69&70

72 4 0
                                    

'''Continuation......'''  Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa, rike shi Mamy tayi tana kallon sa daga kafan sa har tsakiyan kansa, idanun ta cike yake da hawaye, tana matukar son Haisam, tana Kuma Jin tausayinsa, hannu yasa ya share Mata hawayen da suka fara gangarowa daga idanun ta, Yana girgiza Kai alamun ya Isa.

      Murya na sassarkewa Mami Tace "Haisam Ashe ka farka? Kai Allah mun gode maka"
Malam Hassan kallon Haisam d'in yake Yana daga kwance a Kan sick bed d'insa, a hankali a Haisam ya zare hannun Mami a Jikin Sa ta fara takawa a hankali, har ya nufi gun malam hassan, wani irin Kallo malam Hassan keyi wa Haisam Mai cike da ma'anoni, Haisam d'in ma kallon sa yake, mamy ce ta matsa kusa dasu ganin Shirun yayi yawa, Tace "Haisam!!!
"d'ago wa yayi ya kalleta ba tare da yace komai ba.

     Tace "Yanzu Babu abinda kake ji ko?"
Murmushi yayi kana yace "Eh Mami" ya maida kallon sa ga malam hassan da ya juya masa keya kana yace "Ya Jikin Daddy?"
"Da sauki za'a ce kullum Babu improvement"
"Allah ya bashi Lafiya"
Mummy da Nabila suka amsa da Amin.

   Jin Muryar Nabila ne yasa ya kalli inda take a tsaye bai ma lura da ita a gun ba, Yana kallon ta ya Gane Yar Mamy ce sabida duk yaran Kama da ita suke, hatta yaranta mazan ma Babu Wanda yayi Kama da malam Hassan, duk da shid'in bafulatani ne na usul Amma bakine, Nabila ce ma ta d'an d'auki kalar fatar sa, hakanne yasa duk ta fi su kyau, Kun San ance black is beauty.


      Kallon ta yayi kana yace "Farida ko?"
Murmushi tayi kana Tace "A'a Nabila"
"oh sorry My Bad,Nabila amma Mami yarinyar Nan ta girma fa sosaiii"

   Yar karamar dariya Mami tayi duk da haryanzu hawayene fal a idanun ta, Tace "Eh ta girma nan ma baka ga Auta ba"
Nabila turo baki tayi kamar zatayi Kuku, ita ta tsani daji ance mata wai ta girma, ganin yanda take ta kunkuni ba karamin bashi dariya yayi Amma ya gimtse dariyar tasa.

    Babu Wanda ya Kuma cewa komai kusan na mintuna uku, mami Tace "Baka tambayi kanwar ka Ayrah ba"
Kai ya sane a kasa, kamar wani Mai nazari yayi ajiyar zuciya kana ya d'ago Kai ya kalli mami yace "Eh Mamy ban tambaya bane ba sabida ina da labarin abinda ya same ta"

    " kaga Allah ko Haisam? Baka da hakkin su shiyasa Allah ya Kama su, ban San me ka terawa malam ba, babu yanda banyi dashi ba Akan ya d'auke ka kamar d'an cikin sa, Amma ina son zuciya da son Kai irin nasa ya rufe Masa Ido, bai tsaya a iya Nan ba ya had'a har da Yar sa wacce bata da ji ba bata gani ba yayi amfani da ita wurin biyan bukatar sa....... " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar, Nabila ce ta sa hannu tana d'an bubbuga mata baya alamun rarrashi, mamy hannu tasa ta share hawayen ta,kana ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko kana Tace "Haisam Dan Allah na roke ka ka yafe Mana a Karo na sau ba adadi, kila in ka yafe mana Rayuwar mu zata Koma dai dai" ta cigaba da kukan ta.

        Haisam da d'an saurin sa ya nufo ta Yasa hannu Yana share mata hawaye, yace "Mami Wallahi ban tab'a rike Daddy a Raina ba ko da na minti d'ayane, Kuma maganar yafiya tun a ranar na yafe Masa wannan kadara tace Ni Musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau da Mara kyau,a ranar da Daddy yasa wa Abba guba na ganshi,Amma yace idan na kuskura na fad'awa,kowa sai ya kashe Ni ya kashe Umma,sannan a ranar da muka Koma gidan su Isha,na fito naje gidan mu don na d'auko Abu,babu Wanda ya sani daga ni sai maigadi,da idona naga daddy yana fad'a musu su sa petir ta ko ina,hmm su mutu kowa ya huta,a ranar na gane Isha is an Angel to me sends from the almighty Allah........." Ya d'aga Kai ya kalli Isha,da take ta matsar kwalla tana jin tausayin Yayan ta, ya maida kallon sa ga Mamy yace " let the bygones be gone Mamy, Allah baya barin wani don wani but am Very sure that ya barni a Raye ne to make things right and I'll surely do that insha Allah yanzu abinda ya Kamata muyi shine mu maida hankali gun Nemo Ayrah"

    Fashewa Mamy tayi ta kuka Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Haisam kaga rayuwa, kaga rayuwa sabida dangin Uban ka, tun kana yaro kaga jarrabawa kalala"

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now