Duk su ukun suka Mike suna kallon juna Meerah Tace "Isha me ya kawo Yar iskan yarinyar Nan gidan Nan?"
Murya na rawa Tace "Dama kin santa ne?"Wani irin mugun kallo ta mata sama da kasa Tace "Nasan ta mardiya Kenan, itace wacce nake baki labari Wanda suka Shiga tsakani na da Bashir da kawarta Ayrah"
Kallonta mardiya Isha tayi Tace "Tirkashi to ai nima itace kawar Ayrah da sanadiyar ta Yaya na ya Shiga comma"Ma'aruf Duk ya rikece ya kasa fahimtar inda maganar su ta dosa cikin rashin fahimta yace "Wai me ke faruwane Kun sani a duhu?"
Meerah Tace "Ni zan fitar da Kai daga cikin duhu ko Kuma ince zan kunna maka haske,in dai Wannan yarinyar kanwar kace Wallahi Sam bakayi dacen kawa ba sabida wannan da kake gani tafi bakar macijiya mai mugun dafi"
Isha Tace "Please Meerah maganar nan ta wuce, please kiyi hakuri ki manta komaai dan Allah"
"Isha ke Shaida Ce kin San halin da suka sa na shiga, Duk duniya zan iya yafe komai Amma banda abinda Sukayi min"
Ma'aruf yace "Isha please Kar ki hanata Dan Allah, Meerah Sanar dani me Kanwata ta Miki?"Mardiya kuwa duk da AC da ke d'akin bai hana jikinta jikewa da zuwa fa, sai rarraba idanu take, juyawa tayi da niyar fita daka Mata tsawa ma'aruf yayi yace "Dawo Nan"
Jiki Sim sim ta dawo ya nuna mata kujerar dake gaban sa yace "Zauna anan" sai da ta zauna ya maida kallon su ga Meerah da Isha yace "Please ku zauna, Meerah ki Sanar dani abinda ya kamata na sani"
Kallon Kallo Meerah da Mardiya suka shigayi wa juna.Ana wata sai ga wata shine mene ne wannan abun da Mardiya tayiwa Meerah?
Ku cigaba da bibiyata, don Jin yanda labarin zata kasance.
_____________________________
Ina Jin dad'in comments d'inku Group d'in Dangin Uban dama sauraun groups d'in, bana samun damar yi muku reply Amma ina gani sannan hakan na faranta min Rai nagode Sosai Allah ya bar Kauna.Please kuyi min sharing sannan ku cigaba da Sharhi ni Kuma na Rika yi muku typing
Milhaat Ce
Yar Terawa
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali