81&82

119 7 2
                                    

Continuation...............Mardiya ce tsaye tana kallon d'an jaririn Isha Kuma d'a agun Yayan ta , jiki na 'bari ta d'auki d'an tana kallonsa kamar yayanta ne yayi kaki ya zubar, Kuka tayi sosai sabida mutuwar yayanta da iyayen ta sun dawo Mata sabo fil, har kasa ta durkusasa ta roki yafiyar Isha dama Mutanen gidan gaba ki d'aya, duk wani munafurcin da tayi ta kullawa ta fad'a musu hatta 'bata auren Farukh da Ameerah da tayi Niyan yi, kowa sai da yayi mamakin abubuwan da ta aikata Amma ance d'an Adam ajizine, Isha ta yafe Mata, anan take shaida musu anga Aurahi suyi murna matuka musamman ma Haisam da haryanzu Yana sonta Amma a matsayin soyayyar ya da kanwarsa.

Har gida taje ta nemi yafiyar Meerah da Farukh, Kuma sun yafe Mata,duk da Farukh da kyar ya hakura sabida ya d'au alwashin sai ya d'auki fansar abinda ta yiwa meeran sa.

"Ayrah me hakan yake nufi? Congratulations? Ciki kike dashi?"
Duk a jere mami ta jero mata tambayoyin nan. Kallon ta kawai Ayrah take yi sai ta kawar da kanta tana fuskantar bangon d'akin.

      "To Wallahi Dole ne a zubar da cikin Nan, wannan abun kunyan ba dani ba Baki Isa ki haifa min shege a cikin zuri'a ta ba"
"Mami!!" Ayrah ta kira sunan ta kamar ba ita tayi maganar ba, Zama tayi ta jigina jikin ta ta pillow kana Tace "Mami bazan zubar da cikin Nan ba sabida ba d'an  shege bane"
Baki a bud'e take kallon ta Tace "Ashe baki da hankali Ayrah ban sani ba? Ko dai kin samu tabin hankali ne?"
"Ni Lafiya ta kalau au..... " Bata karisa maganar ba taga shigowar Mardiya wani irin Kallo ta mata sai Kuma ta kawar da kanta.

    Mardiya karasowa tayi ta dafe ta a kafad'a had'e da fad'in "sannu Qawata" ture hannun ta Ayrah tayi cikin tsawa Tace "Kar ki tab'a Ni" a d'an zabure ta jaa da baya tana mamakin abinda ke damun ta, mardiya Tace "Ayrah lafiyan ki kuwa, me ke damin ki?"

    "ina mijina?" Shine tambayar da ta wurga mata kallon Kallo Mami, Mardiya da Nabila suka Shiga yi kana suka maida kallon su gareta, Mardiya ta ce "Mami bari naje na Kira likita don na lura bata cikin hayyacin ta maybe ya tab'a mata kwakwalwar ta"
"Ke malama da hankalina Kuma a cikin hayyacina nake nace miki ina Kika Sa aka Kai min shi"

"Auuu Wai Adnan kike nufi? Yaushe Adnan ya Zama mijin ki Kuma, Ayrah na lura baki da hankali"
"Kar ki Kuma cemin bani da hankali Adnan mijina ne Kuma ina son sa" mikewa tayi Tace "ina yake?"

Kallon ta Mardiya tayi kana Tace "Me nake gani kamar cikine a Jikin ki Ayrah? Fyad'e ya Miki?"
Zafin zuciyar Ayrah ya Shiga yi mata saisaita kanta tayi kana Tace "Kina 'bata min lokaci ina yake?"

     "Mutumin da ya sace ki? Ya Miki fyad'e? Sannan yayi kidnapping d'inki shi kike Kira da miji Ayrah?"

Mami ne tayi karfin halin rike hannun Ayrah ta zaunar da ita cike da tausayin Yar nata don zuwa yanzu a tsorace take ga kukan da Ayrah ta fara, cikin Muryar rarrashi Tace "Ayrah ki fad'a min abinda ya faruwa tun daga ranar da Kika barni a asibiti Akan zaki je gidan su Mardiya?"

Shiru tayi tana kallon ta zancen zuci take " Taya za'ayi na fad'a mata abubuwan da ya faru,Taya za'ayi na fad'a mata cewar ina son Wanda yamin fyad'e a karo na ba adadi? Taya zan fad'a mata irin abubuwan da Adnan yamin?"

Sai ta tsinka kanta da fad'in "Mami a hanya ya tare ni sannan yayi barazanar zai kashe ni idan ban bishi ba,Ni Kuma naji tsoron Kar ya cutar Dani sabida nasan na yaudare shi,Bayan na Shiga motar sa sai ya kaini gidan gonan sa tun daga wannan ranar take bani duk wata kulawa sai nake mamakin meyasa ya d'auko ni in dai bai cutar dani yake Shirin yi ba? Dana tambaye shi dalili yace Yana so ya hora nine Amma Kuma bai tab'a cutar dani ko na second d'aya bane....."

Ajiyar zuciya na ta sauke ta cigaba da fad'in "Tun a wannan lokacin yace zai dawo dani gida Amma da sharad'in zan aure sa,Ni Kuma a wannan lokacin wutar tsanar sace a zuciya ta naki amincewa da bukatar sa,aiki kawai yake fita idan ya dawo yana Nan a cikin gidan sai abinda nake so yake yi ,Mami kin San zuciya Kuma ya Hadu da dama Nima inason shi tunda akan sa ne na San mene ne soyayya, soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanina dashi daga bisani muka yanke shawarar a d'aura Mana aure,Bayan Yan watanni ya nemi mu dawo gida sai naki sabida ina tsoron zaku rabani dashi" ta fashe da wani irin kuka Mai cin raai. Kallon ta Mami tayi ji take kamar karya take mata,Amma duba da yanayin jikinta da bata rame ba ,jikinta yayi kyau tayi fresh hakan ne ya tabbatar mata da cewar gaskiya take fad'a mata.



   Rungumar ta Mami tayi tana patting Bayan ta kamar wata Yar baby,babu Wanda ya Kuma cewa komai sai sautin kukan Ayrah da AC dake aiki a d'akin,Mami Tace "Ayrah lamarin kin Nan ya d'aure min Kai,wannan wani irin rashin hankali ne Ayrah kin sani cikin damuwa,bana iya bacci bana Kuma iya cin abinci duk a kanki Ayrah, ga Jikin baban Kuma abin Sai Kara gaba gaba yake yi" ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Ayrah Tace "Mami Dan Allah ki daina kuka,kinsan kukan uwa Akan 'ya'yan ta ba abu bane Mai kyau"
Murmushi mami tayi Wanda yafi kuka ciwo Tace "Kin San da hakan Kika yanke wannan d'anyen hukuncin? Kin tab'a tunanin a wani Hali nake ciki ko da na second d'ayane?"
Ayrah kasa magana tayi idan mami tasan wahalar da tasha baza Tace haka ba idan Kuma ta kuskura ta fad'a mata tasan cewar ita da Adnan har abada.

        *Bayan kwana biyu*
Adnan da Abdallah horo ake musu mai tsanani, duk sun lalace sunyi baki, musamman ma Adnan da shine babban Mai laifi, dakyar Ayrah ta shawo Kan Mami suka dunguma zuwa asibiti, tu daga waje take jiyo ihun say da gudu ta Shiga cikin Suma Mami suka rufa mata baya, Ayrah na kokarin shigewa inda take Jin kukan sa, wani police dake tsaye yaga shigowar ta ya daka mata tsawa ba ita kadai ba hatta su Mami Saida suka tsorata.

"Ina Zaki?"
Cikin kuka Tace "Dan Allah kace su daina dukan shi ni ba sace ni yayi ba"

Isha da jaririn ta na samu kulawa sosai a gun Umma da Mummy , harda Haisam da yake ji kamar d'ansane, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sa wato Mansur (Mansur Mansur) su Mardiya sai rawar kai ake, su Meerah uwaye ita ma da d'an katon cikin ta anci ansha daga bisani kowa ya watse anan Mummy ta bukaci Isha ta koma gida Sam Umma bata ji dadi ba dakyar ta amince ta koma gida.

