pg 1.....

730 17 9
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]

_*ANAYAH*__[Heart Touching Story]

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.





*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


بسم الله الرحمن الرحيم

_*Ya ALLAH yadda na fara rubuta littafin nan lafiya*_ _*kasa in gama shi lafiya,ALLAH kasa in rubutaa abun da zai anfanar da mutane da al'umar*_ _*musulmi gaba daya,ALLAH ya jikan iyayen mu da kakannin mu,ALLAH ya gafarta mana*_ _*zunubanmu,ALLAH ka bama marasa lafiya wadanda suke gida da asibiti lafiya.Ameen ya hayyu y*_ _*qayyum.*_

*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_


*_#hadith of the day_*

_An karbo daga Nanah Ummu Habiba (R.A) tace"Naji manzon ALLAH (SAW)yana cewa wanda yayi salloli_ _na nafila raka'a goma sha biyu a wuni daya,da dare daya za'a gina masa gida a aljanna._

_Muslim ne ya ruwaito shi._


*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_

_*Pg 1.....*_

_EDITED_

Daga ina zan fara,labarin rayuwata ko kuma labarin soyayya ta da Haydar.Labarin rayuwata yana da matukar sarkakaiya,da wahala in iya baku shi saboda nasan bazaku iya dauka ba,dan cike yake da ban tausayi,azabtarwa da kuma cin amana mai tsanani,da farko ban so in fara baku labarin rayuwata ba,amma daga baya sai nayi tunanin cewa inna baku labarin rayuwata zakuyi koyi da darussa masu matukar yawa a cikin sa,dan haka yanzun zan fara baku labarin rayuwata ne mai cike da abubuwan mamakin da ban san ya zan musalta muku shi ba,amma kar ku damu zaku fahimci komai a lokacin da muka shiga cikin labarin na,labarin rayuwata wacce nayi mata lakabi da labarin ANAYAH,kafin in baku labarin soyayyata da Aliyu wacce ta kasance cike da sadaukarwa,wasa da hankali,jarumta,zugar abokai da sauran abubuwa masu matukar gaske Wanda sau da yawa in na tunasu sai inje hawayee suna zubowa daga idanuna.Haydar ya kasance mai sadaukar da farin cikin sa saboda ni,in takaice muku ya zamar min kamar wani mijin marainiya,innace mijin marainiya ina nufin ya zamar mun uwa,uba,wa,kani,kanwa da kuma kawai,Haydar ya taka muhimmiyar rawa a rayuwata wacce ba zan taba mantawa da ita ba.

Ni dai asalin sunana Aisha amma mafi yawancin mutane da _*ANAYAH*_ mahaifina ya kasance Air vice Marshal ne wato(AVM),wanda mutane suka fi kiran shi da AVM Sadeeq,babana dan asalin mambila ne wanda ke jahar Taraba wato Jalingo,amma yanzun muna zaune ne a garin Kaduna,muna Zaria.Babana hamshakin mai kudine wanda in har ana lissafo masu kudin garin mu dole ya fito a cikin top 3,kai in taikaice muku ko gidane ake kwatancen kyawunsa,da tsarin sa da girman sa akanyi dana mahaifina saboda makudan kudaden da aka narka gurin gina gidan da yake zaune. Mahaifina yayi aure aure yafi a qirga amma fa shi ba zaka kira shi auri saki ba dan matan ne kan kawo Kansu gurin shi,wasu saboda kudin sa dan suci arziki,wasu kuma dan su haihu dashi saboda su samu gado,shikuma a nasa bangaren suna rayuwa da matan ne saboda asirce asircen su,kun san dai jami'in tsaro da bincike yawanci toh saboda wadannan matsalolin yake rabuwa dasu.Mahaifiyata yar asalin Adamawa state ce,kyakykyawar bafulatana,sun hadu da mahaifina ne lokacin tana kiwo shi kuma yaje garin Adamawa akan wani case,anan suka hadu har ya aureta,shi ya kaita makaranta har gashi yanzun ta zama Justice,babu wanda bai san mahaifiyata ba a fannin shari'a, duk inda ka shiga a garin Zaria ka Tambaya wacece Justice Fatima Abdu sai an kawo ka gurin ta saboda kwarewarta a fannin shari'a, mahaifiyata lokacin da sukayi aure da babana sun dade basu samu haihuwa ba shiyasa dukkan mu ba wasu manya bane.Mu hudu Allah ya azurta iyayen mu dashi,nice babba sai mai bimin Ummu Sulaim amma mun fi kiran ta da Sulaimy,sai Maryam sai kuma autan mu Abdallah wanda muna yawan kiran sa da Abdul.

ANAYAHWhere stories live. Discover now