sannu suka amsa Nan fa daddy suka fara Hira ba kakkautawa da mutumin nan.

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now