_Continuation........_ jiki a sanyaye mummy ta nufa part d'insu Haisam na Mata magana Amma Bata kulashi ba, a parlor ta zauna tana matsar kwalla, Haisam cikin tashin hankali ya zauna a gaban ta had'e da riko hannayen ta, cike da kulawa yace "Umma me ya Faru ne ban tab'a ganin daddy acikin irin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi dashi ba, Haka ma mummy har kuka naga tana yi kema gashi kukan kike yi what Happened Umma?"
Cikin shesshekar kuka Tace "Nothing Haisam, babu abinda ya Faru"
"Dan Allah Umma ki fad'a ya za'ayi kice babu abinda ya faru Kuma kike kuka Dan Allah ki fad'a"
Mikewa tayi a d'an tsawace Tace "Nace maka Babu ko"
Ta shige d'akin ta.Ya dad'e a wurin yana zaune daga baya ya tashi ya bar gidan ma gaba ki d'aya.
"Kin 'bata min Rai Maryam, Akan me Zaki sa ta agaba dole sai ta amince kar ki manta fa kece Kika sa na d'auko su na ajiye su akarkashina ba takura babu takura Jan su da mukayi a jikine yasa har suka sake jiki damu muka Zama one and family, tunda tace Bata so let her be ana Dole ne? Bafa yarinya bace ba tasan me take so da abinda bata so, Shima Abdallah zan Kira sa na fad'a Masa ya bar maganar sabida na lura ya na neman sata a Rai daga jiya zuwa yau"
"Uhmn Alhaji Kenan yanzu duk abinda mukayi masu da abinda zata saka Mana Kenan, Alhaji dama don mu ba wallahi nasan inda Bata mutu ba da ta kusa mu...... "
A tsawace yace "Ke Zaki kashe ta? Nace ke Zaki kashe ta?"
Ta girgiza Kai had'e da sunkuyar da Kai, iska ya hura kana ya sassauta Muryar sa yace "Maryam zaki goge ladan da Kika Samu idan Kika cigaba da fad'an haka mun taimaka Mata don Allah Ne ba don ta biya mu ba, kar ki manta fa kece Kika kawo shawarar taimaka musu har Kika sa na dawo na su cikin gidan nan, Dan Allah idan na Isa dake ki bar maganar nan ban yarda ki sake Mata maganar ba bare ki nuna Mata a fuska"
" Insha Allah zanyi yanda kace kayi hakuri"Ma'isha da Meerah Havilla Ice cream suka nufa, Bayan Meerah ta tabbatar da ta kwantar wa da Isha hankali, ice cream suka Sha har sai da akayi la'asar tayi suka koma gida, sai da Isha ta ajiye ta a gida kana ta wuce gida.
Haisam kuwa school ya Shiga, Duk da bayi da Lectures jiran ta yayi ta gama Lectures suka Sha hiran su ya samu hankalin sa ya kwanta , sai Kuma yayi sa'a yau bata fito da motar ba hakan ya bashi kaita gida.
Bayan sallar Isha Umma kasa zuwa gun Mummy tayi suyi hirar da suka Saba, Ma'isha na d'akinta taji Duk bata jin dad'in zaman hakan Yasa ta fito parlor ganin ba kowa ta nufi d'akin Mummy da sallama ta shiga Tace "Mummy ya na ganki a kwance yau baza a yi hiran parlor bane?"
"Uhmnn bani Jin dad'i ne"
"Subhannallah me ya same ki?"
"ciwon Kaine ba wani Abu ba"
"Amma kinsha magani ko?"
"Eh Nasha"
"To Allah ya sauwaka"
"ameen"
Mikewa tayi Tace "Bari naje part d'insu Umma"
"Okay" tab'e baki Isha tayi ta nufi part d'insu Umma.Ganin Umma Bata parlor ta wuce d'akin ta cike da mamaki Tace "Umma kema a kwance ko kema bakya Jin dad'in ne?"
Kirkirerren Murmushi tayi tace "Eh wallahi bana Jin dad'in jikina"
"Oh ikon Allah sai kace Kun had'a baki ga mummy ma a chan ta kwanta wai kanta na ciwo"
Umma a ranta Tace "Oh Allah kar dai ita ma tasa maganar a ranta kamar Ni" a bayyane ta ce "Lallai kamar mun had'a baki"
"Allah ya baku Lafiya"
"Ameen"
"Ya Haisam fa yana Nan?"
"Ki duba shi a d'akinsa d'azu dai baya Nan ban San ko ya Shigo ba"
Ta amsa da "Ok sai da safe Allah ya sauwaka"
"ameen daughter nagode."'dakin Haisam ta nufa ta shige d'akin taga wayam Bayanan, kwan kwasa kofar d'aki tayi ko Yana ciki taji shiru hakan ya tabbatar mata da Bayanan d'aga kafad'a tayi irin I don't care, ta fice.
A hanyar ta, ta fita suka had'u da Isha yace "Princess kin dawo Kenan?"
"Eh na dawo tun d'azu"
"Su Umma fa"
"Suna kwance wai Basu da lafiya"
"Duk su biyun?"
" Eh Umma wai zazzab'i take ji Mummy Kuma Wai ciwon Kai""Hmm kin San d'azu bakyanan me ya Faru?"
"A'a sai ka fad'a"
Nan ya jero Mata abinda ya gani da idon nunsa , cike da mamaki tace "eh Lallai no wonder biri yayi Kama da mutum, to Amma me ya faru haka?"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali