Pg 24.......

58 2 0
                                    

_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_




*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_









*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







‎بسم الله الرحمن الرحيم






*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_




*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_



Pg 25.......




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_



Haka lokaci ya cigaba da tafiya,komai na tafiya yadda ya kamata bani da wata matsala yanzun a rayuwa ta haka ma soyayya ta da HAYDAR na tafiya yadda ya kamata.A yau ne muka tashi da mummunan labarin cewa Allah yayi wa Najaatu yarinyar Baba Arma rasuwa,hankalin mu ya tashi matuka,haka muka shirya muka nufi Taraba ranar,na dade banga tashin hankali kamar wadda na gani ba lokacin da Najaatu ta rasu,Allah sarki rayuwa kenan komai da yadda Allah ya tsara shi,iyayen ya sun matukar bani tausayi na hawaye sai da nayi musu shikenan fah wannan shi ne rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka girba,duk abinda kai aikata alkhairy ko akasin hakan kaima ka tabbatar sai an aikata maka shi,gashi dai abinda gwaggo Tabawa ta aikata ita tana tunanin ta ci bulus gashi nan abin ya saka rayuwar iyalan ta cikin kunci da danasani,haka mukayi kwana bakwai muka juyo muka dawo gida duk kuwa da cewa ba karamin tashin hankali muka baro mutan gidan a ciki ba dan rikice ake sosai,Baba Arma yace ko mai zai faru ba zai yadda ba dan baba Isuhu shi ya kashe mishi yarinya sai ya kaishi kotu duk abinda zai faru sai dai ya faru shima a kashe shi kamar yadda ya kashe mai tashi yarinyar,daddy yayi iya bakin kokarinshi dan yaga ya sasanta su amma abin ya ba faskara haka nan muka baro su muka dawo gida.

        Shiryen shiryen biki na gidan mu suke yi sosai kasancewar ba'a saka ranar da wani yawa ba sosai,lokaci tafiya yake yi,gaba daya mummy ta maida ba hankalin ta gun aurar dani,bata nuna damuwar ta gun kashe kudin da take yi ko nawa akace mata abu bata damuwa take fito da kudi ta siya mun,sau da dama tana tambaya na zabi amma bana iya zaba sai dai ita da Maryam su zaba,tun yanzun har na fara ramewa saboda kewar gida da nake ta tunani,kullum inna ga ana shirin auren ji nake jikina yayi sanyi kamar in zauna in ta kuka,wani lokacin kasa danne zuciya ta nake yi har sai nayi kukan da nake son yi,komai da kuka san ana ma yarinya na aure babu abinda ba'a mun ba.

A bangare na ni da HAYDAR kuwa soyayya muka sha kamar ba gobe,na manta duk wani kunci da ya faru dani a baya komai ya zama tarihi duk na manta.

Kamar ko yaushe yau ma muna zaune a parlour dukkan mu har da daddy da mummy sai list din kaya sukeyi da Maryam,kamar an gefo ta haka muka ga ta shigo cikin dakin,cike da matsananciyar mamaki muke kallon ta,a rayuwa ta ko zan manta da ko wacce fuska bazan taba mantawa da fuskar wannan matar ba,na tsane ta naki jinin ta,itace sanadin shigar mu duk wata bala'i da muka shiga a baya,ina mata wani irin tsana na musamman wanda ban taba ma wani mahaluki ba,mikewa daddy da mummy sukayi lokaci guda,kallo daya zakayi wa daddy kaga tsantsar bacin rai kwance a fuskar sa,kallon ta yake yi cike da tsana yace "Sabreen mai ya kawo ki gida na mai kika zo yi",kafin tace wani abu mummy ta kalli daddy tace"kaddai ace ka koma ruwa  dan ban san mai ya kawo wannan tsinanniyar matar da wannan mummunar fuskar ta ta cikin gida na ba",mu dai muna zaune munyi shiru muna kallon abin da ke faruwa kamar mun samu Tv kowa da abinda yake rayawa a cikin zuciyar sa,kuka mai ba karfi Sabreen ta saka,sai da tayi kuka na kusan mintuna talatin babu wanda ya tanka ta kafin ta bude baki ta fara magana"nasan da wuya ku yafe mun abinda na aikata muku,nayi dana sani sai daga baya na gane rashin kyautawa ta bai kamata ko da Sadeeq ya mun ba dai dai ba in aikata abinda na aikata dan nima naga ya shiga halin bakin ciki da tashin hankalin da na shiga ba",wani tsawa mummy ta daka mata tace"malama ki fadi abinda ya kawoki in kuma wannan doki burutsin zaki cigaba dayi shikenan bana bukatar ji ki tashi ki bar mun gida",ajiyar zuciya Sabreen ta sauke kafin ta fara cewa;

