🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
ByMilhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
3 and 4
Da sassafe, Haisam ya shirya don zuwa tallan Kosai Kan yaje makaranta, yana kokari yaga ya had'a kud'in w.a.e.c d'insa , Amma Kan ya dawo daga talla lokacin zuwa makaranta har ya kure, a ranar ya shigo school a makare ya tarar ansa wa anda sukayi letti shara, bayan sun gama yayi saurin shiga aji yana had'a zufa, cikin rashin sa'a ya tarar da malamin Mathematics d'insu a aji yace "Haisam Ahmad Umar, Why are you late to school and why are you sweating like a Christmas goat?" Yan ajin suka shiga dariya Ma'isha ce kad'ai batayi dariya ba don ita bata ga abin dariya anan ba, Haisam shiru yayi baice komai ba, sabida bai San me zaice Masa ba hannu ya Masa alamun ya shigo.Lokacin break, Ma'isha da kawayenta suka nufo inda yake, suna rokon sa akan ya Kara musu bayani akan darasin da akayi dazu da safe, ya na cikin koya musu kwasam wayar Haneef ya soma ringing, Afnan 'daya daga cikin kawayen Ma'isha Tace "Haneef meyasa kake kokarin distracting din mu? " " How am I distracting you, wannan ba Lokacin break bane?" Cikin 'bacin Rai Ma'isha tace " Na lura kana da neman magana Haneef, Mr trouble" Haneef mikewa yayi ya ture Ma'isha ta buge kanta a bango, Haisam ransa yayi mugun 'baci bai tsaya wata wata ba ya tsinke shi da mari, fad'a Mai Karfi ya parke a tsakanin su d'aya daga cikin d'aliban ya Kai karar su gun Form master din su.
Zane su yayi sosai kana yasa su yanka ciyawa, Ma'isha da kawayenta suka Zo da niyar taimakawa Haisam, Amma yaki yace su taimakawa Haneef sabida shi aka bawa wurin noman dayawa sabida shine silar fad'an Ma'isha Tace "A'a baza mu taimaka Masa ba, shi ya jawo wa kansa jiki magayi, yaron yana da matsala sosai" " Ma'isha ba a Rama mugun ta da mugunta, da babu Wanda zai tuba ya gyara laifin sa, Dan Allah kuje ku taimaka Masa" " okay , zamu taimaka Masa Amma da sharad'i" " What? " " Sai dai idan zaka Bari driver na ya ajiye ka a gida" "Inaa bazaiyu ba, I won't, I can't, can't you see that my uniform is very dirty? " Afnan tace " that's even more you should allow her to take you home, bai kamata ka tafi acikin kaya Masu ditti haka ba" "Okay, agreed, na amince"
Ma'isha da kawayenta sunji dad'i sosai, yanda Haisam yace sukayi hakan sukayi suka taimakawa Haneef, abin ya bashi mamaki sosai, bayan sun gama yaje ya bawa Haisam hakuri, Haneef yace "am awfully sorry for everything, Dan Allah kuyi hakuri, all of you should forgive For all the trouble I caused, Dan Allah ku barb'e ni a matsayin aboki" girgiza Kai Haisam yayi yace "Kar ka damu komai ya wuce" Ma'isha zuwa tayi ta sayo musu ruwan sanyi duk suka Sha sannan suka koma aji..
Bayan an tashe su, Ma'isha babu inda bata duba ba Amma bata ga Haisam ba, taji ba dad'i, shigewa tayi mota ta wuce gida, bayan ta bar gun ya fito ya fashe da dariya "Hahaha come and take me home Mana, so kike kije Kiga gidan mu don ki gane cewar mu talakawa ne, inaa bazaiyu ba" sai da ya tabbatar Ma'isha sunyi nisa da barin gun, kana ya fito ya wuce gida.
WASHE GARI
Ma'isha na Isa school ta tinkare shi "Na tabbata kana sane kake guje min, But Haisam, meyasa kake guje min? Why are you hurting me like this? Bani da kowa shiyasa nake so ka zame min d'an uwa kwalli d'aya, please stop avoiding me Dan Allah.""Am sorry,kiyi hakuri, forgive me please" " You're forgiven, yau zamu Kai ka gida" "Dan Allah ki bar maganar kaini gida, akwai inda nake zuwa ne Kan na tafi gida" Kan ta bashi amsa principal ya shigo yace "Good Morning class, today is the last day for those who have not paid for thier w.a.e.c fees. starting from tomorrow , personally will be coming to send home any student who comes to school without his or her Money, have I made myself clear?" Duk suka amsa da "Yes Sir" bayan ya fita, Haisam kansa yasa a Kan benci ya shiga tunani mai nisa, har aka tashi bai kula kowa ba tunanin yanda zai samu kud'in ne ke damun sa.
"Yaya zanyi?" Zancen zuci yake "mahaifiya ta bata da Kud'in da zata biya min sannan Dangin Ubana Babu Wanda yake da niyar biya min, Ya Allah ka kawo min mafita" Ma'isha Tace "lafiya kuwa? Haven't you paid the money?" Haisam yace "Eem.....Eem.... Eh but I hope to pay soon" baya cikin yana yin magana da kowa.
Ana tashi ya Kama hanyar gida shi kad'ai yake tafiyar. Ma'isha ta Shiga damuwa ta rasa abinyi daga bisani ta yanke shawarar bin Haisam. Sai da ta tabbatar driver d'inta bai ganta ba a silale tabi bayan Haisam amma Haisam bai San da cewar tana biye dashi ba, yana isa gida ya Shige, Murmushi tayi tace "Finally, yau nasan gidan su. Sai ta juya ta koma makaranta, driver yayi jiran Duniya bai ganta ba hakan yasa ya koma gida.
Ma'isha na zuwa taga wayam ba driver hakan ya tabbatar mata da ya tafi, bata da wani zab'i da ya wuce ta taka da kafa. Kan ta Isa gida mahaifiyarta ta shiga tashin hankali kasantuwar bata tab'a aikata hakan ba, ranta yayi mugun 'baci da driver sabida ya dawo ba tare da Yar ta ba, a tsawace tace "Idan wani Abu ya sami 'yata I'll make sure you spend the rest of you life in jail"
Cikina Rawar murya driver yace "Is not my fault Ma, na dubata ta ko ina a makarantar Amma ban ganta ba, sannan bata makarantar don nine mutum na karshe da ya rage a makarantar, Kuma har na bar gun ban ganta ba"
"Zaka yimin Shiru a wurin Nan ko Sai na buge maka baki? Kaje ka Nemo min 'yata....." Kan ta karasa maganar da zatayi ta hango Mai gadi ma Bud'e gate,Yana Bud'ewa sai ta ga shigowar Ma'isha, da gudu ta nufi inda take.
_____________________________
Milhat ce
Yar Terawa
Please comment and share
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali