Pg 25....

55 3 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_









*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







‎بسم الله الرحمن الرحيم






*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_




*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_



Pg 26.......




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_



Kare ya daddy yayi yana kallon mummy sannan yace"ki kyale ta tayi ma kanta tunda yanzun gashi hankalin ta ya kasa kwanciya saboda abinda ta aikata",juyawa yayi ya kalli Sabreen yace"kije Allah ya yafe mana gaba daya",cike da matsanancin kuka Sabreen ta kalli daddy tace"na gode Sadeeq ban taba tunanin zata yafe mun wannan mummunan aikin da na aikata maka ba,na gode "tana fadin haka ta juya ta bar gidan,fadawa kan kujera mummy tayi dabas ta zauna,kuka ta fashe dashi mai cin rai tace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,dama wannan matar ita tayi sa abin mutuwar yata,ita tasa aka aikata mata wannan mummunan aikin wanda duk rashin imanin ka ya kamata ka tausaya ma mutum balle mace yar uwar ta",kuka sosai muka shaa kamar yau ne abinda ya faru da Sulaimy ya dawo,ji nake yi gaba daya komai ya dawo kaina duk abinda ya faru kawai ganin sa nake yi a cikin idanuwa na,halin da ta shiga har Allah ya dauki ranta,ranar mun sha kuka duk wani farin cikin mu sai da muka neme shi muka rasa,Allah dai ya jikan Sulaimy Allah yasa tana kyakykyawan matsayi shi ne kawai abin cewa.

HAYDAR

A bangaren su Ummi suma shirye shiryen biki suke ba kama hannun yaro,yanzun halin da ake ciki gaba daya basa kula Yaya sun watsar da ita da problems din ta,gaba daya jin zaman gidan take kamar tana zaune a kan kaya,taso ace Abba ya amince da zabin ta na cewa HAYDAR ya auri Samha amma dan Abba yaki yarda yace zabin dan sa zai bi ba ruwan shi,in yaron yace Samha yake so shikenan zai aura mai ita kuma zai yi farin ciki tunda yar uwar sa ce amma in yace yana da wadda yake so shikenan zai aura masa wadda yake muradi ne,wannan maganar ba karamin bata ma Yaya rai tayi ba shiyasa ma yanzun ta bar ba kula Ummi gaba daya,itama kuwa Ummi hakan ya matukar yi mata dadi dan haka ta watsar da ita ta manta da cewa akwai wata hakura wai ita Yaya a cikin gidan ta.Kamar kullum yau ma Samha a gidan ta yini gun Yaya dan ta riga ta kwallafa ranta akan HAYDAR gani take kawai ko mai zai faru dai ta auri HAYDAR sai ta zama matar sa,ta alkawarta ma kanta wannan sai dai duk abinda zai faru ya faru amma bazata yarda wata ta aure shi ba ko da kuwa bata samu nasara ba in yayi auren duk yadda zata yi ta mu guna wa matar sai tayi,tayi alkawarin da Jafar ya sai ta gudu ta bar gidan wannan shine alkawarin da ta daukar wa kanta,kallon Yaya tayi tace "Yaya na rasa meyesa Yah HAYDAR ya tsane ni baya kaunata wallahi,kinga kuwa kallin daya mun lokacin da zan Shigo cikin gidan nan kallo mai cike da tsana da kin jini",ajiyar zuciya Yaya ta sauke tace "kar ki damu yayi ya gama nasan wannan makirar uwar tasa ce take zugashi amma bari matar tazo sai ta gane kuranta",dariya Samha ita ma ta kwashe dashi sannan tace"hmmm ai wallahi sai na koya wa yarinya hankali sai na nuna mata ni yar duniya ce sai ta gane ta aure mun miji dani take zancen",dariyan mugunta Yaya ta kwashe dashi tace "yawwa haka nake son ji hakan da kika fada ya kara tabbatar mun da cewa ke jinin mu ce,dan nasan jinin muce zata tsaya tsayin daka ya kwatar ruwa kanta yanci",haka Yaya ta zauna ta gama zufa Samha kan yadda zata gabatar da komai.
Ita kuwa Ummi ko ta kansu bata yi ba dan ko mai zai faru sai dai ya faru amma bazata taba yarda a aura ma Santa Samha ba yarinyar da babu wanda bai san tsantsar rashin tarbiyyar dake dawainiya da ita ba itace zata yarda ta zama surukar ta,haba hakan ma bazai taba yuwu ba,ita kanta Ummi ta manta yaushe rabon da gaisuwa ya shiga tsakanin ta da da Samha har ta manta,rashin tarbiyyar ta ma ba zata yadda a hada mata ita da dan ta ba,ko dan tarbiyyar yaran shi.

ANAYAH

Yanzun haka saura 1months bikin mu komai an gama yin shi kamar yadda ya kamata,kallona Maryam tayi tace "Aunty wai dan Allah kina nufin ba wani event da za'a yi a wannan bikin,haka zamuyi shi kamar wani gidan mutuwa ",dariya na saki sannan nace"dan ba'ayi event ba shine za'a dauka kamar wani gidan mutuwa,albarkar aure nake nema so babu wani abinda za'a yi daga walima sai taron biki",tabe baki Maryam tayi tace "tab lallai gaskiya hakan bazai yuwu ba,bari ma kiji ko ke bazaki yi ba mummy sai tayi kinsan dai ba zai yuwu ace first born din mummy zata yi aure ba amma ba'ayi wani event ba wannan ma kinsan ba mai yuwuwa bane ",jinjina kaina kawai nayi dan nasan ko banyi ba mummy sai tayi ko Mother's Day ne wannan nasan kamar dole ne,ni kuma Allah ya sani baba bukatar wani bidi'a a ba aure na.....


KAMAR YADDA NA ALKAWARTA MUKU KO KADAN NE ZAKU RINKA SAMU KULLUM GASHI NAN BA YAWA MANAGE KAWAI....

SHARE FISABILILLAH


Zahraty
08063304625

ANAYAHWhere stories live. Discover now