FLASHBACK

     Lokacin da muka rabu da Sadeeq ina barin gidan shi kai tsaye gidan wata kawata na nufa,Suhaimah babban dillalaiyar mata ce,duk wani matsala in har ka shiga ciki tabbas in dai tana da hanyar magance maka ita sai ta magance maka,ina shiga gidan na tadda ta zaune a parlour tana qirga kudi masu yawan gaske,yadda taga na shigo tasan ba lafiya ba,dagowa tayi cikin wani kallo na yan duniya tace "haba Sabreen ya haka menene kuma yau?"kuka na fashe mata dashi nace "Sadeeq ya sake ni Suhaimah nan dan ya zanyi ba,Sadeeq bai da mutunci mai nayi mai da zafi haka",baki kawai Suhaimah ta saki tana kallo na,numfasawa tayi tace"lallai Sadeeq ban taba tsammanin cewa mutumin nan shah starten dan iska bane zai yau,wannan wani irin bala'i ne,saki kuma,lallai toh wallahi ya debo ruwan dafa kansa da kansa sai mun nuna masa waye mu,sai mu masa tabon da bazai manta dashi ba,sai mun lalata rayuwar iyalan shi",ta fada cikin karaji kamar wata zakanya,juyowa tayi ta kalleni,dafani tayi tace"Sabreen karki damu kanki kar ki sa ciwon zuciya ya mamaki akan wani matsiyaci wanda ba ko Allah ya sawake bazai ce miki ba in yaji labarin kin kamu da ciwon zuciya,akwai hanya daya da zamuyi anfani dashi gun ganin mun lalata mishi farin cikin sa kamar yadda ya miki",dagowa nayi cikin wani yanayi nace "Suhaima kawai fadamun,bana mukatar bata lokaci yanzun nake so ayi ayi komai kawai kowa ma ya shiga cikin tashin hankalin",nan take ta bani shawarar akwai wasu maza da ba take dasu kusan su takwas kawai su sato daya daga cikin yaran ka tunda duk yawancin su mata ne suyi mata fyade su lalata mata rayuwa ta yadda bazata moru ba,babu wani namijin da zai kalleta yace yana shaawar auren ta,haka muka sa aka sato ta suka aikata mata fyade,hankali na bai tashi ba a lokacin,banji wani tunanin wannan abinda zan aikata ba bashi da kyau ba sai dana samu labarin rasuwar Sulaimy,hankalina ya tashi na shiga cikin matsananciyar danasani da nadama,nayi kuka har na gaji,a kwana a tashi rayuwa tayi mun zafi,bana iya bacci kwata kwata dan in har zan kwanta sai nayi mafarkin Sulaimy tazo tana cemun "mai na aikata miki haka da zafi dana cancanci wannan hukuncin daga gare ki",kuka ta qara fashewa dashi tana cigaba da cewa"hakkin ran Sulaimy yaki bari a cikin kwanciyar hankali,duk wadan nan shekarun nadade ina neman ku ban same ku ba sai daga baya na samj labarin kun dawo Abuja da zama,na kasa samun kwanciyar hankali har sai da na nemi gidan ku yau nazo domin neman gafara daga gun ku,"dan Allah ku yafe mun nayi dana sanin abinda na aikata",wani irin kuka mummy ta fashe dashi tana kallon ta,kasa jurewa tayi ta mike cikin matsananciyar harzuka tayo kanta.......

DAN ALLAH KUYI HAKURI,BANSAN YADDA ZAN MUSALTA MUKU BA,WALLAHI ABUBUWA NE SUNYI MUN YAWA A KA,NI KAINA BANA JIN DADIN RASHIN YIN UPDATE A KAI AKAI AMMA DAN ALLAH KUYI HAKURI INSHA ALLAH DAGA YAU ZAKU DINGA SAMUN UPDATE KO BA YAWA,KU MIN UZIRI DAN ALLAH 😫🙏🏻

SHARE FISABILILLAH

Zahraty
08063304625

ANAYAHWhere stories live. Discover now