17&18

86 5 0
                                    


Haisam da Ma'isha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?"

"Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?"
"To ai Ni bana sal...... " Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me?"
Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?"
Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours"
Yace "Naga kunyi sauri ne ai"
Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?"

Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi"
Tace "To a dawo lafiya"
Ya amsa da "Ameen"
Sai yayi ficewar sa.

Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa.

Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwab'ar nan Haka"

Haisam yace "Daddy ai saima abinda ya karu, Mijin ta zai Sha wahala sosai don na tabbata ko da bayan ta haihuwane Reno biyu zaiyi"

A zuciyar Tace "Zaka Sha Reno dai, don kaine mijin nawa Insha Allah" a bayyane Kuma Tace "Uhmnn daddy kace Masa ya daina tsokana ta" har da bubbuga kafar ta kamar yarinya Yar shekara biyar daddy yace "Son ka daina tsokanar ta"

Haisam dariya kawai yayi baice komai ba, mummy ce ta Shigo parlor taci kwalliya sai zuba kamshi take Tace "Daga dawowar sa kun sashi a gaba da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karb'ae jakar sa"

Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi  tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta"
Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa"
"Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku"
A tare sukace toh.

Karb'an jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa"
"Anki d'in mijinkine ko mijina?"
Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?"
Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun d'azu ta wuce d'akin sa.

Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori"

Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi"
"kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? "
"Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?"
"Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki."
Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo.

Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?"
Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko"
" Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace"
"Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo"
"nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare.

Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki"

"sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu"
"a a yi hakuri nayi shiru"
Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta"
Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa"
"Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?"

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now