pg 2...

160 5 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_



*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

بسم الله الرحمن الرحيم

*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_

*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_
_*Pg 2.....*_

_EDITED_

Salati kawai Dr.Maryam keyi,yanzu kuwa bata san taya zata fara wannan maganar ba,dago kai tayi ta kalli mummy tace "haba mum ANAYAH wannan wani irin magana ne babu dadin ji babu dad in saurare,Dan Allah kiyi hakuri,kisa ma zuciyar ki salama kada kizo kiyi abunda nan gaba zakizo kina dana sani,zama ya kamata kiyi ki bnincika wani dalili ne yake saka mijin ki neman mata saboda wasu m!azan ba haka kawai suke neman mata ba akwai dalili", wani irin murmushi mai ciwo mummy tayi tace" haba Maryam ke me kike tunanin zai saka Sadeeq neman mata,kawai dabbanci ne da akuyanci dake damun sa,Maryam condom fa na tsinta a dakin sa,haba me yake yi da condom,da farko da ace yana da gaskiya zai zaunar dani ne yamun bayani akan abunda na bani,ya wanke kanmsa,amma da yake ance 99days for a thief one day for the owner gama kasa kwanciyar hankali,hankalin sa ya tashi daya tabbatar naa abun, a lokacin sai nayi main uzuri kan cewa kila banashi bane,jiya a nan wata karuwa tazo neman sa,daga nan na dasa alamar tambaya akan shi,na tambaye shi wacece ita,ya kasaa bani ansa,yau kuwa kin San wani abun mamaki,kaya fa ya siya mata,inners da sexy wears na gani a motar sa ,amma a haka kuma ake bani hakuri in cigaba da zama da wanda bai dauki aure da mutunci ba,wanda bansan darajar aure ba,wanda bai san inda ke masa ciwo ba,haka I'm tired wallahi Dr,I can't kawai kind ki same shi ya bani takarda ta,I can't continue living with a man that betrayed me,wallahi Allah sai saka mun,Allah ba zai bar Sadeeq ba sai ya bi mun hakki na",hawaye ne masu zafi suka sauka akan fuskar Dr.Maryam,kallon mummy tayi tace"maza kala kala ne mum ANAYAH,dayawan su akwai abun da yasa suka fara neman mata,akwai namijin da sai bayan da yayi aure ne ya fara neman matan,irin wadannan kuwa sakaci ne daga gurin matan mostly saboda mazan nada kafin sha'awa amma sun kasa kula da wannan sai kiga namiji baya neman mata kafin yayi aure amma bayan auren shi sai kiga ya fara neman mata.Na biyu;akwai wanda yana Neman mata kafin yayi aure amma da zarar yayi aure sai kiga ya bari,wannan kuwa da yawa matan su sun taka babbar rawa gun wannan bar in da yayi saboda kila rashin mata ne yasa yake Neman matan,amma da yayi aure sai kiga ya daina saboda matar shi zata iya gamsar dashi.Na uku;akwai Wanda tun kafin yayui aure yake neman mata,kuma har yayi auren bai dena ma,irin wadannan sai dai ke a matsayinki na matarshi kiyi ta main addua Allah ya shirya shi saboda irin wadannan ma sunfi yawa.Abun dubawa a nan shi ne ke a matsayin ki na matar shi zaki duba me ke kara dilmiya shi a cikin wannan harkar neman matyan,wasu zaki ga yawancvi abokai ne da mutanen dake kusa dasu sosai, sai ki San yadda zakiyui ki rinka janye shji daga abokan da baki gamsu da abokantakar su bana,in Allah yazo sai kika ga ya bari amma bari in fada miki wani Abu,duk wacce mijinta ke neman mata sai tayi hakuri,zina Nada wahalar dainawa ga mai yinta,amma in Allah ya taimake ki mijin ki ya tuba ya bari tareda alkawarin insha Allah bazai koma mata,shikenan sai ki gode ma Allah",hawaye ne suka zuba akan kuncin mummy tace"mum Munaya wallahi bansan sanda Sadeeq ya fara neman mata ba,I'm trying my possible best inga cewa ban tuye Sadeeq ba a shinfidan shi,mum Munaya abunda ke kara daga mun hankali shi ne Sadeeq fa Zina yake aikatawa da auren sa fah,bai duba mai wannan dabi'ar zaij haifar ma family din nan ba yake aikatawa,mum Munaya kar ki manta cewa Zina bashi ne in har ka aikata sai an aikata maka,in ba'a yi da yar ka ba,za'a yi da matar ka,ko da mahaifiyar ka ko kuma da kanwar ka ko yar ka,ko kuma da katangar gidan ka,mutane da yawa bnasu San mai ake nufi da wannan katangar ba,zai iya yuwa wacce zata gina maka family kenan wato surukarka",hawaye Dr.Maryam ta share tare da cewa"nasan da haka mum ANAYAH amma duk da haka kiyi hakuri ANAYAH bazata iya kula da yaran nan ba in kika tafgi kika bar su,tsaya yara shekara 12yrszata kula dasu,ga Ummusulaim ga Maryam ga Abdallah tsaya zata kula dasu,kin San bazata iya ba",ajiyar zuciya mummy ta saukme sannan tace"shikenan Dr naji zan zauna amma ina mai tabbatar miki da cewa a yanzun duk duniyar nan ba wanda na tsana na tsani gani kamar Sadeeq amma zan yi hakuri in zauna ko dan yarana",cike da farin ciki Dr Maryam tace"masha Allah gaskiya naji dadin yadda kika sauka da wuri haka,kuma ina fatan an sasanta kenan,da izinin Allah ba zai kara shiga cikin lamauran ku ba","ameen ",mummy ta ansa dashi,sannan Dr.Maryam tayi mata sallama ta tafi,har bakin kofa ta rakota sannan ta nufi dakin su ANAYAH ta duba su,Dr.Maryam na fitowa ta tadda daddy a tsaye,kallon sa tayi tace "gaskiya dad ANAYAH banji fadi ba akan abunda ka aikata,baka tunanin wannan abun yana ma rayuwar yaran ka da matsala, its unfair Allah,naji kunya sanda take fada mun abunda ka aikata,haba yanzun ma da kyar ta amince zata cigaba da zama a cikin gidan nan,amma not because of you is just for the sake of her children", kallon ta yayi yace" thank u Dr.Maryam I really appreciate, I know what I'm going to do zata sakko",godiya ya kara ma Dr Maryam sannan ya shige gidan.

ANAYAHWhere stories live. Discover now