       Rikici akayi sosai tsakanin family d'insu Adnan dana Ayrah sabida Mahaifiyar shi sama taki amincewa da wannan auren, Adnan kuwa ya kafa ya tsare bazai tab'a rabuwa da matar Sa ba musamman a a yanzu da  yasan tana son shi duba da irin karyar da tayi don ta kare shi ya tabbata da ayanzu yana gidan yari.

Dakyar mahaifin Adnan ya shawon Kan hajiya larai(Mahaifiyar Adnan) Akan idan ta haihu za'a kawo Masa matar sa, Adnan ya nuna shi Sam bai San da wannan zancen ba a haka yasa dole aka kawo Masa matar sa.

   'bangaren Malam Hassan kuwa hankalin shine ya kwanta ganin yarsa ta dawo , Kuma ya amince da auren nasu, Haisam ne ya d'auki nauyin jinyar sa zuwa India inda mami da Faisal ne suka tafi, ya daina fushin da yake da mahaifin nasa.

  Mardiya kuwa Abdallah ya daina kulata tayi kuka har ta kamar idanun ta zasu Fad'o da taimakon Adnan ya hakura har ya tura iyayen sa a nema Masa auren ta.

       Zuwa yanzu Little Mansur Yana wata shida a yayinda kamanin sa da ubansa yake sake fitowa , a sanadin sane mardiya ta canza ta daina duk wani mugun hali nata, idan bata gun aiki kullum suna tare dashi bata ma barin Isha ta d'auke shi idan kaga ta kaishi gunta to don yasha nonone hatta wanka ita take mishi.

*Bayan shekara d'aya*
Abubuwa da dama sun faru, Meerah ta haihuwa yarta mace,taci sunan aminiyarta Ayrah, Ayrah don farin ciki har kuka Saida tayi,  Malam Hassan Lafiya ta samu sannan Abdallah da Mardiya sunyi auren su babu wani shamaki, a yayin da Haisam Kuma zallan so yake nunawa Isha, don ita kanta ta Fara tsorata da irin soyayyar da yake Mata, Daddy da Abba suka yanke shawarar d'aura musu aure da zaran ta yaye little mansur.


    Bayan an yaye little mansur, aka sa ranar Auren Isha da Haisam anyi hidama sosai Saida garin gombe ya amsa, Bayan aure kuwa Isha ta koma aiki a karkashin asibitin Haisam, daga bisani Haisam ya hana ya bud'e Mata babban chemist yasa mata masu aiki tana gida kud'i suna Shiga account d'inta, sai da ta suka mori amarcin sa kana ya koma bakin aiki a hakan ma idan ba wani serious abu bane ba Zama yake a gida.

*After 5 years*
Dukkanin family suna cikin kwanciyar hankali , a yanzu Isha yaranta 6,3 mata 3 maza da Mansur ya Zama Yara 7, Ayrah kuwa yaranta 4,3 mata d'aya na miji Wanda shine d'an farin ta, sai Meerah yaranta biyu da Mai sunan Isha sai kanin ta daga Nan Kuma haihuwan ya tsaya, Nabila ma tayi aure, haka ma Faisal, a haka family din suke cikin kwanciyar hankali sannan kullum suna cikin mutunci da mutun ta juna.

Alhamdulillah Alhamdulillah, a yaune na kawo karshen littafina Mai suna DANGIN UBANA, Nagode sosai da goyon Bayan da kuka bani har na samu na kammala.

Kuskuren da nayi aciki Allah ya yafemin abinda na fad'a dai dai Kuma Allah ubangiji ya bamu ladan sa dani daku baki d'aya, har kullum Ni din ce Milhaat taku Yar tarewa ku kasance dani a littafina na gaba Mai suna *HAKKIN SO* da fatan zaku bani had'in Kai Nagode.

DANGIN UBANAWhere stories live. Discover now