75&76

91 4 0
                                    

'''Continuation.........''' sai da ya Kai bakin kofa yasa hannu ya bud'e kofan kana ya waigo ya kalle ta, Murmushi yayi yace "Zaki Koma gida a matsayin Mata ta, idan kin amince ki same ni a d'akina, and kir ki wani damu da batun waliyi, Zanyi handling na komai" ya fice kana ya rufe Mata kofar , duk da ya fita Amma baki a bud'e take kallon kofan, tana mamakin karfin Hali irin nasa.


Zama yayi yana jiran ta Amma shiru har bacci yayi awun gaba dashi, alarm d'insa ne ya buga na karfe 5 ,jaan wayar yayi ya kashe kana ya Shiga ban d'aki ya d'auro alwala ya tada sallah , Bayan ya idarne ya Koma baccin Sa.


Ayrah kuwa kasa bacci tayi tana ta kuncewa da tsakawa ta rasa abinda zatayi, sai da taga wuri ya fara haske ta shige ban daki tayi alwala, Bayan ta idar da sallah, zaune take Akan prayer mat d'in haryanzu dai maganar Adnan ke Mata yawo a kwakwalwar ta, Bayan ta gama tsakawa da warware a bayyane Tace "Zan amince na aure ka, Amma da zaran na fita anan dole ne ka sake ki, in Kuma kaki kotuce zata rabani da Kai"


Kofar d'akin sa ta nufa, ta kwankwasa kofar had'e da kusa Kai ciki, duk zaman ta a gidan bata tab'a zuwa d'akinsa ba, daga d'akin da take sai kitchen, baccin Sa taga yana yi, ta koma da niyar fita Muryar da taji yace "Ina Zaki?" Cikin Muryar bacci ya mata tambayar Nan.

"Na d'auka bacci kake"
"Umm yanzu na farka Shigo Mana"

Kujeran dake gaban Mirror ta ja ta zauna a kusa dashi kana Tace "Nazo muyi magana ne"

Zama yayi yana d'an goge idanun sa da yatsunsa kana yace "Ina jinki"
Shiru tayi kanta a kasa kana Tace "Na'amince zan aure ka, Amma Dan Allah Kar ka cutar Dani" hawaye fal a idanun ta, hannu yasa ya share mata kana yace "Insha Allah, I will never guv you the chance to regret, Is a promise"
Murmushi tayi, shima ya maida mata mikewa yayi da d'an saurin sa ya shige ban d'aki karar ruwan da taji ne hakan yasa ta gane yana wanka ne, Zama tayi tana jiran sa, tana jin ya fito ta sunkuyar da kanta, ta cigaba da wasa bda yatsun ta, abun ma dariya ya bashi, me bata sani a Jikin sa ba? Sai da ya gama Shirin sa tsaf yace "Muje muyi breakfast ko?"

Ta amsa da toh, had'e da mikewa tayi gaba yabi bayanta, yau tare sukayi girki, sunayi suna Hira abin birgewa kamar wasu amarya da ango, ko da yake sun kusa su fad'a lambun ma'aurata.

Bayan sun gama karyawa ne, ya fita da niyar tsara komai na yanda za'a d'aure auren sa da Ayrah, hakan kuwa akayi bai dawo ba har sai da ya tabbatar an sa ka ranar d'auren su Nan da sati d'aya hakan kuwa akayi,dama ba wuya a wurin Allah muddin an sa Rana, a yau aka d'aura auren Adnan da Ayrah Akan sadaki dubu d'ari.

(Oh Ni Milhat jikar Mutum hud'u, Adnan ya d'aura auren da masoyiyar sa ba tare da iyayen sa ko iyayen ta sun sani ba, yayi hayan iyaye ba tare da Wanda ya d'aure ya sani ba, Ko ya zasu wanye? Mu cigaba da zuwa).

Adnan ya sa an yi Masa video don ya tabbatar wa da Ayrah cewar an d'aura musu aure ta Zama mallakin sa, Allah sarki Ayrah a duk sanda aka d'aura wa yarinya aure tana samun kula ta musamman a gun dangin ta, za a rako ta har d'akin ta ana nuna mata so da Kauna sannan su rabu cikin kuka da kewar juna, Amma kashhh ita ta samu aka sin hakan, video d'in da yayi shine shaidar auren su, tayi kuka sosai Adnan tun yana rarrashin ta har ya daina ya fita ya bar mata d'akin ma gaba ki d'aya.

Tun daga wannan ranan Ayrah kullum cikin kuka take,shi Kuma Adnan baya gajiya da bata hakuri a haka har ta sake Jiki dashi ta bashi dama Yana nuna mata irin soyayyar da yake mata,yana Kuma saka ta tana Kara son shi,duk da cewar tana kokarin taga ta 'boye,Amma masu iya magana sunce shi so baya 'buya.

Haisam ta samu sauki sosai har ya Fara fita gun aiki,farin ciki da kwanciyar hankali Kuma sai dai ace Alhamdulillah,Isha na samun kula sosai musamman ma gun Umma da ta hana ta fita ko ina,idan ta fito to tare da Haisam suka fita Nan ma idan suka dad'e Umma tayi ta Kira Kenan Kira Kan Kira.

Shirye shiryen Biki Meerah ake yau saura kwanaki Uku, events Kam sun Sha shi,sunyi friends day,bridal shower da dai sauran isha ba a barta a baya ba duk da ba wani Abu take ba sai dai ta zauna tana kallon su.

*Ranar Biki*
Farukh ne zaune da Haisam da sauran abokan sa suna shiri zuwa gun d'aurin aure sai tsokanan sa suke musamman ma haisam da dama sarkin tsokana ne,wayar Farukh ce tayi kara har da bazai d'auka ba sai Kuma ya zaro wayar a chaji ,sakon da ya shigo wayar sane yasa shi tsuman tsaye,Nan da Nan hawaye suka cika idanun sa,Kallo d'aya Haisam ya Masa ya Gane ba lafiya,hakan yasa ya mike ya nufi inda yake kafad'ar da ya dafa had'e da fad'in "Ya dai ango Lafiya kuwa ga na ganka Haka?"

Farukh Mika Masa wayan yayi ba tare da ya Ce Masa kala ba, Haisam da d'an saurin sa ya sa hannu ya karb'a.

Yana ganin abinda faruk d'in ya kalla zaro ido yayi dq d'an karfi yace "whaaaaatttt!!!!
Hakan yasa dukkanin abokan su hankalin su yayi ta Dawo kansu,d'akin shiru yayi baka jin motsin komai sai Karan AC da kumma TV dake aiki.
_________________
Please comment and share
Milhat ce
Yar Terawa

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now