_Continuation........._ Cike da fargaba da tsoro suka chiccibeta suka kaita A&E (Accident & Emergency) Nan da Nan likitoci sukayi kanta, kwata kwata bata numfashi da taimakon Oxygen ta fara numfashi, Haisam kuwa yazo wucewa ne don duba patient d'insa ya hango meerah na ta aikin kuka, da sauri ya karasa inda suke ganin Isha ce a kwance bata motsi ya birkice Yana tambayar su "Me ya same ta ne?"
Wurin Meerah ya nufa Yana tambayar ta "Meerah what Happened to her? Me ya same ta? Please ki Sanar dani"
Cikin kuka Tace "Yanke jiki tayi ta Fad'i"
Likitane ne ya juyo yace "Dr Haisam, itace sister d'inka ko?"
Cikin rawar murya yace "Eh itace"
"To ya akayi kuka bari har ciwon zuciya ya kamata?"
Zaro Ido yayi yace "What ciwon zuciya dai? But how comes?"
Kafad'ar sa ya d'aga had'e da fad'in "I don't know, thank goodness ma ta samu kulawa cikin gaggawa da an rasata Kai ma kasan irin wannan lokaci d'aya mutum yake mutuwa ko Kuma ya kamu da mutuwar 'barin jiki"
Haisam dafe kan sa yayi ya jaa da baya ya jingina da bango yana kallon Ma'isha da haryanzu oxygen na hancin ta, d'an bubbuga shi likitan yayi kana ya fice dashi da sauran nurses d'in.Kallon Meerah yayi yace "Dan Allah ki Sanar dani me ke damun Princess nasan kisan komai a kanta sabida kinfi kusanci da ita fiye da kowa"
Kai a kasa tace "Ni ban san komai ba, babu abinda na sani"Girgiza Kai kawai yayi ya Koma kusa da ita ya zauna ya sanya hannunta a cikin nasa Yana ta kallon ta, sai yamma ya tuna bai Kira su Mummy ba, Nan ya kirasu ya Sanar dasu, ba dad'ewa Mummy da Daddy suka zo, mummy na ganin halin da yarta ke ciki ta Shiga rera kuka dakyar daddy ya samu ya rarrashe, a takaice dai Ma'isha a haka ta kwana bata farka ba ta kwana ta wuni tana bacci, sai yamma lis ta bud'e idon ta haisam da kanshi ya duba ta, ya mata alluran da ya kamata, aiko ta sake komawa bacci.
A takaice dai Ma'isha Kwanan ta uku a gadon asibiti, sai da ta d'an Samu sauki aka sallame ta, a cikin Yan kwanakin Nan ta rame ta lalace Kamar ba ita ba, kuka kuma sai abinda ya karu,mummy da daddy sunyi rarrashin sunyi fad'an Amma taki fad'a musu, mummy Tace "Ma'isha idan baki fad'an min damuwar ki ba wa Zaki fad'awa umm? Ki duba kiga yanda kika lalace fisabilillahi baki kyauta wa Kanki ba wallahi"
"Mummy nifa ba abinda yake damina"
"Idan babu abinda ke damin ki me ya kawo miki ciwon zuciyar?"
"Uhmnn mummy ciwo ne kawai daga Allah ba wani abinda yake damina"
"Toh naji kukan da kike Kuma fa? Ki duba abincin Nan da sadiya ta kawo miko tun na safe baki ma tab'a shi ba"
"Zanci Mummy"
"A gaskiya Ma'isha bana Jin dad'in ganin ki a haka Dan Allah........ "Sallamar da akayi ne ya katse ta amsawa tayi had'e da kallon kofar don ganin wane ne, Murmushi Umma tayi Tace "Ameerah kece?"
"Eh Mummy ina wuni?"
"Lafiya lau ya gida ya su maman naku?"
" Suna lafiya sunce a gaishe ku da maie jiki"
"Allah sarki muna amsawa , sannu Ameerah Allah ya biyaki sai faman wahala kike "
"Aaaa haba Mummy nida Isha ai Mun Zama d'aya nima idan hakan ta same ni nasan zata min fiye da hakan,fatan mu shine Allah ya bata lafiya"
"hakane Allah ya bar zumunci"
"Ameen Mummy"
"Please kiyi Mata magana ta fad'a miki abinda ke damin ta, Kuma taki cin abinci, rabonta da abinci tun jiya da dare"
"Kar ki damu mummy zataci insha Allah"
Mummy fita tayi ta barsu da ga ita sai Isha, plate da d'auka tasa abincin d'an dai dai ta ajiye Sannan ta zaunar da ita ta Shiga bata a baki ba musu ta karb'a.Cike da kulawa Tace "Haba Isha, Isha so kike ki kashe Kanki?wannan fa ba alkawarin da Kika d'aukan min ba Kennan, kin zabi ki mutu Kennan?"
"uhmn zan mutu idan kwana na ya kare,kema kin San da hakan ko?"
"Amma kuka ai gangancin kine zai saka ki rasa ran naki tun kwanakin ki bai kare ba, wallahi Isha na gaji da ganin ki a Haka, a gaskiya lokaci yayi da zan fad'a Masa da dasu mummy"
"Meerah please ki tuna alkawarin, Duk Wanda ya karya alkawarin to ba Makawa alkawari zata cishi, kin fiso a rasa rayuka biyu ne?"
"Ban gane a rasa Rayuwa biyu ba, wa Dawa Kenan?"
" Ni da Ya Haisam, wallahi farin cikinsa matters allot to me, bazan juri ganin sa a cikin damuwa ba, moreover ba Sona yake ba"
"Shima Kuma bazai tab'a jin dad'in abinda kike Shirin aikatawa ba, ko da ace baya sonki na tabbata zai so ki Nan gaba"
Maganar Meerah a kunnen Haisam ya sauka, turo kofan yayi ya shigo gaisawa sukayi kana Meerah ta Mike Tace "Zan wuce asibiti dama nazo na duba jikin nakin ne, sai gobe zan dawo insha Allah, Allah ya baki Lafiya"
Suka amsa da ameen tayi ficewar ta, tana fita ta nufi gun motar ta Muryar Haisam taji yana kiranta a hankali ta juya tana jiran sa.
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali