Ma'isha ganin har sun Isa bai kulata ba cikin Murya kamar zatayi kuka Tace "Yaya yanzu Dan Allah baza ka kulani ba? Duk hakurin da nake baka baza kayi hakuri ba tsakani da Allah, bayan Kuma Kai ne kamin laifi"
Kallon kin Raina min hankali ya Mata sannan yace "Ni ne ma nayi Miki laifi?"
"Eh Kaine"
A dai dai suka Shiga School d'in sai da yayi parking kana yace "Uhmn ina jinki laifin me na miki?"
"Kasan time d'in da zan gama Lectures sannan ka kashe wayar ka bayan Nan Kuma kaje ka zauna da yarinyar Nan kana hiran ka hankali kwance ka ma manta dani" ta karasa maganar tana matsar kwalla.Murza goshinsa yayi ya ce "Amma meyasa baki min magana ba?"
Bud'e kofar motan tayi Tace "Haka kawai" ta rufe kofar motan da d'an karfi yayi Kara har Saida yayi saurin rufe idon sa, hatta mutanen da ke tafiya da Wanda ke zaune suka kalli inda suka jie karar wasu suna magana kus kus.Haisam kuwa fita yayi daga makarantar Sai da ya daidai ci lokacin da Aysha zata Shigo ya dawo,Bayan sun had'u suka Shiga hirar su har ta manta da wani abu Wai shi Lectures, ganin karfe 6 ya kusa yace ta tashi ta wuce gida maghrib ya kunno Kai, ba musu tayi yanda yace.
Har wurin motar ta ya raka ta sai da ta Shiga ta tada motar ya bar gun ya d'aga mata hannu ya nufi gun motar sa, daga nesa Ma'isha ta hango su girgiza kai tayi a tare suka nufi wurin motar, zagayo wa yayi ya bud'e mata ta Shiga ta zauna sannan ya rufe, kana yanzagaya Shima ya Shiga ya tada motar suka wuce gida.
*AFTER 1 WEEK*
Wata shakuwace mai karfi ta Shiga tsakanin Aysha da Haisam, yayin da tsakanin shi Ma'isha ina kwana ina wuni ne kawai.Wata ranar lahadi, ta shirya ta Sanar da Mummy zata gidan su Ameerah Mummy ta mata fatan a dawo lafiya sannan ta jaddada mata kar ta dad'e, Haisam ta hango a garden d'in gidan kanta ta kawar kamar bata gansa ba, gun Driver ta nufa ta umurce shi da ya d'auko mota ya Kai unguwa, cikin sauri ya d'auko yayie parking ita kuwa ta Shiga gidan baya.
Haisam kallon ikon Allah yake a bayyane yace "Wato yarinyar Nan ta ganni Amma tayi kamar bata ganni ba, Kuma ma ina zata je da Rana tsaka haka?" Ganin ba samun amsa zaiyi ba ya zaro waya ya kirata.
Tana ganin call d'in tsaki tayi ta kashe wayar ma gaba ki d'aya, Haisam bin wayar sa yayi da kallon ganin ta danna Masa Line busy,ciza leb'en sa yayi,ya Shiga cikin d'akin sa ya d'auko key d'in motar sa ba fice daga gidan,basu d'au lokaci Mai tsawo ba suka Isa, sai da ta fita ta waigo ta kalli driver Tace "Baba kabiru kar ka manta karfe biyar Zako d'aukana"
A d'an rutsune yace "Inshallah rankashidad'e, karfe hud'u da rabi anan zata same ni"
Murmushi tayi Tace "To sai anjima"
Ta shige ciki.Ma'isha ne zaune a Kan gadon Ameerah suna kallon juna, tana kwararo Mata bayani, sai da ta gama bata labarin duk abinda le faruwa tsakanin ta da Haisam kana ta fashe da kuka mai cin Rai.
Ameerah taji tausayin kawar tata sosai, ta Shiga rarrashin ta har sai da tayi kuka mai isan ta don kanta tayi shiru.
Ajiyar zuciya Ameerah tayi Mai d'an sauti tace "Isha gaskiya Yayan ki bai kyauta ba tun ba yau ba nake fad'a miki kin nunae damuwa sosai akan shi na miji ba a mishi haka, in fact ma d'an Adam haka yake idan ka nuna masa ka damu dashi sosai sai ya d'auka duk duniya baza ka tab'a samun irin sa ba ko Kuma baza ka iya Rayuwa babu shi ba, Ni shawarar da zan baki shine ki cire Shi a ranki alamu sun nuna Yana son So Called Aysha d'in Nan, Don iya abinda Kika fad'a min Haisam a matsayin kanwa ya d'auke ba masoyayi ba"
Murmushin takaici Ma'isha tayi Tace "Nayi kokarin fahimtar hakan Ameerah Amma na kasa ke Kanki kin sani tun muna makaranta nake crushing d'insa, in fact tun muna primary, Har Saida muka Isa SS 3 da ya bani amsar tambayar da ake kana na Samu damar Shiga rayuwar sa, yanzu Kuma kice na rabu dashi?"
YOU ARE READING
DANGIN UBANA
General FictionLabarin DANGIN UBANA labarine Wanda ya kunshi, mugunta, makirci, soyayya, hassada da Kuma zamantakewar iyali